A Karo na 4, Majalisar Tarayya Ta Tsawaita Wa'adin Kasafin Kudin Bara a Najeriya
- Majalisar Wakilai ta tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren ayyukan raya kasa na kasafin kudin 2025 zuwa 31 ga Disamba, 2026
- Wannan shi ne karo na hudu da aka tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin ayyukan raya kasa na 2025
- Wannnan mataki ne zai bai wa ma’aikatu da hukumomin gwamnati karin watanni uku domin kammala ayyuka da amfani da kudaden kasafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren ayyukan raya kasa na Kasafin Kudin 2025 a karo na hudu, inda ta daga ranar karewa daga 30 ga Satumba zuwa 31 ga Disamba, 2026.
Rahotanni sun ce an amince da tsawaita wa'adin kasafin ne yayin zaman majalisar na ranar Talata, bayan Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Julius Ihonvbere, ya gabatar da kudirin.

Source: Facebook
Majalisa ta tsawaita wa'adin kasafin 2025
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan mataki na nufin cewa wa’adin aiwatar da kasafin ayyukan raya kasa na 2025, wanda tun farko ya kamata ya kare a ranar 31 ga Disamba, 2025, yanzu an tsawaita shi da karin shekara guda.
Majalisar Dokokin Tarayya ta fara tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin ne a watan Disamba 2025, inda ta daga ranar karewar zuwa 31 ga Maris, 2026.
Daga bisani ’yan majalisar suka kara daga wa’adin zuwa 30 ga Yuni, sannan daga baya suka kara lokacin zuwa 30 ga Satumba.
Majalisa ta yi karin wa'adi a baya
Wannana karin wa'adi da aka yi a karo na hudu ya zo ne kwana guda kafin wa’adin da aka tsawaita a baya ya kare.
A watan Yuni, Majalisar Wakilai ta amince da tsawaita wa’adin daga 30 ga Yuni zuwa 30 ga Satumba, inda ’yan majalisar suka ce har yanzu ba a kammala wasu manyan ayyuka da ke cikin kasafin 2025 ba.
Majalisar Dattawa ta riga ta amince da irin wannan tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Karin lokaci ga hukumomi
Bayan matakin da majalisar ta dauka a ranar Talata, ma’aikatu, da hukumomin Gwamnatin Tarayya za su samu karin watanni uku domin aiwatar da ayyuka da kuma amfani da kudaden da aka ware a karkashin kasafin na 2025.

Source: Facebook
A watan Disamba 2025, lokacin da Majalisa ta tsawaita wa'adin kasafin, Shugaba Bola Tinubu ya ce matakin zai taimaka wajen sakin kudaden da aka ware domin ayyukan raya kasa ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Lokacin da aka sake tsawaita wa’adin zuwa 30 ga Yuni, Fadar Shugaban Kasa ta ce an yi hakan ne domin tabbatar da kammala muhimman ayyuka da gina ababen more rayuwa.
Majalisar wakilai ta janye kudirinta
Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta tarayya ta janye kudirinta da ta fara karatu a kansa kan batun kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya.
Ta dauki wannan mataki ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura nasa kudirin kan wannan batu na kafa rundunar yan sandan jihohi.
Asali: Legit.ng

