Ana Batun Takarar Pantami, Sanata Goje Ya Dauki Matakin da Zai Kawo Cikas ga APC a Gombe
- Sanata Muhammad Danjuma Goje ya ce magoya bayansa su guji zaɓar wasu ’yan takarar Majalisar Wakilai da na Majalisar Dattawa a zaɓen 2027
- Goje ya ce hana shi tikitin komawa Majalisar Dattawa cin amana ne daga wasu masu ƙarfi a jam’iyyarsa da ba sa son ci gaban al’ummar Gombe
- Sanatan ya ce ba zai gaya wa magoya bayansa wanda za su zaɓa ba, amma zai ci gaba da ba su umarni kan waɗanda bai kamata su zaɓa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanatan Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya aika sako ga magoya bayansa kan zaben 2027.
Sanata Goje ya umurci magoya bayansa da kada su zaɓi mutanen da suka yi aiki wajen hana shi samun tikitin komawa Majalisar Dattawa.

Source: Twitter
Goje ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a gidansa da ke Gombe ranar Lahadi, 27 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Goje ya ambaci ’yan takarar Majalisar Wakilai
Sanatan ya gaya wa magoya bayansa kada su zaɓi ’yan takarar Majalisar Wakilai daga mazabun tarayya na Akko da Yamaltu/Deba, da kuma ɗan takarar kujerar Majalisar Dattawa ta Gombe ta Tsakiya na jam’iyyarsa.
Ko da yake Goje bai ambaci sunan jam’iyyar ba, masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce yana magana ne kan ’yan takarar All Progressives Congress (APC) a babban zaɓen da ke tafe.
Ɗan takarar APC na kujerar Majalisar Dattawa ta Gombe ta Tsakiya shi ne DCP Mohammed Ahmed (mai ritaya).
’Yan takarar Majalisar Wakilai kuwa su ne Hon. Usman Bello Kumo, mai neman wakiltar mazabar Akko, da Hon. Inuwa Garba, mai neman wakiltar Yamaltu/Deba.
Goje ya ce an ci amanarsa
A cewar Goje, shawarar hana shi tikitin komawa Majalisar Dattawa cin amana ce daga wasu ɓangarori a cikin jam’iyyar da ya ce ba sa yi wa al’ummar Akko, Gombe ta Tsakiya da jihar baki ɗaya fatan alheri.
Goje ya ce magoya bayansa suna da ’yancin zaɓar ɗan takarar kowace jam’iyya, amma ban da mutanen da ya ambata.
Ya ce ya kamata aminci ya kasance ga al’umma, ba ga mutanen da suke aiki a kan muradun waɗanda suke wakilta ba.
“Ba zan gaya muku wanda za ku zaɓa ba”
Goje ya ce ba zai gaya wa magoya bayansa wanda za su zaɓa a babban zaɓen 2027 ba, amma zai gaya musu waɗanda bai kamata su zaɓa ba.
“Ba zan gaya muku wanda za ku zaɓa a babban zaɓen 2027 ba. Amma zan gaya muku waɗanda bai kamata ku zaɓa ba. Kada ku zaɓi duk wanda ya hana ni tikitin komawa Majalisar Dattawa, ko na kujerar Majalisar Dattawa ko na Majalisar Wakilai ta Akko da Yamaltu/Deba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa magoya bayansa za su iya zaɓar duk ɗan takarar da suke so, matuƙar ba daga cikin waɗanda ya ce sun yi aiki wajen hana shi komawa Majalisar Dattawa ba.
Ya kuma roƙe su da su jira ƙarin umarninsa kan ’yan takarar kujerar gwamna da na Majalisar Dokokin Jihar Gombe da bai kamata su zaɓa ba.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin shugabannin APC na jihar da kuma ’yan takarar uku na jam’iyyar da Goje ya ambata, amma ba a samu amsa ba har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoton.

Source: Facebook
Sanata Goje ya musanta barin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Danjuma Goje, ya musanta cewa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.
Sanata Danjuma Goje ya ce yana tuntubar masu ruwa da tsaki na siyasa, kuma zai bayyana matakin da zai dauka a lokacin da ya dace.
Asali: Legit.ng


