‘Zan Iya Yanke Hannu Na saboda ba Tinubu Kuri’u Miliyan 2.5’: Wani Shugaban APC
- Shugaban APC na Edo, Jarrett Tenebe, ya ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa domin samun kuri’u miliyan 2.5 ga Tinubu a 2027
- Ya ce shugabannin APC na jihohi ba su taɓa yin taro tare domin amincewa ko yin watsi da ƙawancen jam’iyyun adawa ba
- Tenebe ya ce ba batun nasarar Tinubu kaɗai ne a 2027 ba, adadin kuri’un da zai samu a jihohi ne abin da ya fi muhimmanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin City, Edo - Shugaban jam’iyyar APC a Edo, Jarrett Tenebe, ya yi alkawarin samar da miliyoyin kuri'u ga Bola Tinubu.
Ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin taimakawa wajen samun kuri’u miliyan 2.5 ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Tenebe ya bayyana hakan ne yayin wata hira da TVC News, inda ya kuma yi bayani kan matsayin shugabannin APC na jihohi game da shawarar ƙulla ƙawance tsakanin jam’iyyun adawa da jam’iyya mai mulki.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba
Ya ce babu wani taro da shugabannin APC na jihohi suka gudanar tare da amincewa ko yin watsi da ƙawancen da ake shirin kullawa.
A cewarsa, shugabannin APC na jihohi ba sa yanke shawarar matsayar jam’iyyar kan manyan batutuwan siyasa da kansu, yana mai cewa gwamnoni su ne shugabannin jam’iyyar a jihohinsu.
Tenebe ya kuma yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa taron APC na baya-bayan nan da aka gudanar a Maiduguri taron shugabannin jam’iyyu na jihohi ne domin yin watsi da ƙawancen.
Ya ce:
“Shiri ne na Kwamitin Ayyuka na Ƙasa, ba shirin jiha ba ne. An gayyace mu ne kawai a matsayin shugabannin jam’iyyu na jihohi da mambobin NEC zuwa taron, kuma abin da muka yi ke nan.”
Ya ce shugabannin APC za su jira matakin da hukumomin jam’iyyar da suka dace za su ɗauka kafin su yi wani abu kan batun ƙawancen.
Sai dai, da yake magana musamman kan Edo, shugaban APC ɗin ya ce jam’iyyar ta kuduri aniyar samar da kuri’u miliyan 2.5 ga Tinubu, kuma za ta duba duk wata yarjejeniya ta siyasa da za ta taimaka wajen cimma wannan buri.
“Abin da muke yi shi ne jira mu ga sakamakon, sannan duk abin da sakamakon ya kasance, za mu bi shi, a jiharmu, mun yi alkawarin cewa za mu bai wa Mai Girma Shugaban ƙasa kuri’u miliyan 2.5."
Tenebe ya ƙara da cewa jam’iyyar a shirye take ta bi duk wata hanya da za ta yiwu a jihar domin taimaka mata wajen cimma wannan buri.
Da yake jaddada ƙudurinsa, Tenebe ya yi amfani da wani misali mai ƙarfi wajen bayyana irin nisan da yake shirye ya je domin cimma burin.
“Duk abin da ɗan Adam zai iya yi, a shirye muke mu yi shi domin tabbatar da cewa mun samu waɗannan kuri’un ga Shugaban ƙasa.”
“Ko da hannuna ne zai zama cikas wajen samun kuri’u miliyan 2.5 da muka yi wa Shugaban ƙasa alkawari, zan yanke hannun; ko da kaina ne, zan yanke shi domin tabbatar da cewa mun samu kuri’un."
- In ji shi.
2027: Abba Kabir ya shawarci yan Arewa
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana goyon bayansa ga ci gaba da tsarin sauya kujerar Shugaban Ƙasa tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya.
Gwamnan ya ce ya kamata kowane ɓangare ya samu damar riƙe mulkin ƙasa na wa’adin shekara takwas kafin a miƙa shi ga ɗayan ɓangaren.
Ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen ci gaba maimakon hare-haren siyasa da kalaman da za su iya kawo rikici.
Asali: Legit.ng

