Zaben Osun: Ana Rige Rigen Sayen Kuri'un Talakawa da Kudi da Abinci

Zaben Osun: Ana Rige Rigen Sayen Kuri'un Talakawa da Kudi da Abinci

  • An zargi jam’iyyun APC da Accord da shiga gasar sayen kuri’u a faɗin jihar Osun, inda ake zargin wakilan jam’iyyun na bai wa masu zaɓe kudi
  • Rahotanni sun ce an fara rabon kuɗin ne kwanaki shida kafin zaɓen gwamnan jihar, yayin da aka kuma tattara lambobin asusun bankin dubban masu zaɓe
  • Wani bayani da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa ana tura wa masu zabe ta asusun bankinsu daga tsakanin N10,000 da N20,000 domin jan hankalinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Osogbo – Ana zargin jam’iyyun APC da Accord da fara rabon kuɗi ga masu zaɓe a wasu sassan jihar Osun yayin da ake gudanar da zaɓen gwamna a yau.

Gwamna Ademola Adeleke na Accord na fuskantar Bola Oyebamiji na APC, Najeem Salaam na ADC da wasu ‘yan takara tara a zaɓen.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Yadda aka yi zaben Edo
Mutane ne na kada kuri'a a zaben Edo. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Punch ruwaito cewa wasu masu zaɓe sun tabbatar da karɓar kuɗi da kayan abinci daga jam’iyyun, yayin da wasu aka ce an tilasta masu yin rantsuwa cewa za su zaɓi jam’iyyar da ta ba su kayan.

Ana rabon N20,000 a Ilesa

Masu zaɓe a Ilesa sun ce APC na raba N20,000 ga kowane mai zaɓe a wasu sassan ƙananan hukumomin Ilesa Ta Gabas, Ilesa ta Yamma da Atakunmosa.

Wasu daga cikin waɗanda suka karɓi kuɗin sun ce ana rabawa ne a gidajen wasu jiga-jigan jam’iyyar da aka naɗa a rumfunan zaɓe.

Wani da ya ci gajiyar shirin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce ya karɓi N20,000 a yankin Bonnke da ke Ilesa ranar Laraba.

Ya ce an raba kuɗin ne a takardun N1,000 da N500, inda mutane sama da 200 suka karɓa a rumfar da yake zaɓe.

Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a Ilesa ya kuma tabbatar da rabon kuɗin a yankunan Coca-Cola da Abiola Avenue.

Kara karanta wannan

Osun: APC na zargin an yi mata mummunan barna ana shirin zaben gwamna

Ana rabon kuɗi da shinkafa

A yankunan Iroye da Imo na Ilesa, an kuma ce APC na rabawa masu zaɓe shinkafa tare da wani adadin kuɗi da ba a bayyana ba.

Wani shugaban ɗalibai a yankin ya ce ya ga magoya bayan APC suna raba kuɗi da shinkafa tare da gargaɗin masu karɓa kada su ci amanar jam’iyyar a lokacin zaɓe.

A halin da ake ciki, rahoton ya ce Accord na rabon N10,000 ga masu zaɓe a wasu yankunan Ilesa.

An kuma ce a Olowu da ke Atakunmosa, jam’iyyar ta raba N10,000 tare da buƙatar waɗanda suka karɓa su yi rantsuwa za su zabe ta.

APC ta ce kuɗin sufuri ne

Wasu mazauna Ilesa sun ce Accord ta fara rabon N10,000 a yankunan Ifofin, Iloro da Okesa tun ranar Talata.

Sai dai wani jigon APC a Ilesa ya tabbatar da rabon kuɗin, amma ya musanta cewa ana sayen kuri’u ne da su.

Ya ce kuɗin da jam’iyyar ke bayarwa na sufuri ne domin taimaka wa masu zaɓe su isa rumfunan zaɓensu.

Kara karanta wannan

ADC: 'Abu 1 da zai hana jam'iyyar su Atiku nasara a zaɓen Osun'

Ana rabon N15,000 a Osogbo

A ƙaramar hukumar Osogbo, an tattaro cewa APC na bai wa wasu masu zaɓe N15,000 a rumfunan zaɓe da ke cikin dukkanin unguwanni 15.

Wani jigon APC da ke da hannu wajen rabon ya ce jam’iyyar ta naɗa shugabanni uku a kowace unguwa domin gudanar da aikin.

Mutane a layinzabe
Lokacin da aka kada kuri'a a zaben Anambra. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Ya ce an yi niyyar bai wa mutane 150 a kowace rumfa, inda aka ba masu zaɓe 75 N15,000 ranar Laraba, sannan wasu 75 suka karɓi irin wannan kuɗin ranar Alhamis.

An tura jami’an tsaro Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa jihar Osun ta kasance cikin kwanciyar yayin da aka tura jami’an tsaro masu yawa yayin da ake shirin zabe.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce manyan‘yan sanda 30 za su kula da tsaron zaɓen, yayin da Hukumar Tsaron Fararen Hula, NSCDC, ta ce za ta tura jami’ai sama da 10,000.

Rahotanni sun ce jami’an soji, ‘yan sanda, NSCDC da sauran jami’an tsaro sun bazu a ƙananan hukumomi 30 na jihar domin tabbatar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng