An Samu Kudi: Kamfanin NNPCL Ya Bayyana Yawan Ribar da Ya Samu a 2025

An Samu Kudi: Kamfanin NNPCL Ya Bayyana Yawan Ribar da Ya Samu a 2025

  • NNPCL ta sanar da samun ribar Naira tiriliyan 7.2 bayan haraji a shekarar 2025, daga cikin kudaden shiga da suka kai Naira tiriliyan 34.5
  • Kamfanin ya ce ribar ta karu da sama da kashi 30 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda ya samu Naira tiriliyan 5.76
  • NNPCL ta kuma bayyana cewa ta tura Naira tiriliyan 22.3 ga Gwamnatin Tarayya a matsayin haraji, kudin sarauta da sauran kudaden da ta biya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kamfanin Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya ce ya samu ribar Naira tiriliyan 7.2 bayan cire haraji a shekarar 2025.

Babban Daraktan Rukunin Kamfanin (GCEO) na NNPCL, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar da bayanan binciken kudi na shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da sanarwa, ya hana bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya

Yawan makudan kudi da NNPCL ta samu a 2025
Shugaban kamfanin mai na NNPCL, Bayo Ojulari. Hoto: NNPC Limited.
Source: Getty Images

Ojulari ya ce ribar ta samu ne daga kudaden shiga da kamfanin ya samar, wadanda suka kai Naira tiriliyan 34.5 a shekarar, cewar Daily Trust.

Bambanci a ribar da aka samu a 2024

Shugaban ya ce ribar ta wakilci karin sama da kashi 30 cikin 100 idan aka kwatanta da ribar da aka samu a shekarar 2024.

Sai dai, jimillar kudaden shigar kamfanin ta ragu da Naira tiriliyan 10.6 daga Naira tiriliyan 45.1 da aka samu a shekarar 2025.

Ya ce NNPCL ta biya Gwamnatin Tarayya haraji, kudin sarauta da sauran kudaden da suka kai Naira tiriliyan 22.3.

Ya kara da cewa kamfanin ya samar da matsakaicin ganga miliyan 1.77 na danyen mai a kowace rana, da kuma kafufin iskar gas biliyan 7.2 a kowace rana.

An dai tuna cewa NNPCL ta samu ribar Naira tiriliyan 5.76 a shekarar 2024 wanda ya nuna bai kai abin da ya samar a 2025 ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Ojulari ya ce:

“Abin da muka cimma a shekarar 2025 ya nuna irin abin da tsayayyen aiki cikin tsari da kuma ƙwararrun ma’aikata za su iya samarwa.
“Mun na ƙara ƙarfafa kudaden shigar kamfanin, ƙara yawan man da muke samarwa, tare da saka hannun jari ga ma’aikata da kadarorin da za su taimaka wajen dorewar daraja ga masu hannun jari, al’ummomi da al’ummar Nijeriya.”

Ya kara da cewa kamfanin ya samar da matsakaicin ganga miliyan 1.77 na danyen mai a kowace rana, da kuma kafufin iskar gas biliyan 7.2 a kowace rana.

An dai tuna cewa NNPCL ta samu ribar Naira tiriliyan 5.76 a shekarar 2024 wanda ya nuna bai kai abin da ya samar a 2025 ba.

NNPCL ya zuba biliyoyi a asusun gwamnati

A baya, an ji cewa NNPCL ya tura Naira tiriliyan 6.286 zuwa Asusun Tarayya tsakanin Janairu da Yunin 2026, ƙasa da rabin abin da ta biya a shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadada a Afrika, ya ci burin komawa samun ribar $35bn nan da 2030

Kamfanin ya samu ribar Naira biliyan 535 a watan Yuni duk da ɗan raguwar yawan ɗanyen mai da aka haƙo.

Ayyukan bututun iskar gas na OB3 da AKK sun kusa kammala, inda ake sa ran fara samar da iskar gas nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.