Atiku Ya Ragargaji Tinubu kan Karbo Bashin Kusan Naira Tiriliyan 2

Atiku Ya Ragargaji Tinubu kan Karbo Bashin Kusan Naira Tiriliyan 2

  • Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan yadda aka kashe kudin da Najeriya ta ci bashi kafin neman sabon bashin dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya
  • Atiku ya ce bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 166.79, yana mai tambayar gwamnatin tarayya dalilin ci gaba da neman karin bashi duk da ikirarin samun karin kudin shiga
  • Ya kuma bukaci gwamnati ta bayyana ayyukan da za a gudanar da sabon bashin, wadanda za su amfana da su da kuma yadda za a bibiyi sakamakon ayyukan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi bayani kan yadda aka yi amfani da kudin da gwamnatin tarayya ta ci bashi kafin neman karin $1.5bn daga Bankin Duniya.

Kara karanta wannan

'Za a yi babban haɗari idan Tinubu ya bari aka yi faretin 1 ga Oktoba,' Ayodele

Hakan na zuwa ne yayin da sabbin bayanai suka nuna cewa bashin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 166.79 a watan Yunin 2026.

Atiku Abubakar da shugaba Bola Ahmed Tinubu
Atiku Abubakar a hau da shugaba Bola Ahmed Tinubu a dama. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Atiku ya yi wa Tinubu tambayoyi

Daily Trust ta wallafa cewa Atiku ya bayyana matsayarsa ne cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kamfen na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar.

Ya ce iyalai na fama da tsadar abinci, man fetur da wutar lantarki, yayin da bashin kasar ke ci gaba da karuwa.

Atiku ya ce an bukaci ’yan Najeriya su jure wasu tsauraran matakai na tattalin arziki da alkawarin cewa hakan zai samar da kudin gudanar da ayyukan raya kasa.

Dan takarar shugaban kasar ya tambayi shugaba Bola Tinubu ya nuna fa'idar da aka samu a bashin da ya ciwo a baya.

Karin tambayoyi ga Tinubu

Atiku ya ce sababbin wuraren da ake son amfani da bashin, wadanda suka hada da muhalli, tallafin jama’a da bunkasa kananan yara, na iya magance wasu bukatu.

Sai dai ya ce sunayen shirye-shiryen kadai ba su isa ba, yana bukatar gwamnati ta bayyana yadda aka kashe bashin da aka karba a baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Ya bukaci a wallafa jerin ayyukan da za a gudanar, al’ummomin da za su amfana, manufofin kowanne shiri, sharudan karbar bashin da yadda za a raba kudin.

Atiku ya ce ya kamata kuma a samar da jadawalin da zai bai wa ’yan Najeriya damar bibiyar yadda ake aiwatar da ayyukan.

Maganar karuwar bashi

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma kalubalanci gwamnatin Tinubu kan karuwar bashin kasar duk da ikirarin cewa kudin shiga sun karu bayan cire tallafin man fetur.

This Day ta wallafa cewa ya ce idan kudin da gwamnati ke samu sun karu, ya kamata a bayyana dalilin da ya sa bashin kasar ke ci gaba da karuwa.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar da abokin takarar shi na ADC. Hoto: Atiku
Source: Facebook

Atiku ya kuma bayyana cewa idan ’yan Najeriya sun sha wahala sakamakon matakan tattalin arzikin gwamnati, ya kamata a nuna musu sakamakon da aka samu.

Gargadi kan faretin 1 ga Oktoba

A wani labarin, mun ruwaito cewa Primate Babatunde Ayodele ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya soke faretin ranar ’yancin kan Najeriya da aka shirya gudanarwa ranar 1 ga Oktoba.

Sai dai malamin addinin Kiristan bai bayyana takamaiman irin hadarin da yake magana a kai ba ko kuma hujjar hasashen nasa.

Ayodele ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da kada su karbi wani abu daga ’yan siyasa a zaben 2027, yana mai cewa su yanke shawarar zabe bisa cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng