Yadda Aka Yaudare Ni a NNPP Na Dauka Ina Takara In ji Mai Neman Kujerar Majalisa
- Hajara Alhassan Masaga ta zage tana kamfe domin zama ‘yar majalisar tarayya ta yankin Chachaga a jihar Neja
- Sai yanzu kwatsam ta gane cewa jam’iyyarsu ta NNPP ba ta tura wa INEC sunanta a matsayin ‘yar takararta ba
- Saboda haka ‘yar siyasar ta bukaci NNPP ta biya ta N7.8m da ta kashe da karin N10m na wahalar da ita a banza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - Hajara Alhassan Masaga ta dauki lokaci tana tunanin tana takarar ‘yar majalisar wakilan tarayya a jam’iyyar NNPP a 2027.
Bayan dogon lokaci tana sa ran ita ce ‘yar takarar mazabar Chanchaga a jihar Neja, sai yanzu ta fahimci babu sunan ta wajen INEC.

Source: Facebook
Hajara Alhassan Masaga ta ce an hana ta takara
A wata zanta wa ta musamman da Legit Hausa, Hajara Alhassan Masaga ta zargi jam’iyyar NNPP da karya da bata mata lokaci.

Kara karanta wannan
Hakeem Baba Ahmed ya tsallake Atiku, ya fadi dan takarar da ya fi cancanta a zaben 2027
Ranar 20 ga watan Agusta 2026, ‘yar siyasar ta rubuta wa jam’iyyar NNPP wasika tana amincewa da shiga takara a zaben 2027.
Ta sanar da shugabannin jam’iyya cewa tana harin kujerar ‘yar majalisar wakilan tarayya ta mazabar Chanchanga a inuwar NNPP.
NNPP ta tsaida 'dan takarar majalisa a Chanchaga
Hakan ya biyo bayan zaben ta da aka yi a matsayin ‘yar takara daya tilo, bayanan da muka samu sun nuna ta samu kuri’u 22 a ranar.
Kwamred M. K Garba ya sa hannu madadin jam’iyyar NNPP a takardar zaben da aka yi da nufin sauya ‘dan takarar kujerar majalisar.
Masu kada kuri’a sun fito daga Nasarawa, Sabon Gari, Limawa, Tudun Wada da Minna duk a karkashin mazabar ta Chanchaga.
Daga baya shugaban NNPP na kasa, Agbo G. Major ya fitar da takarda, yana sanar da INEC game da canjin ‘yar takarar da suka yi.
Wata wasika daga Major da sakatarensa, Olaposi Oginni sun nuna NNPP ta canza Abdullahi Halifa Aliyu da ita wannan ‘yar siyasa.
NNPP ba ta aika wa INEC sunan mai takara ba
Hajara Masaga ta ce bayan wannan ne ta fara jin labari dabam, har ta fahimci ba ta cikin ‘yan takaran da aka aika wa hukumar INEC.
Bayan ta tabbatar da babu sunayen ta a cikin masu neman takarar ‘yan Majalisar tarayya a zaben 2027, yanzu ta fito tana neman hakkinta.
Cikin farkon makon nan kwamitin yakin neman zaben Masaga ya rubuta takarda zai aika wa NNPP a Neja domin neman hakki daga jam’iyya.
'Yar takara ta taso jam'iyyar NNPP a gaba
Wasikar ta ce ‘yar takarar ta yi duk abin da ake yi da nufin shiga zabe amma sai ga shi babu sunan ta a jerin masu shiga babban zaben 2027.
Kwamitin kamfen din ya ce babu inda Hajiya Hajara Masaga ta janye takara kuma ba a yi maganar cewa an maye gurbinta da wani dabam ba.
Saboda haka ne ake neman jam’iyyar ta dawo wa ‘yar takarar da N17, 823, 400 da ta kashe.

Kara karanta wannan
Daga zuwa NDC, Babachir ya shiga tono abubuwa har da bayyana masu munafuntar jam'iyya
‘Yar siyasar tana zargin da gan-gan aka kawo mata cikas, kuma an yi mata barazana, kuma tana tunanin akwai cin dunduniya a jam'iyyar adawar.
Hajara Masaga tana neman N17m hannun NNPP
Isah Kusherki Yusuf da ya sa hannu a wasikar ya ce sun kashe N7.823m a kamfe - N1.85m wajen sayen fam da hulda da manema labarai.
Ya ce zirga-zirga ta ci N890, 000 sannan an biya jami’an tsaro N620, 000 sai N540, 000 a kan wallafe-wallafe da tallar takarar da aka yi.
Sauran kudin sun hada da kashe N478, 000 wajen walwala da N310, 000 da aka biya wajen yin taro da wasu kudi na man janareto da sayen data.
Bugu da kari, Kusherki Yusuf ya bukaci NNPP ta biya su N10m a matsayin ukubar bata masu lokaci da wahalar da su da aka yi a banza.

Source: Facebook
Shugabannin NNPP ba su yi magana ba
Jaridar Legit Hausa ta tuntubi shugabannin NNPP na reshen jihar Neja kuma sun nuna cewa batun yana hannun uwar jam’iyya ta kasa.
Shi shugaban jam’iyyar ya ce a matsayinsa, tuni ya gudanar da zaben tsaida gwani domin fitar da wanda zai tsaya wa NNPP takara.

Kara karanta wannan
Isa Pantami, Donald Duke da ‘yan siyasan da hukuncin Kotun koli zai iya rusa takararsu
Zuwa yanzu ba mu iya samun shugabannin jam’iyyar adawar na kasa domin jin ta bakinsu ba.
Takarar Pantami ta ga ta kanta a PDP
Matsala ba ta kare wa Isa Ali Pantami ba domin ana da labari wani mai neman gwamnan Gombe a PDP zai sake maka shi a kotu.
Khamis Mailantarki ya ce shi ya yi nasara a zaben gwanin PDP, hakan yana nufin sabuwar shari’a a kotu tana jiran jam’iyyar adawar.
Kafin wannan takara, Hon. Mailantarki ya nemi zama gwamnan Gombe a jam’iyyun APC da NNPP amma bai taba yin nasara ba.
Asali: Legit.ng
