Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamnan Jihar Osun ke Gudana, Accord, APC da ADC Sun Ja Daga
Zabe ya kai dare a rumfar zaben Oyebamiji
Ana amfani da Janareta yayin da ake ci gaba da kada kuri'a a rumfar zaben Oyebamiji.
Lokaci: 6:29 na yamma
Wuri: Open Space, Gantry Sawmill, Ward 09, Ikire I, Irewole LGA
Ana ci gaba da kada kuri’a a rumfar zaben dan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, yayin da lokaci ya ja zuwa yamma.
Yayin da hasken rana ke raguwa, jami’an zabe na shirin amfani da janareta domin samar da haske, ta yadda za a ci gaba da gudanar da kada kuri’a a rumfar.
An fara kidaya kuri'u a zaben Osun
Rahotanni sun nuna cewa an kammala kada kuri'u tare da fara kidaya a wasu rumfuna, yayin waus kuma har yanzu ake ci gaba da zabe a jihar Osun.
A Mazaba ta 08, rumfuar zabe ta 003 da ke gaban fadar Timi of Edeland, karamar hukumar Ede north, malaman zabe sun fara kidaya kuri'un da aka kada.
'Yan sanda na sa ido kan zaben Osun
Babban Jami’in Tsaro da ke kula da zaɓen Gwamnan Jihar Osun, DIG Isyaku Mohammed na gudanar da sa ido ta sama da kuma bibiyar tura jami’an tsaro domin tabbatar da kare lafiyar jama’a da gudanar da zaɓen cikin lumana.
Yayin da al’ummar Osun ke kaɗa ƙuri’a, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta wallafa a Facebook cewa ta kuduri aniyar kare rayuka, tabbatar da tsaron tsarin zaɓe da kuma tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar.
An zargi APC da sayen kuri'u
Masu zaɓe a wata rumfar zaɓe da ke ƙaramar hukumar Ejigbo ta jihar Osun sun zargi wasu da ake kyautata zaton magoya bayan jam’iyyar APC ne da raba kuɗi yayin zaɓen gwamnan jihar.
An dauki lamarin a wani bidiyo, inda aka ga masu zaɓe suna fuskantar wasu mutane da ake zargi da raba kuɗi a wajen rumfar zaɓen.
A cewar masu zaɓen, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na safe. Haka kuma, an samu irin wannan zargi da misalin ƙarfe 10:30 na safe.
Punch ta wallafa cewa daya daga cikin masu zaɓen da ya yi magana a cikin bidiyon ya ce waɗanda ake zargin da raba kuɗin sun gudu daga wajen tare da wasu daga cikin kuɗin da suka saka a cikin leda.
Rigima ta barke a rumfar dan takarar ADC
Dan takarar gwamnan Osun na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya tsallake rijiya da baya bayan tashin hankali ya barke a rumfar zabensa da ke Ejigbo ranar Asabar.
Lamarin ya faru ne a Unit 003, Iroyin Ayo Open Space, Ward 004, jim kadan bayan Salaam da matarsa sun kada kuri’unsu, cewar rahoton Vanguard.
Bayan barkewar rikicin, tsoro ya mamaye rumfar zaben, lamarin da ya tilasta masu kada kuri’a, jami’an INEC, masu sa ido da ‘yan jarida barin wurin domin kare lafiyarsu.
Yayin da lamarin ke kara kamari, jami’an tsaron da ke kula da lafiyar Salaam sun gaggauta fitar da shi daga wurin domin tsira da ransa.
Bayan haka, jami’an zabe sun bar rumfar saboda fargabar abin da ka iya faruwa, lamarin da ya sa aka dakatar da kada kuri’a a wurin.
Daga bisani, jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) sun isa wurin domin kokarin dawo da zaman lafiya.
Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaron sun bar wurin daga baya yayin da har yanzu yanayin ke cike da tashin hankali.
Shin ko kun san cewa?
Dan takarar gwamnan Osun na jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya yi murabus daga mukaminsa na Manajan Darakta na National Inland Waterways Authority (NIWA) a watan Nuwamba 2025, domin ya mayar da hankali kan burinsa na neman kujerar gwamnan jihar.
Bayan murabus dinsa, Oyebamiji ya samu karbuwa a cikin jam’iyyar, inda masu neman takara bakwai suka janye daga neman takarar domin mara masa baya, cewar TheCable.
Hakan ya kai ga bayyana shi a matsayin dan takarar da APC ta amince da shi a matsayin wanda kowa ya yarda da shi.
Kwamitin tantance ‘yan takarar APC ya kuma soke cancantar wasu masu neman tikitin, ciki har da Iyiola Omisore, tsohon sakataren jam’iyyar na kasa.
Shin ko kun san cewa?
Dan takarar gwamnan Osun na jam’iyyar ADC, Najeem Salaam, ya taba zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun daga 2011 zuwa 2018.
A lokacin da Salaam yake matsayin kakakin majalisar, tsohon gwamnan Osun kuma jigo a ADC, Rauf Aregbesola, shi ne gwamnan jihar.
Salaam ya samu tikitin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a watan Disamba 2025, bayan ya tsaya takarar fidda gwani shi kadai. Daga cikin wakilai 528 da suka halarci zaben fidda gwamin, 520 ne suka kada kuri’ar amincewa da shi, lamarin da ya tabbatar da shi a matsayin dan takarar ADC a zaben gwamnan Osun.
Dan takarar ADC na samun goyon bayan Rauf Aregbesola da kuma mambobin kungiyar Omoluabi Progressives, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar Osun.
Salaam na daga cikin manyan ‘yan takarar da ke fafutukar ganin sun lashe zaben gwamnan Osun na 2026.
Jami'an ICPC sun je rumfunan zabe
Jami'an hukumar ICPC na sanya ido a rumfunan zabe yayin zaben gwamnan jihar Osun.
Wuri: Rumfar zabe PU 08, Mazaba 04, Alajue 1, Ede ta Kudu
Sakataren APC na kasa ya yi jawabi
Sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Ajibola Basiru, ya bayyana cewa zaben gwamnan Osun na iya samun yawan masu kada kuri’a.
Basiru ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da zaben a fadin Jihar Osun a yau, Asabar.
Sakataren na APC ya ce abubuwan da ake gani a rumfunan zabe da dama sun nuna cewa akwai yiwuwar zaben ya samu kyakkyawan adadin masu kada kuri’a.
“Yana da alamar zai kasance zaben da za a samu yawan masu kada kuri’a, watakila saboda irin jan hankalin da kamfen din ya yi.” In ji shi
Yan sanda sun cafke baki
Kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da tsaron zaben gwamnan Osun na 2026, Erale Samuel Etaifo, ya ce rundunar tana tsare da kusan mutane 100 da suka fito daga jihohin aOndo da Ekiti, cewar rahoton Channels tv.
Kwamishinan ya bayyana cewa an kama mutanen ne bisa zargin cewa sun shigo Osun domin kawo cikas ga gudanar da zaben.
Ana zargin yan sanda da sace akwatu
Rikici ya barke Mazabar Modakeke ta 10 a Jihar Osun biyo bayan zargin wasu da ake tunanin 'yan sanda ne da kwace kayayyakin zabe gami da tarwatsa masu zabe da ma'aikatan INEC.
Kamar yadda wani shaida da abin ya faru a gabansa ya bayyana, lamarin ya faru ne bayan an fara kaɗa kuri'a a rimfar zaben cikin salama da kwanciyar hankali.
Shaidan ya yi zargin cewa mutanen da ake zargin 'yan sanda ne sun kwashe kayayyakin zaben gabanin su harba abin da aka bayyana a matsayin barkonon tsohuwa, sannan suka fice daga wurin.
”Daukacin wakilan jam'iyyu da masu yi wa kasa hidima sun tsere daga wurin,” in ji shaidan.
Wannan al'amari ya haifar da firgici a yankin da ake gudanar da zaben, inda ma'aikatan zabe da wakilan jam'iyyu suka tsere domin tsira da rayukansu.
Dan takarar APC ya shirya kada kuri'a
Bola Oyebamiji ya shirya kada kuri'arsa a rumfar zabensa yayin zaben gwamnan jihar Osun.
Dan takarar na APC na daga cikin na gaba-gaba a cikin masu neman kujerar gwamna.
Oyetola ya kada kuria
Tsohon Gwamnan Jihar Osun kuma Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Gboyega Oyetola, ya kada kuri’arsa a rumfar zabensa da ke karamar hukumar Boripe.
Oyetola ya shiga cikin masu kada kuri’a yayin da ake gudanar da zaben gwamnan Osun a fadin jihar a yau, Asabar.
Tsohon gwamnan yana mara wa Bola Oyebamiji, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), baya a zaben.
Malaman zabe sun isa mafi yawan rumfuna tun 8:30
Da misalin karfe 8:30 na safe, jami’an INEC sun isa rumfunan zabe 300 da ya kai kashi 78 cikin 100, masu sa ido na shirinmu na bayar da rahoto daga cikinsu.
Wannan na bayar da wani haske na farko kan yadda shirye-shiryen gudanar da zabe ke gudana a rumfunan zaben da ake sa ido a kansu, cewar Yiaga Africa.
Yan daba sun tarwatsa masu zabe a Osun
An samu tsaiko wajen kada kuri’a a rumfar zaben tsohon Gwamnan Osun kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kori masu kada kuri’a tare da dagula tsarin zaben.
Lamarin ya haifar da tashin hankali a rumfar zaben, inda aka ruwaito cewa an tilasta wa masu kada kuri’a barin wurin yayin da yanayin ya rikice.
Hakan ya kawo cikas ga tsarin kada kuri’a tare da haifar da damuwa kan yadda ake gudanar da zaben gwamnan a yankin, cewar The Nation.
Adeleke ya ce zai yi nasara
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana kwarin gwiwar cewa zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a yau, Asabar, zai gudana cikin kwanciyar hankali kuma zai samu nasara.
Adeleke ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya kada kuri’arsa a Sagba Agbogunde Ward 2, Unit 9, da ke Ede North Local Government Area.
Gwamnan ya kammala kada kuri’arsa tare da sauran masu zabe a rumfar, kafin ya yi magana kan yadda yake kallon sakamakon zaben, cewar Vanguard.
Adeleke ya ce yana da kwarin gwiwar cewa zai samu nasara a zaben, yayin da ake ci gaba da kada kuri’a a sassa daban-daban na jihar.
An cafke mutane 300 a gidan dan siyasa
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kama wasu mutane 300 da ba a bayyana dalilin kasancewarsu ba a gidan wani jigon siyasa a Jihar Osun, cewar rahoton TheCable.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Anietie Okokon Iniedu, ya bayyana cewa an kama mutanen ne a gidan wani mai ruwa da tsaki a harkokin siyasa.
Ya ce a halin yanzu ana gudanar da bincike da tantance bayanan wadanda aka kama domin gano dalilin kasancewarsu a wurin.
Gwamna Adeleke ya kaɗa kuri'arsa a Osun
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya kada kuri’arsa a zaben gwamnan jihar da ake gudanarwa a yau.
Adeleke ya isa rumfar zabensa da ke Ede da misalin ƙarfe 8:30 na safe, inda ya shiga cikin sauran masu kada kuri’a domin sauke nauyin da ke kansa na zaɓe, cewar rahoton Channels.
An fara kada kuri'a
An fara kada kuri'a a rumfunan zabe.
Hukumar zabe ta INEC ta sanya hotunan wasu rumfunan zabe da aka fara kada kuria a shafinta na Facebook.
Osun: Jami’an INEC sun karɓi kayayyakin zaɓe
An fara rarraba kayayyakin zaɓe domin gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun na shekarar 2026 a faɗin jihar.
A lokacin da ake tattara wannan rahoto, jami’an zaɓe sun riga sun isa cibiyar rajista da ke Makarantar CAC Grammar School, Araromi, Oshogbo, domin karɓar kayayyakin tare da wucewa da su zuwa rumfunan zaɓe daban-daban, Channels TV ta ruwaito.
An ƙara tsaurara matakan tsaro a ofishin INEC da ke Osun
Yayin da Jihar Osun ke shirin gudanar da zaɓen gwamnan jihar, ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke kan titin Gbongan-Ibadan a Osogbo ya cika da jama’a, yayin da aka ƙara yawan jami’an tsaro a wurin.
A cewar rahoton Channels TV na ranar Juma’a, 14 ga Agusta, an ga jami’an tsaro da dama a harabar ofishin INEC, ciki har da jami’an Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF)
Zaɓen Osun: INEC ta yi bayani kan matsayin PDP
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce duk da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya umarci a saka ɗan takarar PDP cikin zaɓen gwamnan Jihar Osun, jam’iyyar ba za ta gabatar da ɗan takara a zaɓen ba.
Babban Sakataren Yada Labarai kuma Mai Ba Shugaban INEC Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Adedayo Oketola, ya shaida wa jaridar The Nation cewa hukumar ta shigar da ƙara domin dakatar da aiwatar da hukuncin tare da ɗaukaka ƙarar.
Ana zargin an kama shugabannin Accord a Osun
Majalisar Yaƙin neman zaɓen Imole ta yi zargin cewa wasu sojoji da ke cikin manyan motoci sama da 15 sun kai samame gidajen shugabannin jam’iyyar Accord a sassan Jihar Osun da daren Juma’a, 14 ga Agusta, 2026.
Majalisar ta kuma yi zargin cewa zuwa safiyar Asabar, 15 ga Agusta, 2026 wani mai ba Gwamna Ademola Adeleke shawara na musamman da kuma wani babban mai fafutukar neman zaɓen Accord suna tsare a wani sansanin soji da ke Ede.
Legit.ng ta ruwaito cewa a cikin sanarwar da majalisar ta fitar, ta buƙaci Laftanar Janar Waidi Shaibu, da ya gaggauta sa baki kan lamarin, yayin da al’ummar Osun ke shirin fita domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar a yau, Asabar, 15 ga Agusta, 2026.
An fara zuwa rumfunan zabe
Masu kada kuri'a sun fara sanya layi a rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben gwamnan jihar Osun.
Jaridar TheCable ta rahoto cewa mutane da dama sun yi layuka a rumfunan zabe daban-daban domin jiran a fara kada kuri'a.
Alkaluman INEC
Kananan hukumomi - 30 LGAs
Mazabu - 332
Rumfunan zabe - 3,763
Masu kada kuri'a da suka yi rajista - 2,339,233
Katin PVC da aka karba - 1,906,390 (81.50%)
Katin PVC da ba a karba ba - 432,843 (18.50%)
INEC ta fara raba kayan zabe
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara jigilar kayayyakin zabe masu muhimmanci zuwa daukacin kananan hukumomi 30 na Jihar Osun tun a ranar Alhamis.
An samu tsaiko wajen rarraba kayayyakin ne biyo bayan umarnin kotu da ya haifar da sake buga takardun zabe domin shigar da dan takarar jam'iyyar SDP.
Mutum miliyan 1.9 sun karbi katin zabe
INEC ta bayyana cewa sama da katunan zaɓe (PVCs) miliyan 1.9 aka karɓa domin zaɓen gwamnan jihar Osun da zai gudana yau Asabar.
Hukumar zaben mai zaman kanta ta dauki alkawarin gudanar da zabe mai inganci, sahihi kuma cikin kwanciyar hankali.