Mutane fiye da 10 da Adeleke Ya Tara Wuri Daya Ya Yi Masu Duka a Zaben Osun
Osun - Ta tabbata cewa Sanata Ademola Nurudeen Jackson Adeleke ya sake yin nasara a zaben gwamnan jihar Osun da ka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Wannan karo, ya ci zabensa ne a karkashin Accord Party, jam’iyya ta uku da ya tsaya takara a karkashinta a cikin shekaru tara.

Source: Twitter
'Yan APC da Adeleke ya ba kunya
Rahoton nan namu ya tattaro ‘yan siyasar da suka tsaya layi dabam da gwamnan da niyyar su ga bayan shi, shi kuma ya kai su kasa.
1. Bola Tinubu
Daily Trust ta ce cikin mutanen da aka doke duk ba su shiga takarar kai-tsaye ba akwai shi kan Mai girma shugaban kasa.
An yi tunanin tun da yana da alaka da jihar Osun kuma a matsayinsa na shugaban kasa, Bola Tinubu zai jawo APC ta karbe mulki.
2. Bola Oyebamiji
Limamin shan kashi a zaben da aka yi shi ne Bola Oyebamiji wanda Ademola Adeleke ya doke shi da tazarar kuri’u 66, 252.
Ban da dukiya da ya rasa, abin da ya fi ciwo a takarar da ya yi shi ne ajiye mukaminsa da ya yi a NIWA domin neman gwamna.
3. Monday Okpebholo
Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya tsokano wa kan shi fada lokacin da ya zargi Adeleke da yawan tika rawa har ya manta da aikinsa.
Bayan kwanaki takawaran nasa ya masa martani, yana sukar sunansa, kuma ya yi masa shagube dangane da sakamakon jarabawarsa ta WAEC.
4. AbdulRahman AbdulRazaq
Shi Gwamnan Kwara wanda shi ne shugaban gwamnonin jihohi ya fito yana cewa Osun na bukatar gwamna mai kusanci da Bola Tinubu.
Tun daga wajen Davido ya fara shan suka mara dadi. Mawakin ya ce kusancin wasu jihohin kasar nan da Tinubu bai kara masu komai ba.
5. Hope Uzodinma
Gabanin zabe aka ji Hope Uzodimma yana fada wa Davido ya shirya daukar kawunsa aiki, yana nufin zai rasa kujerar gwamna.
Premium Times ta rahoto mawakin yana maida martani, ya zargi wani daga jihar Imo da kokarin kawo matsala a zaben jihar Osun.
6. Olagunsoye Oyinlola
Daf da zabe aka ji The Cable ta ce Olagunsoye Oyinlola ya fito ya mara wa APC baya, an yi mamakin jin hakan daga tsohon ‘dan PDP.
Duk da ya guji tsohon ‘dan jam’iyyarsa, goyon bayan Oyinlola da yaransa ba ta jawo masa komai ba illa shan kunya tun a rumfar zabensu.
7. Ajibola Basiru
Yadda jam’iyyar Accord ta doke Oyinlola a karamar hukumar Okuku, kusan haka aka yi wa Ajibola Basiru a zaben gwamnan na 2026.
Sakataren APC na kasa ya kawo akwatin rumfarsa da tazarar kuri’u 117 a Osogbo amma bai iya sa Oyebamiji ya zama gwamna ba.
8. Bisi Akande
Bisi Akande tsohon gwamna ne a Osun kuma wanda ya fara rike shugabancin APC, ba zai ji dadin sukuwar da Adeleke ya yi masu ba.
The Sun ta ce Baba Omokeekeeke ya iya jagorantar jam’iyyarsa ta samu kuri’u 181 inda yake zabe a Ila-Orangun a karamar hukumar Ila.
9. Francis Adenigba Fadahunsi
Gabanin zaben gwamna a Osun aka rahoto cewa Francis Adenigba Fadahunsi ya yi umarni a kashe ‘ya ‘yan jam’iyyar Accord mai mulki.
Sanatan ya karyata zargin inda ya ce an juya maganarsa wajen fassara. Za a sa shi cikin wadanda suka ji babu dadi a zaben da aka yi.
10. Sauran gwamnonin APC
Gwamnonin jihohin APC da dama sun tafi jihar Osun saboda su ga jam’iyyarsu ta raba Ademola Adeleke daga kan karagar mulki.
Osun: Ragowar wadanda suka sha kashi
A shafin Facebook, Babafemi Ojudu ya jero wasu mutane da ya ce su ne suka jawo jam’iyyar Accord ta doke APC a zaben jihar Osun.
Sanata Ojudu ya ambaci wasu ‘yan APC da yake ganin ba su taimaki jam’iyyar ba tare da yaba wa namijin kokarin Ademola Adeleke.
11. Hukumar EFCC
EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun lokacin da awanni suka rage a shiga zaben gwamna amma daga baya Bola Tinubu ya sa baki.
12. Gboyega Oyetola
‘Dan siyasar ya zargi ministan tarayyar da tsaida ‘dan takaran gwamna mara farin jini a APC wanda a karshen hakan ya ba gwamna mai-ci tazarce.
13. Hon. Wole Oke
Tsohon hadimin na marigayi Muhammadu Buhari ya kawo sunan Wole Oke wanda duk inda ya je sai ya tuna wa mutane Tinubu ne a mulki.
14. Ero Arike
Ojudu ya na da ra’ayin cewa Falilat Yusuf da ta fi shahara da Ero-Arike ta cuci APC da tsine-tsine da surutan da ta rika yi da sunan yakin zabe.
Yadda Adeleke ya lashe zabe a Osun
Rahoton nan ya yi nazarin irin yadda ayyukan Gwamna Ademola Nurudeen Jackson Adeleke suka ceci shi a zaben bana.
Dabarun siyasarsa da kuma rikicin APC sun taka rawar gani wajen kashin Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji a jihar Osun
Ademola Adeleke ya ga bayan Asiwaju Munir Bola Oyebamiji da Najeem F. Salaam na APC da ADC da wasu ‘yan takara 13.
Asali: Legit.ng



