Sanatan APC da Ya Yi Barazanar Kashe Ƴan Adawa Ya Ba Magoya baya Sabon Umarni
- Sanatan APC da ya umarci magoya bayansu su hallaka yan adawa na jam'iyyar Accord ya bukaci sabon abu daga wurin masoyansa a zaben Osun
- Sanata Francis Fadahunsi ya bukaci magoya bayansa su sanya ido sosai kan yadda ake gudanar da zaɓen gwamnan Osun da har yanzu ake yi
- Sanatan ya ja hankalin jama'a a Osun da wajen jihar bayan ya fito karara ya na neman magoya bayansa su hallaka yan adawa, amma ya gyara zancen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Sanatan da ke wakiltar Osun ta Gabas, Francis Adenigba Fadahunsi, ya bukaci magoya bayansa su sanya ido sosai kan yadda ake kaɗa ƙuri’u a zaɓen gwamnan jihar Osun.
Ana ci gaba da zaben gwamna a jihar Osun yau Asabar 15 ga watan Agusta, 2026 yayin da aka kammala kada kuri'a a wasu rumfunan zabe.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Fadahunsi ya yi kiran a saka ido kan sakamakon zaben ne yayin da yake magana da magoya bayansa a Ilesha, inda ya bukace su da su tabbatar da cewa masu zaɓe sun kaɗa ƙuri’unsu yadda ya kamata.
Sanatan APC ya bayar da umarni
The Cable ta kawo labarin cewa a wani bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, an ji sanatan yana umartar magoya baya su saka ido a kan abin da kowa ke zabe.
Ya bayyana cewa:
“Ku sanya ido kan ƙuri’ar, kada ku bari wani ya gaya muku, ku sanya ido a kanta. Duk wanda bai kaɗa ƙuri’a yadda ya kamata ba, ba ɗan wannan ƙasa na gaskiya ba ne.”
Kalaman Fadahunsi na zuwa ne kwanaki bayan ya jawo ce-ce-ku-ce kan wata magana da aka fassara a matsayin kira ga tashin hankali kan mambobin jam’iyyar AP a Ilesha.
Sanata ya jaddada magana kan zaben Osun
Sanatan ya kuma jaddada bukatar magoya bayansa su sanya ido kan tsarin kaɗa ƙuri’u domin tabbatar da cewa an kare zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.

Source: Original
Ya bukaci masu zaɓe su kasance masu lura da abin da ke faruwa a rumfunan zaɓe tare da tabbatar da cewa an ƙidaya ƙuri’un yadda aka kaɗa su.
Wannan na zuwa bayan sanatan ya yi gargadin cewa za a samu matsala idan aka ga mambobin AP a yankin, inda aka ruwaito ya ce ce masoyansa su kashe su.
Yan daba sun tarwatsa masu zaben Osun
A wani labarin, kun ji cewa an samu rikici a kada kuri’a a rumfar tsohon gwamnan Osun kuma tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola inda lamarin ya tayar da hankulan sauran jama'a.
Rahotanni sun ce ‘yan daban sun kori masu kada kuri’a daga rumfar, lamarin da ya haifar da fargaba tare da dagula tsarin zaben gwamnan da ake gudanarwa a wannan rana ta Asabar 15 ga watan Agusta, 2026.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da jami’an tsaro ba su bayyana cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da jiran matakan da za a dauka domin a kammala zaben lafiya kalau
Asali: Legit.ng

