APC, ADC da Jam'iyyun da Suka Bayyana Shirinsu na Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa
- APC ta ce tana kammala cikakken shirin yakin neman zabe, yayin da take ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kafin gabanin bayyana tsarinta
- Jam'iyyar su Atiku Abubakar, ADC ta ce tana gina tsarin yakin neman zabe na dogon lokaci, inda ta jaddada cewa za ta shigo da salo da dabara
- Sauran jam'iyyun PDP, LP da SDP sun bayyana dabarunsu, inda PDP ta ce za ta mayar da hankali kan yakin neman zabe mai tushe a kan manufofi masu kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Bisa jadawalin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar, yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ya fara a ranar Laraba, 19 ga Agusta, 2026.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki zai gudana ne a lokaci guda a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Source: Twitter
Binciken Nigerian Tribune ya nuna cewa manyan jam’iyyun siyasar kasar na shirye-shiryen bayyana tsare-tsarensu domin tunkarar babban yakin neman zaben 2027.
Abin da jadawalin INEC ke cewa
A cewar jadawalin INEC, yakin neman zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi zai fara ne a ranar 9 ga Satumba, 2026.
Binciken ya gano cewa APC na jiran umarnin jagoran jam’iyyar kuma dan takararta na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan yadda za a tsara kwamitocin yakin neman zabenta.
A halin yanzu, ana ta maganganu kan wanda zai jagoranci tawagar yakin neman zaben Tinubu a matsayin Darakta-Janar da ai shugabanci lamarin.
Daga cikin sunayen da ake ambata akwai Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, da tsohon Gwamnan Zamfara, Abdul’aziz Yari.
Haka kuma, ana ambaton sunan Ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin daya daga cikin manyan jiga-jigan da za su taka rawa a yakin neman zaben APC.
Wata majiya daga jam’iyyar ta ce:
“Zabar wanda zai jagoranci yakin neman zaben ya rataya ne kawai a kan Shugaba Tinubu.”
Shirin jam'iyyun adawa kan zaben 2027
Jam’iyyar ADC ta ce tana kammala tsarin yakin neman zabenta na abin da ta kira “yakin neman zabe na dogon lokaci” kafin zaben 2027.

Source: Getty Images
Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya ce ba sauri suke ba, saboda zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki zai gudana ne a watan Janairu na shekara mai zuwa.
Ya ce:
“Muna shiryawa. Muna hada tsarin yakin neman zabenmu.”
Ita ma PDP ta ce yakin neman zabenta na 2027 ba zai kasance irin tarukan shagali da hayaniya da aka saba gani a lokutan zabe ba.
Sakataren Yada Labarai na Kwamitin Gudanarwa na Kasa na wucin gadi na jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce PDP ta koyi darasi daga gazawar da ta fuskanta a zabukan 2015, 2019 da 2023.
Ya ce jam’iyyar za ta gudanar da yakin neman zabe da zai mayar da hankali kan matsaloli da bukatun al’umma, tare da isar da sakon ‘yan takararta kai tsaye ga masu zabe.
Ita kuma LP ta bakin Sakataren Yada Labarai na kasa, Ken Asogwa, ya ce karfin tsarin jam’iyyar na matakin kasa zai taimaka wajen tallata ‘yan takararta a zaben 2027.
Ya ce tsarin daukar shugabanni da kara karfin jam’iyyar ya samar da kyakkyawan tushe domin gudanar da yakin neman zabe bisa gaskiya, amana da rikon gaskiya.
A bangaren SDP ta ce tana shirin bayyana babban tsarin yakin neman zabenta na shugaban kasa nan ba da jimawa ba. Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar na kasa, Araba Rufus Ayenigba, ne ya bayyana hakan.
Ya ce ana gudanar da tuntuba domin kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa mai karfi wanda zai taimaka wajen yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar, Prince Adedayo Adewole.
Shirin NDC kan fara yakin neman zabe
A baya, kun ji cewa NDC ta ce za ta bi dabarun da suka dace wajen yakin neman zaben 2027, maimakon fara manyan gangamin siyasa da aka saba gani ana yi a zabukan baya.
Jam’iyyar ta ce za ta yi amfani da lokacin da ya rage wajen tsara yakin neman zabe mai tasiri da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki game da yadda za a samu jama'ar da suka dace.
NDC ta kuma yi Allah-wadai da karin kudin tallan allunan siyasa da wasu gwamnatocin jihohi suka yi, tana cewa hakan na takura wa ’yancin yan siyasa na bayyana ra'ayinsu kan wanda su ke so.
Asali: Legit.ng



