Akwai Matsala: An Dauko Batun da Zai Tsoratar da Yan Arewa kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce dawowar tallafin man fetur zai gurgunta Arewacin Najeriya tare da kara jefa mutane cikin talauci
- Yilwatda ya ce dawo da tallafin zai iya kawo karshen ayyukan tituna, gas da takin zamani da ake gudanarwa a Arewacin kasar
- Ya bayyana wasu ‘yan takarar ADC da suka fice daga takara tare da komawa APC a matsayin mutanen da suka zo domin ba da gudunmawa ga jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sake yi gargadin da ka iya tsoratarda yan Arewa kan dawo da tallafin man fetur.
Farfesa Nentawe ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na dawo da tallafin fetur zai gurgunta Arewacin Najeriya, yana mai cewa hakan zai kawo karshen ayyukan tituna, gas da takin zamani tare da sake jefa ‘yan Arewa cikin talauci.

Source: Twitter
Vanguard ta ce Yilwatda ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Sakatariyar APC da ke Abuja, yayin da yake karbar ‘yan takarar ADC na kujerun majalisun dokokin jihoji, wadanda suka janye tare da sauya sheka zuwa APC.
Gimbiya Aslam Aliyu, wadda aka fi sani da Gimbiyar Kauran Namoda, ce ta jagoranci tawagar, yayin da Hon. Mohammed Hassan, dan takarar ADC daga Jihar Zamfara, ya yi magana a madadin tawagar.
APC ta hango matsala ga Arewa
Da yake jawabi ga masu sauka shekar, Farfesa Yilwatda ya kalubalanci alkawarin ‘yan adawa na dawo da tallafin man fetur.
Shugaban APC ya ce:
“Gidajen rediyon Hausa suna gaya mana cewa za su dawo da tallafin. Ina ci gaba da tambaya, ta yaya za su dawo da tallafin?
"Shin suna nufin za su dakatar da duk wadannan ayyukan gina tituna ne saboda suna son dawo da tallafin? Domin ba za a samu kudin gudanar da wadannan ayyukan ba idan tallafi ya dawo."
“Masu cin gajiyar bashin karatu, mafi yawansu daga Arewa suke. Muna da da yawa daga cikinsu a wannan bangare na kasar. Shin mu dakatar da shi? Tambayoyin suna da yawa. Ba za mu iya ambatar su duka a nan ba.”
An dauko halin da jihohin Arewa suka shiga
Shugaban jam’iyyar APC ya kuma tuna da halin da jihohin Arewa ke ciki game da kudaden shiga kafin gwamnatin yanzu.
“Daga cikin kusan jihohi 30 da ba su iya biyan albashi a Najeriya, dukkan jihohin Arewa, babu ko daya da ta iya biyan albashi a shekarar 2023. Shin mu ce jiharmu yanzu ta koma baya?” in ji shi.
Yilwatda ya yi watsi da ikirarin ADC da ake yadawa a shirye-shiryen gidajen rediyon Hausa cewa Shugaba Tinubu ya yi watsi da Arewa.

Source: Facebook
Ya kara da cewa hanyar Abuja zuwa Kano “ta kusa kammaluwa”, yayin da bangaren aikin titin Maiduguri zuwa Kano ya “kusa kammala kashi 50 cikin 100”.
Ya lissafta wasu hanyoyin da ake gudanar da ayyukansu, ciki har da hanyar Jos zuwa Akwanga, hanyar Kwara zuwa Mokwa a Jihar Neja, hanyar Sokoto zuwa Kebbi, hanyar Kano zuwa Daura, da hanyoyin da suka hada Zariya da Illela a Jihar Sokoto.
APC ta gargadi yan Najerirya kan Atiku
Kun ji cewa jam’iyyar APC ta yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su zaɓi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta zargi Atiku da hannu a cikin wasu tsofaffin badakalar cin hanci da rashawa, tana mai cewa bai kamata a sake ba shi babban matsayi ba.
Asali: Legit.ng


