Zaben Gwamna: Abubuwa 5 da Za Su Iya Taimakon APC Ta Karbe Jihar Osun
Osun - Jam’iyyar APC ta shiga zaben gwamnan jihar Osun da karfinta kuma a karshen makon nan za ta ga yadda ta kaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bayan rasa jihar Kudu maso yammacin Najeriyan a zaben 2022, APC ta yunkuro da karfinta domin ganin bayan Ademola Adeleke.
Rahoton nan ya duba wasu daga cikin abubuwan da za su iya yin tasiri har Osun ta koma hannun APC mai mulkin jihohi fiye da 30.

Source: Twitter
Abubuwan da za su taimaki APC a zaben Osun
1. Karfin gwamnatin tarayya
Ana ganin tasirin da jam’iyyar APC ta ke da shi a sama zai iya bada gudumuwa wajen kawo karshen gwamnatin Accord a birnin Osogbo.
Ban da gwamnatin tarayya, Bola Ahmad Tinubu yana da dadaddiyar alakar siyasa da jihar Osun da ke Kudu maso yammacin kasar nan.
A Najeriya, karfin gwamnatin sama ya kan ba jam’iyya mai mulki dama ta bangaren kudi, shirye-shirye da sauran dabarun lashe zabe.
2. Tasirin masu rike da mukamai
Akwai fitattun mutane daga jihar Osun da suka samu mukamai daga gwamnatin tarayya da ba za su so APC ta ji kunya ba.
Daga cikin wadanda ake takama da su a Abuja akwai irinsu Adegboyega Oyetola, Ajibola Basiru da kuma Dr. Charles Akinola.
Waidi Olajire Ayinla da Hon. Adekola Aliu duk samu rabota da mukaman tarayya. Haka kuma akai manya a Majalisar tarayya.
3. Goyon bayan wasu talakawa
Ana ganin cewa har gobe jam’iyyar APC tana da magoya baya a Osun, akwai wadanda sai inda karfinsu ya kare a zaben jihar.
Masoyan jam’iyyar za su dage domin su burge Bola Tinubu, su nuna masa jihar tashi ce musamman da ake hangen babban zaben 2027.
Wasu ayyuka da gwamnatin Tinubu ta yi da manfufofi da tsare-tsare da aka kawo a jihar za su taimaka mata wajen doke Adeleke.

Kara karanta wannan
Tinubu zai wallafa yadda aka kashe kudin da aka samu daga cire tallafin man fetur
4. Hadin kan jam’iyyar APC
Legit ta fahimci rikicin cikin gidan APC ya lafa a yanzu, kusan za a iya cewa kan yawancin ‘ya ‘yan jam’iyyar adawan a hade yake.
Akwai kyakkyawar alaka tsakanin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da talakawa da-dama da ke kananan hukumomin fadin jihar Osun.
Da alama dai mulkin da jam’iyyar ta yi tun daga 2014 lokacin da aka kafa APC zuwa 2022 ya ba ta damar samun gurbi a zuciyar mutane.

Source: Facebook
5. Goyon bayan wasu jam'iyyu
Sauran dalilan sun hada da hadakar siyasa daga sauran jam’iyyun hamayya da APC take samu.
‘Dan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu goyon baya daga tsagin jam’iyyar Accord Party karkashin Christopher Imumolen
Farfesa Christopher Imumolen da wani bangaren PDP da ke tare da tsohon gwamna Olagunsoye Oyinlola za su bi bayan APC ne a yau.
An kashe 'dan APC kafin zaben Osun
An ji cewa APC a jihar Osun ta zargi cewa wasu 'yan daba sun harbe Dele Ayegbo, dan uwan daraktan yakin neman zaben gwamna.
Kakakin APC a jihar, Kola Olabisi, ya bayyana cewa an aikata wannan aika-aika ne a kusa da gidansa da ke garin Esa-Oke a makon nan.
Jam'iyyar ta dora alhakin a kan mambobin jam'iyyar Accord Party tare da bukatar jami'an tsaro su gudanar da bincike gabanin zaben jihar.
Asali: Legit.ng

