Adeleke: Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani game da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Osun

Adeleke: Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani game da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Osun

Osun, Nigeria - A ranar Asabar, 15 ga watan Augustan 2026 ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da zaben gwamna a jihar Osun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gwamna Ademola Adeleke, wanda ya tsaya takara a inuwar jam'iyyar Accord ne ya samu nasara a zaben, bayan samun kuri'u mafi rinjaye.

Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke yana jawabi a taron masu ruwa da tsaki Hoto: @AAdeleke01
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa INEC ta tabbatar da Gwamna Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan kammala tattara sakamako daga dukkan kananan hukumomi 30 na Osun.

Adeleke, dan takarar gwamna a karkashin Accord ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Da wannan nasara, Adeleke ya samu damar ci gaba da jagorantar jihar Osun a wa’adin mulki na biyu, wanda zai zama na karshe kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Kara karanta wannan

Bayan tumurmusa shi a zabe, Gwamna Adeleke ya aika sako ga dan takarar APC

Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da zababben gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke.

1. Haihuwar Adeleke

An haifi Ademola Nurudeen Jackson Adeleke a ranar 13 ga Mayu, 1960 a birnin Enugu da ke Kudancin Najeriya, iyayensa su ne, Ayoola Adeleke da Nnena Esther Adeleke.

Shi dan asalin Jihar Osun ne, mahaifinsa musulmi ne wanda ya kasance sanata kuma Sarki mai mukamin Balogun na kasar Ede a Jihar Osun.

The Sun ta kawo cewa Adeleke ya girma ne tare da 'yan uwansa guda biyu: Adedeji Adeleke, mahaifi ga shahararren mawakin Najeriya nan Davido.

Sai kuma marigayi Isiaka Adeleke, wanda babban dan siyasar Najeriya ne, sanata a Jamhuriyya ta Biyu, kuma jagoran siyasa a jam'iyyar UPN. Isiaka ya rigamu gidan gaskiya a ranar 23 ga Afirilu, 2017.

2. Tarihin karatunsa

Ademola ya yi makarantar firamare ta Methodist Primary School da ke Surulere a Jihar Lagos. Daga baya ya koma tsohuwar jihar Oyo, inda ya ci gaba da karatunsa na firamare a makarantar Nawarudeen Primary School da ke Ikire.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An gwabza tsakanin Davido da dan majalisa kan zaben gwamnan Osun

Bayan ya kammala firamare, ya yi rajista tare da shiga makarantar sakandare ta The Seventh Day Adventist Secondary School.

Haka zalika ya halarci makarantar Ede Muslim Grammar School da ke Ede, inda a can ne ya kammala karatunsa na sakandare.

Daga bisani ya dunguma zuwa kasar Amurka inda ya shiga Jami'ar Jacksonville State University da ke jihar Alabama domin karanta fannin Shari'ar Hukunta Laifuka da Kimiyyar Siyasa.

A shekarar 2021 kuma, ya sami digirin farko na Kimiyya (BSc) a fannin Shari'ar Hukunta Laifuka daga kwalejin Atlanta Metropolitan State College, cewar rahoton Sahara Reporters.

3. Ya kasance dan kasuwa

Ademola Adeleke shahararren dan kasuwa ne kafin ya shiga siyasa, kuma ya kasance mai tallafa wa al'umma.

TVC News ta ruwaito cewa ya yi aiki a matsayin Darakta na Gudanarwa a kamfanin Guinness Nigeria Plc daga shekarar 1992 zuwa 1999.

Haka zalika, ya rike mukamin Babban Darakta na Gudanarwa na Rukunin Kamfanoni Pacific Holdings Limited, kamfanin da dan uwansa ke mallaka, daga shekarar 2001 zuwa 2016.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Davido ya yi magana kan nasarar kawunsa, ya cika da murna

Sannan ya taba yin aiki a matsayin 'dan kwangilar ayyuka a kamfanin aika saƙonni na Quicksilver Courier Company da ke Atlanta, Georgia a kasar Amurka, daga shekarar 1985 zuwa 1989.

Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a kamfen PDP Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

4. Yadda ya shiga siyasa

Ademola ya fara harkar siyasa ne a 2001 tare da marigayi yayansa, Isiaka Adeleke. Bayan rasuwar yayan nasa, ya tsaya takarar Sanatan Osun ta Yamma a 2017, inda ya samu nasara a karkashin inuwar PDP.

Vanguard ta ce ya gudanar da aikinsa a matsayin Sanata mai wakiltar shiyyar Osun ta Yamma har zuwa watan Yunin 2019. A baya, ya taba zama mamban jam'iyyar APC kafin ya koma PDP.

5. Fafatawa a zaben Osun 2018

A ranar 23 ga Yulin 2018, Ademola ya samu nasarar zama dan takarar gwamnan jihar Osun a PDP yayin zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

Ya fafata a zaben gwamnan Osun da aka gudanar a ranar 22 ga Satumban 2018 karkashin PDP. INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba a wani mataki mai cike da ce-ce-ku-ce, daga baya aka sake zabe.

Alhaji Gboyega Oyetola na jam'iyyar APC ya samu nasara kan Adeleke a zaben 2018 amma bai amince da sakamakon zaben ba, ya tafi kotu.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Gwamna Adeleke ya yi magana kan nasararsa, ya aika sako ga Tinubu

Duk da kotun zabe ta ba Adeleke nasara, amma kotun kolin Najeriya ta soke wannan hukuncin tare da tabbatar da Oyetola a matsayin zababben gwamnan Osun.

6. Zama gwamna a 2022

A 2022, Adeleke ya fafata a zaben gwamna na ranar 16 ga Yuli a karkashin inuwar jam'iyyar PDP da gwamna mai ci, Gboyega Oyetola, kamar yadda Punch ta rahoto.

Adeleke ya kayar da Gboyega Oyetola da kuri'u 403,371, inda ya samu nasara a kananan hukumomi 17, ciki har da Olorunda, Ede South, Orolu, Osogbo, Odo Otin, Ifelodun, Boluwaduro, Atakumosa, da kuma Ila.

7. Nasarar tazarce a 2026

Zaben gwamnan da aka yi ranar 16 ga Agustan 2026, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Gwamna Adeleke a matsayin wanda ya samu nasara bayan ya samu kuri’u 511,067.

Babban abokin hamayyarsa mafi kusa, dan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu kuri’u 444,815. Adeleke ya samu nasara a kananan hukumomi 19 daga cikin kananan hukumomi 30 da ke jihar Osun.

Wannan zabe dai ya yi matukar daukar hankali musamman saboda gabatowar babban zaben gama gari na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Kananan hukumomin da Gwamna Adeleke da dan takarar APC suka lashe

Adeleke.
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke yana kada kuri'a a rumfar zabensa Hoto: @AAdeleke
Source: Twitter

Gwamna Adeleke ya yabawa Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke , ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan INEC ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2026.

Gwamnan ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kira shi domin taya shi murnar nasarar da ya samu, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar tasirin dimokuraɗiyya Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262