Labarin rayuwar Adegboyega Oyetola wanda zai gaji Rauf Aregbesola

Labarin rayuwar Adegboyega Oyetola wanda zai gaji Rauf Aregbesola

A jiya ne ‘Dan takarar Jam’iyyar APC a zaben Jihar Osun Adegboyega Oyetola yayi nasara bayan ya doke ‘Dan takarar PDP Ademola Adeleke a karasahen zaben da aka yi a Yankin Osogbo da kuma Ife na Jihar.

Labarin rayuwar Adegboyega Oyetola wanda zai gaji Rauf Aregbesola
Adegboyega Oyetola na APC ne sabon Gwamnan Jihar Osun
Asali: Depositphotos

A dalilin haka ne mu ka kawo maku takaitaccen bayani game da sabon Gwamnan na Jihar Osun:

1. Adegboyega Oyetola yayi karatu ne a Jami’ar Legas inda ya karanta harkar inshora a 1978.

2. Daga baya Oyetola ya sake yin Digiri na biyu a Jami’ar a bangaren tattali a shekarar 1990.

3. Oyetola yana cikin Kungiyar Masana harkar inshore da tattali na Landan da kuma gida Najeriya.

4. Sabon Gwamnan ya fara aiki ne da Kamfanin Inshora na Leadway bayan ya kammala karatu.

5. Oyetola yayi bautar kasa ne a Garin Maidguri da ke Arewacin Najeriya bayan ya gama Digiri.

KU KARANTA: Abubuwan da za su sa APC tayi nasara a karashen zaben Osun

6. Bayan Oyetola ya kai koli a Kamfanin Leadway sai kuma ya koma Kamfanin inshora na Crusader a matsayin Manaja.

7. Daga nan kuma Oyetola ya koma wani kamfanin na Corporate Alliance inda ya rike babban Jagora na kamfanin.

8. Daga nan ne dai Adegboyega Oyetola ya bude kamfanin sa mai zaman kan sa mai suna Silvertrust a 1990.

9. Oyetoga yana Mataimakin Shugaban kamfanin mai na Paragon ne aka nada sa Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamantin Jihar Osun.

10. Daga nan ne Gwamna Rauf Aregbesola ya dauko sa domin ya gaje sa a matsayin Gwamna kuma a jiya ya lashe zaben Gwamna da aka yi.

Yanzu dai Gboyega Oyetola zai karbi mulki daga hannun Mai gidan sa Gwamna mai shirin barin-gado watau Rauf Aregbesola. Gboyega Oyetola ya da aure da kuma ‘Ya ‘ya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel