Abin da Kwankwaso da Peter Obi ba Za Su Yi ba don Zaben 2027

Abin da Kwankwaso da Peter Obi ba Za Su Yi ba don Zaben 2027

  • Peter Obi ya ce takararsa ba za ta bai wa wakilan jam’iyya kuɗi domin jan hankalin masu zaɓe ko sayen ƙuri’u a zaɓen 2027 ba
  • Tsohon Gwamnan Anambra ya ce za su tabbatar da cewa masu zaɓe sun samu kariya kuma ƙuri’unsu sun yi amfani
  • Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin Obi da Kwankwaso za ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar talakawan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya yi magana kan zaben shekarar 2027.

Peter Obi ya ce takararsa ba za ta shiga harkar sayen ƙuri’u gabanin babban zaɓen 2027 ba da ke tafe.

Peter Obi ya ce ba za su sayi kuri'a ba
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Obi ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da jama’a da aka gudanar a Sokoto ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026 tare da abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Obi ya dauko irin salon Atiku, ya ce zai maido tallafin man fetur

Obi ya ce ba za a bai wa wakilan jam’iyya kuɗi ba

Tsohon Gwamnan Anambra ya ce ba za a ware kuɗi domin bai wa wakilan jam’iyya su rinƙa jan hankalin masu zaɓe ko sayen ƙuri’u ba.

Ya danganta yawaitar amfani da kuɗi a zaɓe da matsalar talauci da yake ƙara ta’azzara a ƙasar.

“Ba mu shirya ba mu bai wa wakilan jam’iyya kuɗi domin su rinƙa jan hankalin masu zaɓe ba. Wannan sayen ƙuri’a ne, kuma yana daga cikin dalilan da suka sa talauci ke ci gaba da ƙaruwa a ƙasar,” in ji Obi.

Obi ya yi alkawarin kare ƙuri’un masu zaɓe

Obi ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta tabbatar da kare masu zaɓe tare da tabbatar da cewa ƙuri’unsu sun yi amfani, The Punch ta kawo labarin.

Dan takarar shugaban kazar ya kuma ce za a ɗauki matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin tsarin gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ita ce hanya 1 tilo"; Na kusa da Atiku ya samo mafita ga 'yan adawa kan Tinubu . 2027

Ya yi magana kan tallafin man fetur

Obi ya ce yaƙi da cin hanci da rashawa da ke da alaƙa da tsarin tallafin man fetur zai kasance kafin duk wani sabon tsari na rage wa ’yan Najeriya nauyin farashin man fetur.

“Za mu kawar da cin hanci da rashawa, musamman wanda ya shafi tallafin man fetur, kafin mu nemo hanyar dawo da tallafin ta wata siga,” in ji shi.

Tambuwal ya soki tikitin Musulmi da Musulmi

A nasa jawabin, jagoran ƙungiyar Obi/Kwankwaso a Sokoto, Nasiru Tambuwal, ya soki tsarin tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Tambuwal ya ce tun daga shekarar 1999, al’adar siyasar ƙasar ta kasance ana samun daidaito tsakanin Musulmi da Kirista a tikitin shugaban ƙasa, kafin APC ta sauya wannan tsarin.

Kwankwaso ya ce za su yi aiki domin talakawa

A nasa ɓangaren, Rabiu Kwankwaso ya ce tikitin Obi da shi ya mayar da hankali ne kan jin daɗin talakawan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ina da tabbaci": Jigo a APC ya fadi yankin da Tinubu zai kwashe kuri'u a 2027

“Gwamnatin Obi/Kwankwaso a shirye take ta yi aiki domin talakawan wannan ƙasa,” in ji Kwankwaso.
Obi da Kwankwaso sun je Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Okonkwo ya gargadi Obi da 'yan adawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya yi gargadi ga 'yan adawa kan zaben 2027.

Kenneth Okonkwo ya yi gargaɗin cewa rashin haɗin kan ‘yan adawa a bayan ɗan takara guda na iya ƙara wa Shugaba Bola Tinubu ƙarfi a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng