Jerin Wadanda Suka Yi Nasara da Wasu da Suka Tafka Asara a Zaben Osun

Jerin Wadanda Suka Yi Nasara da Wasu da Suka Tafka Asara a Zaben Osun

Gwamna Ademola Adeleke ya lashe zabe inda ya samu yin wa’adinsa na biyu a Osun da kuri’u 511,067, inda ya doke ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji da sauran yan takara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Zaɓen gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta, 2026, ya zo ƙarshe bayan gudanar da yaƙin neman zaɓe da harkokin siyasa a ƙananan hukumomi 30 na jihar.

An sanar da sakamakon zaben gwamnan Osun
Najeem Salam na ADC, Gwamna Ademola Adeleke na Accord da Bola Oyebamiji na APC Hoto: Najeem Salam, Ademola Adeleke, Bola Oyebamiji.
Source: Twitter

Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan ya samu nasarar komawa kan kujerar gwamna a wa’adi na biyu, cewar Punch.

Adeleke, wanda ya tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar Apc, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Ga jerin wasu daga cikin waɗanda suka yi nasara da waɗanda suka sha kaye bayan kammala zaɓen, tare da bayanin rawar da suka taka kafin zaɓen.

Kara karanta wannan

Bayan faduwar APC a Osun, Tinubu ya tura muhimmin sako ga Ademola Adeleke

Waɗanda suka yi nasara

1. Ademola Adeleke

Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya samu damar komawa kan kujerar gwamna na wa’adi na biyu duk da fuskantar ƙalubale daga APC mai mulkin tarayya.

Adeleke ya fara lashe zaɓen gwamna a shekarar 2022 ƙarƙashin jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya koma Accord bayan shirin komawarsa APC bai tabbata ba.

Ya mayar da hankali a yaƙin neman zaɓensa kan ci gaba da ayyukan raya ababen more rayuwa, gyare-gyaren ilimi da kuma hulɗa da jama’a a matakin ƙasa.

Adekeke ya yi nasara a zaɓen Osun
Gwamna Ademola Adeleke da yaronsa, mawaki Davido. Hoto: Davido.
Source: Twitter

2. Jam’iyyar Accord

Wannan nasara ita ce karo na farko da jam’iyyar Accord ta samu damar lashe zaɓen gwamnan Osun, cewar Channels.

Jam’iyyar ta samar da dandalin da Adeleke ya yi amfani da shi wajen neman wa’adinsa na biyu bayan ficewarsa daga PDP.

3. Davido (David Adeleke)

Fitaccen mawakin Afrobeats, Davido, wanda kuma ɗan uwan Gwamna Adeleke ne, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masu tallafa wa yaƙin neman zaɓensa.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso ya ce kan INEC bayan taya Adeleke murnar tazarce a Osun

An ruwaito cewa Davido ya rage wasu harkokinsa na waka domin jagorantar gangamin matasa na yaƙin neman zaɓen Adeleke.

Ya halarci tarukan kamfen tare da amfani da kafafen sada zumunta wajen kira ga matasa da su kasance cikin shiri tare da goyon bayan Adeleke.

4. A'ummar jihar Osun

Fiye da masu zaɓe miliyan ɗaya ne aka tantance domin jefa ƙuri’a a zaɓen, bisa ga sakamakon da INEC ta sanar.

Ƙuri’un da jama’ar Osun suka kada ne suka tabbatar da wanda zai jagoranci jihar, inda Adeleke ya samu damar komawa kan kujerar gwamna na wa’adi na biyu.

Adeleke ya yi nasara a zaben Osun
Mambobin jam'iyyar APC a hagu da Gwamna Ademol Adeleke na Osun. Hoto: Ademola Adeleke.
Source: Twitter

Waɗanda suka sha kaye

1. Bola Oyebamiji

Bola Oyebamiji, ɗan takarar APC kuma tsohon Kwamishinan Kuɗi na Osun, ya samu nasarar lashe ƙananan hukumomi 11 tare da kuri’u 444,815.

Sai dai duk da wannan sakamako, ya sha kaye a hannun Adeleke, wanda ya samu rinjaye a jimillar kuri’un jihar.

Ya mayar da hankali a kamfen ɗinsa kan ƙwarewarsa a harkokin gudanar da kuɗi da kuma buƙatar samar da wani sabon salo na mulki.

Kara karanta wannan

Raɗaɗin faɗuwa: Yadda ƴan APC suka yi wa ɗan jarida dukan tsiya a rumfar zaɓe

2. Jam'iyyar APC

Jam’iyyar APC, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a Osun, ta tsayar da Oyebamiji a matsayin ɗan takararta.

Jam’iyyar ta zo ta biyu bayan samun gagarumin sakamako a wasu wuraren da take da ƙarfi a jihar.

Duk da goyon bayan wasu manyan jami’an gwamnati da ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan jam’iyyar, APC ta kasa kayar da gwamna mai ci.

APC ta sha kaye a zaben Osun
Shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda. Hoto: Professor Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

3. Rauf Aregbesola

Tsohon gwamnan Osun tsakanin shekarun 2010 zuwa 2018, Rauf Aregbesola, ya goyi bayan ɗan takarar ADC, Najeem Salaam.

Aregbesola, wanda shi ne sakataren ƙasa na jam’iyyar ADC, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda ake kallon za su iya samar da wata babbar ƙarfi ta uku.

Sai dai ADC ta zo matsayi na uku a zaɓen, yayin da Aregbesola ya kuma rasa rumfar zaɓensa, kamar yadda TheCable ta ce.

4. Monday Okpebholo

Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya jagoranci kwamitin zaɓen fidda gwani na APC wanda ya samar da Oyebamiji a matsayin ɗan takara bisa yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku ya ce duk da shan kayen dan takarar gwamnan ADC a zaben Osun

Daga bisani Okpebholo ya ziyarci Osun domin yi wa Oyebamiji kamfen, inda ya nemi ‘yan asalin Edo da sauran mazauna jihar su goyi bayan ɗan takarar APC.

Davido ya juyo kan gwamna Okpebholo

A baya, an ji cewa mawaki Davido, ya tura sako ga Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, bayan nasarar kawunsa Ademola Adeleke.

Okpebholo ya yi wa Adeleke ba'a kan yadda yake rawa, yana tambayar ko mutanen Osun sun gaji da ganin gwamnan yana rawa.

Bayan Adeleke ya yi nasara, Davido ya wallafa saƙo a Instagram yana cewa Okpebholo ya shirya, domin zai mayar masa da martani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.