Obi Ya Dauko Irin Salon Atiku, Ya Ce zai Maido Tallafin Man Fetur

Obi Ya Dauko Irin Salon Atiku, Ya Ce zai Maido Tallafin Man Fetur

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027
  • Obi ya ce zai fara magance matsalar cin hanci da rashawa a ƙasar kafin dawo da tallafin man fetur domin tabbatar da cewa ba a karkatar da kudin gwamnati ba
  • Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su zaɓi ‘yan takarar NDC a dukkan matakai a zaɓen 2027 domin, a cewarsa, magance matsalolin ƙasar nauyin kowa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sokoto – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC), Peter Obi, ya yi magana kan matakin da zai ɗauka kan tallafin man fetur idan ya yi nasara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya fada wa 'yan Arewa muhimmancin goyon bayan Tinubu

Obi ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa gwamnatinsa za ta fara yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Dan takarar NDC, Peter Obi
Peter Obi a wajen wani taro yana jawabi a kwanakin baya. Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Obi zai maido tallafin man fetur

Vanguard ta wallafa cewa Obi ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wani taron tattaunawa da aka shirya domin takarar Obi da Kwankwaso a Sokoto.

Ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Najeriya, yana mai cewa gwamnatinsa za ta magance matsalar a dukkan ɓangarorin ƙasar idan aka zaɓe ta.

Ya ce:

“Mutane suna magana ne kan tallafi, amma abin da ya shafi komai shi ne cin hanci da rashawa. Idan muka kawar da cin hanci da rashawa, ina tabbatar muku za mu dawo da tallafi.
“Matsalar Najeriya ita ce cin hanci da rashawa, don haka idan aka zaɓe mu, za mu dakatar da dukkan nau’o’in cin hanci da rashawa a kowane ɓangare na ƙasar.”

Me Obi zai fi bai wa muhimmanci?

Obi ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da zaɓen 2027 wajen zaɓar ‘yan takarar NDC a dukkan matakai, yana mai cewa magance matsalolin ƙasar nauyin kowa ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Ya ce jam’iyyar ta himmatu wajen gudanar da abin da ya kira siyasar kulawa da yi wa ‘yan Najeriya hidima.

Tsohon gwamnan Anambra ya nuna damuwa kan halin tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa idan aka zaɓe shi, zai yi amfani da albarkatun Najeriya wajen inganta tsaro, ilimi da sauran fannoni.

“Bayan haɗin kan ƙasa da tsaro, ilimi shi ne babban abin da za mu fi bai wa muhimmanci,”

in ji Obi.

Daily Trust ta rahoto cewa ya kuma yi alƙawarin haɗa dukkan manyan biranen jihohi da layin dogo domin sauƙaƙa harkokin tattalin arziki da bunƙasa ci gaba.

Bayanin Kwankwaso a Sokoto

Da yake magana, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Dr Rabi’u Kwankwaso, ya ce ziyarar ta kasance ne domin tattaunawa da mazauna Sokoto da neman goyon bayansu gabanin zaɓen 2027.

Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya ce tawagar ta fara ziyartar Sarkin Musulmi, wanda a cewarsa ya yi musu addu’ar samun nasara tare da fatan alheri.

Yan NDC a gidan Sarkin Musulmi
Lokacin ganawar Sarkin Musulmi da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Tun da farko, ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na NDC, Dr Shamsudeen Haido, ya yi alƙawarin samar da shugabanci nagari idan aka zaɓe shi a 2027.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hango abin da ba zai wa 'yan Najeriya daɗi ba kan dawo da tallafin fetur

Jawabin Sarkin Musulm

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta juna, su kare haɗin kan Najeriya tare da guje wa kalaman batanci da zage-zage.

Sultan ya yi wannan kiran ne ranar Litinin lokacin da ya karɓi bakuncin Peter Obi, Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na NDC, Dr Shamsu Haido.

Ya ce ‘yan siyasa na da damar gabatar da manufofinsu da neman goyon bayan masu zaɓe, amma ya kamata su yi hakan cikin mutunta doka da kuma mutanen da ke da ra’ayoyin siyasa daban da nasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng