Akuya Ta Zama Silar Arzikin Sanata Dino Melaye har Ta Kai Ya Mallaki Motoci 200

Akuya Ta Zama Silar Arzikin Sanata Dino Melaye har Ta Kai Ya Mallaki Motoci 200

  • Dino Melaye ya bayyana cewa ya saye akuya tun yana shekara 12, kuma da haka ya biya kudin karatu a sakandare da ABU Zari
  • Ya yi ikirarin fara zuba jari a kasashen waje tun yana karami, ya sa kudinsa a kamfanonin Apple, Microsoft, Uber da kuma Zoom
  • Hukumomin yaki da barna irin su EFCC da ICPC ba su taba gayyatarsa ba, Dino ya ce hakan ya tabbatar da bai mallaki kudin sata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon sanata a mazabar Kogi ta yamma, Dino Melaye ya yi magana game da silar dukiyar da ya mallaka a yau.

Sanata Dino Melaye ya yi watsi da mummunan zaton da wasu suke yi masa, ana ganin da dukiyar siyasa ne yake facaka.

Dino Melaye
Sanata Dino Melaye da wata akuya tana kiwo Hoto: Dino Melaye/Getty Images
Source: UGC

Dino Melaye bai ganin kan shi attajiri

A wata hira da aka yi da shi a shirin KaaTruths kuma aka daura a Youtube, babban ‘dan siyasar ya fadi inda ya samu kudinsa.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya faɗa kan matar aure da 'ya'yanta 2 cikin dare, Allah ya musu rasuwa a Kaduna

Duk da kallon da ake yi masa, Melaye ya ce bai sa kan shi cikin attajirai, sai dai yana ganin cewa ya samu dukiyar rufin asiri.

A wannan tattaunawa ne tsohon ‘dan majalisar ya bayyana cewa ya mallaki motoci 200 kuma har yanzu yana kara sayo wasu.

Sanata Dino ya ce bai saci kudi ba

Duk da shekarun da ya shafe a Majalisar wakilai da ta Dattawa a kasar nan, ‘dan siyasar ya ce bai saci dukiyar al’umma ba.

Premium Times ta rahoto cewa Sanata Melaye ya kuma shaida wa duniya bai taba samun kwangilar gwamnati ba tun da yake.

Da a ce akwai kudin haramun a dukiyarsa, tsohon ‘dan takaran gwamnan ya ce da hukumomin yaki da sata sun bincike shi.

Dino Melaye ya ce:

"Da kudin haramun gare ni, da na taba satar dukiyar gwamnati, ba zan rika sukar gwamnati ba, saboda da tuni sun kama ni.

Kara karanta wannan

Wakar Rarara: Ɗan fim ya yi shagube ga Pantami game da shiga siyasa tsundum

"Ban taba samun gayyata daga EFCC da ICPC ba ko wata hukumar yaki da rashin gaskiya a kasar nan domin ban taba yin kwangilar gwamnati - ko a matakin tarayya ko jiha ba."

Ya aka yi Dino Melaye ya samu kudi?

Akuya ta zama silar arzikin Dino

Da yake bayyana sirrin dukiyarsa, Sanata Dino Melaye ya danganta lamarin da kiwon akuya da ya yi tun yana karamin yaro a duniya.

"Lokacin ina shekara 12, na saye akuya kuma wannan akuyar ta rika haihuwa, sai in saida yaran in biya kudin makarantan sakandare.
"Daga haihuwar akuyan na biya kudin WAEC, JAMB da shekara ta farko da ta biyu na a jami’ar Ahmadu Bello.
"A haka na biya duka kudin makaranta na daga wannan kudi da aka juya. Da na kai shekara 18, ta kai na fara juya kudi a kasashen ketare, amma ba kudi masu nauyi ba."

- Dino Melaye

Dino ya sa kudi a kamfanonin kasashen waje

A cewar ‘dan adawan, mutum bai bukatar kudi masu yawa kafin ya fara irin kasuwancin da ya soma a kasashen waje a lokacin.

Kara karanta wannan

'Lokaci ya wuce da za a zabi mutum saboda Kwankwaso': 'Dan Majalisar Kano

Daga wannan kudi ne ya saye hannun jarin kamfanonin Apple da Microsoft shekaru 27 lokacin ana canza Euro a kan N60 a kasuwa.

A haka ya saye hannun jari a Uber da Zoom lokacin har ana yi masa dariya, amma a lokacin COVID-19 sai ga shi ya samu kazamar riba.

Ga bangaren hirar da Dino ya gutsuro, ya sa a shafin Facebook.

PDP: Dino ya ce jam'iyyar adawa ta shiga garari

An samu rahoto Dino Melaye ya ce PDP ta rasa alkibla kuma ta koma tamkar wata gawa da ke bukatar a birne ta, don haka ya yi bankwana da ita a hukumance.

Melaye ya bayyana cewa jam'iyyar adawar ta koma hannun mutane da ke gudanar da ita tamkar ta hanyar amfani da wani 'remote' wanda hakan ya hana ta ci gaba.

Ya jaddada cewa babu sauran wata adawa ta rage wa PDP da haka ne aka ji ya shiga tafiyar ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng