Netanyahu Ya Gana da Shugaban UAE a Sirrance, Sun Yi Maganar Iran
- Wata majiya ta Isra’ila ta ce Benjamin Netanyahu ya ziyarci UAE a sirrance ranar Lahadi, inda ya gana da Shugaba Sheikh Mohammed bin Zayed
- A cewar majiyar, batun Iran ne ya fi mamaye tattaunawar, yayin da Isra’ila da UAE ke ƙara haɗin gwiwa kan tsaro
- Rahoton ziyarar ya zo ne yayin da ake muhawara a Isra’ila kan zargin cewa UAE da Masar sun yi gargadi kafin harin Hamas na 7 ga Oktoba 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ziyarci Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a sirrance ranar Lahadi, 27 ga watan Satumban 2026.
Benjamin Netanyahu ya gana da Shugaban ƙasar, Sheikh Mohammed bin Zayed, a cewar wata majiya ta Isra’ila da ta san da ziyarar.

Source: Getty Images
Tashar CNN ta kawo rahoto a ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026 cewa wata majiya ce ta sanar mata da hakan.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan tsaron Isra'ila ya dura masallaci na 3 mafi daraja a wurin musulmai
Majiyar ta bayyana cewa batun Iran ne ya fi mamaye ajandar ganawar, a wani fanni da Isra’ila da UAE suka ƙara haɗin gwiwa, ciki har da yayin yaƙin Iran da ake ci gaba da yi.
Ba a tabbatar da ziyarar a hukumance ba
Ofishin Netanyahu bai tabbatar da ziyarar ba, yayin da tashar ta tuntubi Ma’aikatar Harkokin Wajen UAE domin jin ta bakinta.
Idan aka tabbatar da ziyarar, za ta kasance wata ziyara da ba kasafai ake gani ba, kuma ta zo ne daidai wata guda kafin zaɓen Isra’ila na ranar 27 ga Oktoban 2026.
Zargin gargadin harin 7 ga Oktoba
Ziyarar ta kuma zo ne a lokacin da ake ƙara samun ce-ce-ku-ce a siyasar Isra’ila kan rahotannin jaridar Haaretz da The New York Times.
Rahotannin sun yi zargin cewa Sheikh Mohammed bin Zayed ya gargadi Netanyahu game da yiwuwar wani babban hari daga Hamas kwanaki kaɗan kafin harin 7 ga Oktoba, 2023.
Jaridar The Atlantic ita ma ta ruwaito cewa shugaban hukumar leƙen asirin Masar, Abbas Kamel, ya je Isra’ila ranar 26 ga Satumba, 2023, inda ya yi gargadin cewa Gaza na dab da “fashewa”.
A ranar Lahadi kuma, The Wall Street Journal ta ruwaito cewa Masar ta isar wa Isra’ila da aƙalla gargaɗi uku game da Gaza, inda na ƙarshe ya kasance ta hanyar wata tattaunawar waya da Netanyahu kwanaki kaɗan kafin harin.
Ofishin Netanyahu ya musanta samun gargadi
Ofishin Netanyahu ya sha musanta cewa ya samu wani gargadi kafin harin. Ofishin ya kuma yi watsi da rahotannin, yana bayyana su a matsayin ƙagaggun labarai da aka ƙirƙira domin cutar da Netanyahu a fagen siyasa.
Sai dai abokan hamayyarsa sun yi amfani da waɗannan zarge-zarge wajen mayar da batun ɗaukar alhakin gazawar da ta faru kafin harin 7 ga Oktoba, 2023, cikin manyan batutuwan yaƙin neman zaɓe.
UAE ba ta musanta tattaunawar ba
Bayan rahotannin farko da suka ce Bin Zayed ya yi gargadi, Ma’aikatar Harkokin Wajen UAE ta ce a farkon wannan watan ba ta yin tsokaci kan rahotannin kafafen yaɗa labarai ko hasashe game da tattaunawar shugabannin gwamnatoci. Sai dai ba ta musanta cewa an yi kiran ba.
Ma’aikatar ta ce duk wani bayanin leƙen asiri da ya dace “ana isar da shi kuma ana ci gaba da isar da shi tsakanin hukumomin da abin ya shafa” idan hakan ya zama dole.

Source: Twitter
Ministan Netanyahu ya shiga Al-Aqsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaron cikin gida na Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, ya fitar da wani bidiyo da ke nuna shi yana shiga harabar Masallacin Al-Aqsa.
Bidiyon ya nuna dan siyasar masu tsattsauran ra’ayi karkashin kariyar ‘yan sandan Isra’ila yayin bikin Sukkot na Yahudawa.
Asali: Legit.ng

