Labari da ɗumi-ɗumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC

Labari da ɗumi-ɗumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC

- Daga karshe Sanata Iyiola Omisore ya sauya jam'iyya da aka dade ana hasashen zai yi

- Tsohon gwamnan na jihar Osun ya koma jam'iyyar APC mai mulki a ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu

- Tsohon jigon na SDP, Omisore ya karbi katinsa na jam'iyyar APC a mazabarsa a Ile-Ife, jihar Osun

Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

DUBA WANNAN: Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'

Labari da dumi-dumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC
Labari da dumi-dumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC. Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Amma daga bisani ya hada gwiwa da jam'iyyar APC kafin zaben raba gardama ta ranar 28 ga watan Satumba bayan ya juya wa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) baya.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya kore mu daga yankin kudu maso yamma, in ji Miyetti Allah

Daga bisani jam'iyyar APC ce ta lashe zaben wadda hakan ya kara bayyana darajar Omisore a siyasar jihar ta kudu maso yamma.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel