Davido Ya Tafka Katobara, Lauya Ya Nuna Kuskuren Babban Mawaki

Davido Ya Tafka Katobara, Lauya Ya Nuna Kuskuren Babban Mawaki

  • Lauya Timothy Tugbiyele ya bukaci mawakin Afrobeats, Davido, da ya ba Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, hakuri kan wallafa sakamakon WAEC da ake zargin na gwamnan ne
  • Tugbiyele ya ce bai kamata Davido ya mayar da martani da kansa ga kalaman gwamnan ba, domin ya kamata Gwamna Ademola Adeleke ko wani jami’in gwamnatinsa ya mayar da martanin
  • Lauyan ya ce siyasa bai kamata ta koma cin mutunci ba, inda ya bukaci Davido ya nuna tawali’u ya kuma nemi afuwar Okpebholo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Wani lauya kuma marubuci, Timothy Tugbiyele, ya bukaci mawakin Afrobeats David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, da ya ba Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, hakuri.

Lauyan ya bukaci Davido ya bayar da hakurin ne kan wani sakamakon jarabawar WAEC da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Lauya ya ce Davido ya yi kuskure
Babban mawai a Najeriya, Davido Hoto: Davido
Source: Instagram

Jaridar The Punch ta ce Tugbiyele ya yi wannan kiran ne a wani bidiyo yayin da yake tsokaci kan rikicin siyasar da ake fama da shi gabanin zaben gwamnan jihar Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.

Davido ya yi wa gwamna shagube

A ranar Juma’a ne Davido ya wallafa abin da ya bayyana a matsayin sakamakon WAEC na Okpebholo, jim kadan bayan gwamnan Edo ya yi wa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ba’a kan yadda yake yawan rawa.

Okpebholo ya soki salon shugabancin Adeleke ne yayin da yake yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Oyebamiji, wanda aka fi sani da AMBO.

Bayan kalaman, Davido, wanda ke fafutukar ganin kawunsa Adeleke ya samu wa’adi na biyu, ya wallafa sakamakon WAEC da ake zargin na Okpebholo ne ba tare da wani rubutu a kai ba.

Okpebholo ya cancanci a nemi afuwarsa

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An tura saƙo ga Amurka da Birtaniya don su hukunta sanatan Najeriya

Da yake magana kan lamarin, Tugbiyele ya ce bai kamata Davido ya mayar wa gwamnan martani da kansa ba.

“Na kalli wani bidiyo lokacin da Gwamna Okpebholo ya kira gwamnan jihata, Adeleke, gwamnan rawa. Sai dan uwan gwamnan, David Adeleke, ya mayar da martani ta hanyar wallafa sakamakon WAEC na kammala makarantar sakandare na Gwamna Okpebholo, gwamnan Edo.” In ji shi

A cewar lauyan, duk da cewa sakamakon da ake zargin na Okpebholo ne bai yi kyau ba, bai kamata a yi amfani da shi wajen yi masa ba’a ba.

“Sakamakon bai yi kyau sosai ba, amma hakan na iya faruwa. Gwamnan ya sake rubuta jarabawar. Ba mu san da hakan ba, amma ina ganin wallafar Davido, David Adeleke, ba ta dace ba.” In ji shi

Adeleke ya kamata ya mayar da martani

Tugbiyele ya ce Adeleke zai iya mayar wa takwaransa na Edo martani ta hanyoyin hukuma maimakon barin Davido ya shiga tsakaninsu.

"Gwamna Adeleke, Ademola Adeleke, ya kamata ya mayar wa takwaransa gwamna martani, ko ya sa daya daga cikin ma’aikatansa, watakila kwamishinan yada labarai ko mai ba shi shawara na musamman, ya mayar da martani. Ba Davido, David Adeleke ba.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya jawo magana, ya bukaci masoyansa su 'kashe' abokan hamayya

Lauyan ya kuma jaddada cewa Davido da Okpebholo suna da matsayi daban-daban, don haka bai kamata su rika mu’amala da juna a matsayin masu matsayi iri daya ba.

Lauya ya ba Davido shawara
Babban mawaki a Najeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido Hoto: Davido
Source: Facebook
"David Adeleke da gwamnan jiha ba su da matsayi iri daya. Ba su da matsayi guda. Ba su cikin aji guda.” In ji shi.

Tugbiyele ya bayyana wallafar Davido a matsayin rashin girmamawa, inda ya roki mawakin da ya ba Okpebholo hakuri.

"Ina ganin abin da Davido ya yi rashin girmamawa ne, kuma ina rokon sa da ya nuna tawali’u ya nemi afuwa.” In ji shi.

Shehu Sani ya yi wa Davido martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Shehu Sani, ya yi watsi da kiran fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido.

Sanata Shehu Sani ya yi watsi da kiran na Davido na neman Shugaban Amurka Donald Trump da kasashen duniya su sanya ido kan zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng