Wata Sabuwa: Ɗan majalisar Wakilai Ya Fice daga Jam'iyyar PDP, Bayanai Sun Fito
- Hon. Oluwole Oke, dan majalisar wakilai daga Osun, ya fice daga jam’iyyar PDP bayan shekara 24 yana wakiltar mazabar Obokun/Oriade
- Ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne bayan tuntubar abokan siyasarsa, duk da cewa bai bayyana sabuwar jam’iyyarsa ba
- Majiyoyi daga Kudu maso Yamma sun ce Oke na da burin tsayawa takarar mataimakin gwamna a 2026 ko sanata a 2027 karkashin APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahotanni na nuni da cewa wani ɗan majalisar wakilai, Oluwole Oke, ya fice daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
An rahoto cewa Oluwole Oke, ya shafe wa’adi shida (shekaru 24) kenan yana wakiltar mazabar Obokun/Oriade daga jihar Osun, a majalisar wakilai.

Asali: Twitter
Dan majalisar wakilai ya fice daga PDP
Jaridar Punch ta rahoto cewa dan majalisar ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne bayan tattauna wa da abokan siyasarsa, sauran abokai da kuma iyalansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Oluwole Oke ya rubuta takardar murabus dinsa ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, kuma an tura ta ga shugaban jam’iyyar PDP na gunduma ta 7 da ke ƙaramar hukumar Obokun, jihar Osun.
Hon. Oluwole Oke ya tabbatar da murabus ɗinsa a taƙaice lokacin wata hira ta wayar tarho da wakilin jaridar a ranar Laraba.
"Na fice daga jam’iyyar PDP," inji Hon. Oluwole Oke.
Sai dai bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, amma ya bukaci magoya bayansa da su fice daga PDP su jira matakin da zai ɗauka na gaba.
Hasashe kan dalilin dan majalisar na barin PDP
Wasu majiyoyi daga yankin Kudu maso Yamma sun danganta ficewar Hon. Oluwole Oke daga jam’iyyar PDP da burinsa na tsayawa takara a 2026 da 2027.
Ana zargin dan majalisar ya shiga tattaunawa da shugabannin jam’iyyar APC a jihar Osun tun kafin zaben gwamna na baya.
Majiyoyin da suka san harkokin siyasa a jihar sun ce Oke na duba yiwuwar tsayawa takarar mataimakin gwamna a 2026 ko kuma takarar sanata na Osun ta Gabas a 2027 a karkashin APC.

Asali: Facebook
PDP na adawa da takarar dan majalisar
An ce ya fara wannan tattaunawar ne tun a 2022 lokacin da APC ke kokarin samun goyon bayansa a zaben gwamnan jihar.
Haka kuma, wasu jiga-jigan PDP a karamar hukumar Obokun na nuna adawa da yunkurinsa na sake komawa majalisar wakilai a 2027, abin da ka iya zama dalilin ficewarsa daga jam’iyyar.
Sai dai a cikin wasikar murabus da ya aike, dan majalisar tarayyar bai bayyana dalilin ficewar tasa ba, inji rahoton Premium Times.
Gwamnan Delta ya fice daga PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a wani muhimmin sauyin lamuran siyasa a jihar.
Ya bayyana sauyin ne a wata ganawa ta sirri da aka yi a gidan gwamnati dake Asaba, inda jiga-jigan jam’iyyar APC suka tarbe shi cike da farin ciki.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar jihar Delta ke tafasa, yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng