Zaben Osun: INEC Ta Sanar da Dan Takarar da Ya Lashe Zaben Gwamna
- INEC ta ayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben Osun 2026 bayan samun kuri’u 511,067
- Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC ya samu kuri’u 444,815, yayin da Adeleke ya doke shi da tazarar kuri’u 66,252.
- Jimillar masu rajista ta kai 2,339,544, yayin da 1,010,684 aka tantance, kuma kuri’u 985,079 ne aka tabbatar da ingancinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Osogbo, Jihar Osun — Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana dan takarar da ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Hukumar INEC ta sanar da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na shekarar 2026.

Source: Twitter
Jami'in tattara sakamakon zaben kuma shugaban jami'ar gwamnatin tarayya ta Oye Ekiti, Farfesa Joshua Ogunwole, ya sanar da sakamakon zaben da misalin karfe 7:24 na safiyar ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton The Punch.
Adeleke, wanda ya tsaya takara karkashin Accord Party, ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na APC, wanda ya samu kuri’u 444,815.
Dan takarar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.
Adeleke ya lashe zabe da tazarar kuri’u 66,252
Sakamakon karshe da INEC ta sanar ya nuna cewa Adeleke ya doke Oyebamiji da tazarar kuri’u 66,252.
Sanarwar ta biyo bayan kammala tattara sakamakon zaben daga kananan hukumomi 30 na Jihar Osun.
Nasarar ta bai wa Adeleke damar samun karin wa’adin mulki bayan fafatawar da ta gudana tsakaninsa da dan takarar APC.
Adadin masu zabe da kuri’un da aka kada
Jimillar masu kada kuri’a da aka yi wa rajista domin zaben ta kai 2,339,544. Daga cikin wannan adadi, 1,010,684 ne aka tantance domin kada kuri’a, yayin da adadin kuri’un da aka kada ya kai 1,005,800.
INEC ta bayyana cewa 985,079 daga cikin kuri’un sun kasance ingantattu, yayin da aka samu 20,721 da aka yi watsi da su.
Sakamakon karshe ya kuma tabbatar da yanayin da aka fara gani yayin da ake tattara sakamakon kananan hukumomi, inda Adeleke ya ci gaba da samun rinjaye kan abokin hamayyarsa na APC.

Source: Twitter
Adeleke ya samu karin wa’adin mulki
Da wannan nasara, Adeleke ya samu damar ci gaba da jagorantar Jihar Osun na wani wa’adin mulki. Nasarar ta zo ne bayan fafatawa mai zafi tsakanin jam’iyyar Accord Party mai mulkin jihar da APC, wadda ta yi kokarin kwace ikon jihar daga hannun Adeleke.
INEC ta kammala tattara sakamakon daga dukkan kananan hukumomin jihar kafin bayyana Adeleke a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Osun na 2026.
Adeleke ya lashe kananan hukumomi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party ya lashe kananan hukumomi m19 cikin 30 a zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar.
Sakamakon da aka tattara daga cibiyoyin tattara sakamako na kananan hukumomin ya nuna cewa Adeleke ya samu jimillar kuri’u 511,067.
Asali: Legit.ng

