Bayan Tumurmusa Shi a Zabe, Gwamna Adeleke Ya Aika Sako ga Dan Takarar APC

Bayan Tumurmusa Shi a Zabe, Gwamna Adeleke Ya Aika Sako ga Dan Takarar APC

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya aika sa sako ga abokin hamayyarsa Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC bayan nasarar da ya samu a zaben gwamna
  • Ademola Adeleke ya gayyaci abokin hamayyarsa daga jam’iyyar APC da ya zo su yi aiki tare domin ci gaban jihar Osun
  • Gwamnan ya bayyana shirin kafa kwamitin sulhu domin hada kan ‘yan Osun bayan rarrabuwar kawuna da aka samu yayin yakin neman zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan abokin hamayyarsa Bola Oyebamiji, na jam'iyyar APC.

Gwamna Adeleke ya ce Bola Oyebamiji ne ya kamata ya kira shi ya taya shi murna, ba shi ne zai kira Oyebamiji ba.

Adeleke ya aika sako ga Oyebamiji
Gwamna Ademola Adeleke da Munirudeen Bola Oyebamiji Hoto: Bola Oyebamiji, Sen Ademola Adeleke
Source: Twitter

Adeleke ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da Channels Tv ta yi da shi a shirin Sunday Politics, sa’o’i kadan bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Mutane 3 daga gidan Adeleke da suka shiga siyasa kuma suka shahara a tarihi

Da aka tambaye shi ko zai tuntubi dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), gwamnan ya ce Oyebamiji ne ya kamata ya fara tuntubarsa idan yana son nuna wayewa.

“Ba ni ne ya kamata na tuntube shi yanzu ba, saboda ni ne na lashe zaben kuma an sanar da ni a matsayin wanda ya yi nasara. Idan yana son nuna wayewa, shi ne ya kamata ya kira ni ya ce yana taya ni murna,”

Adeleke ya gayyaci Oyebamiji

Duk da cewa ya ce Oyebamiji ne ya kamata ya fara tuntubarsa, Adeleke ya mika gayyata ga abokin hamayyarsa da ya yi aiki tare da gwamnatinsa tare da kawo dabarun da za su amfani jihar.

“Amma a yanzu, ina amfani da wannan dama da na samu a gidan talabijin na kasa wajen mika hannun zumunci gare shi. Ya zo mu yi magana. Idan kana da wata shawara, ka fada mini, zan gabatar da ita. Idan shawarar tana da amfani, zan yi amfani da ita; abu daya shi ne jihar Osun ita ce a farko,” ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An gwabza tsakanin Davido da dan majalisa kan zaben gwamnan Osun

Adeleke zai sulhunta ‘yan siyasa

Adeleke ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi kokarin warkar da rabuwar kawuna a siyasar jihar da aka samu yayin yakin neman zaben.

Ya bayyana shirin kafa kwamitin sulhu da zai hada abokan hamayyarsa na siyasa da sauran masu ruwa da tsaki domin hada kai wajen bunkasa jihar.

“Zan nemi kafa kwamitin sulhu domin hada kan al’ummar Osun. Zan gayyaci hatta abokan hamayyarmu; idan kuna da wata shawara, ku kawo ta domin mu hada hannu mu mai da Osun babbar jiha,” in ji gwamnan.
Adeleke ya bukaci Oyebamiji ya taya shi murna
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun Hoto: Pelumi Olajangbesi
Source: Facebook

Tinubu ya aika sako ga Adeleke

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Ademola Adeleke murna kan nasarar da ya samu a zaben jihar Osun.

Shugaba Tinubu wanda ya taya Gwamna Ademola Adeleke, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar, ya ce nasarar ta tabbatar da amincewar al’ummar jihar gare shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng