Mutane 3 daga Gidan Adeleke da Suka Shiga Siyasa kuma Suka Shahara a Tarihi
- Akwai yan siyasa na yankan-shakku da zuri'ar Adeleke ta haifar a tarihin Osun da kudancin Najeriya
- Mahaifin gwamna mai-ci da yayansa duk sun yi siyasa kafin ya bi tafarkinsu shekaru fiye da 20 da suka wuce
- Raji Ayoola Adeleke sanata ne a jamhuriyya ta 2 wanda ‘ya ‘yansa har biyu suka zama gwamnoni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Osun - A karshen makon jiya aka kammala zaben gwamnan jihar Osun kuma aka tabbatar da nasarar Ademola Adeleke.
Biyo bayan abin da ya faru musamman bayan rawar da mawaki David Adeleke ya taka a zaben, an fara zancen wannan gida.

Source: UGC
Ƴan siyasa daga zuri'ar Adeleke
Kafin gwamnan jihar Osun ya shiga siyasa har ya yi suna, akwai magabatansa daga zuri’arsu ta Adeleke da suka fara sa kafafunsu.
Abin da rahoton nan ya yi shi ne kawo takaitaccen tarihin fitattun mutane daga zuri’ar Adeleke da suka yi siyasa kuma suka rike mukamai.
1. Raji Ayoola Adeleke
A karshen shekarar 1923 aka haifi Raji Ayoola Adeleke wanda shi ne ya bude wannan zuri’a shiga siyasa a jamhuriyya ta biyu a 1979.
Kafin ya shiga tafiyar Obafemi Awolowo a jam’iyyar UPN, an san shi a matsayin malamin asibiti kuma jagora a kungiyar kwadago.
Ayoola Adeleke ya zama sanata a tsohuwar jihar Oyo, ya wakilci mazabun Ede, Osogbo, Irepodun, Ifelodun, Odo Otin, da Ila Orangun.
Shi ne mahaifin Sanata Isiaka Adetunji Adeleke da gwamna Ademola Adeleke da kuma mahaifin mawaki Davido, Adedeji Adeleke.
2. Isiaka Adetunji Adeleke
Isiaka Adetunji Adeleke babban ‘dan siyasa ne a rayuwarsa, shi ne gwamnan farko da aka yi a Osun bayan ta zama jiha da aka yi zabe a 1992.
Amma bai dade a ofis ba Janar Sani Abacha ya hambarar da gwamnatin farar hula a shekarar 1993. Bayan nan ya rike mukamai dabam-dabam.
Kamar mahaifinsa da aka ambata a baya, shi ma Isiaka ya yi sanata har sau biyu yana wakiltar yammacin Osun a Majalisar dattawa.
Da yake kaddara ta riga fata, a 2017 TVC ta ce ciwo ya kashe shi a wani asibiti a Osogbo lokacin an ce yana burin sake neman takarar gwamna.

Source: Twitter
3. Ademola Nurudeen Jackson Adeleke
‘Dan autan wannan gida da yake cikin siyasa a yau shi ne Ademola Nurudeen Jackson Adeleke wanda ya shiga harkar tun 2001.
Gwamna Ademola Adeleke ya sa kafa sosai a siyasa ne da yayansa ya rasu a majalisa, sai aka tura shi ya maye gurbin sanatan.
A 2018 ya zama ‘dan takaran gwamna a PDP amma bai samu nasara ba. Da aka tashi zaben gwamna a 2022, ya doke APC mai-ci.
‘Dan siyasar ya nemi tazarce a zaben da aka yi a 2026 a inuwar jam’iyyar adawa ta Accord, ya yi galaba a kan Bola Oyebamiji.
'Yan takaran da aka ba nasara a zaben Osun
Rahoton mu a nan ya fito da manyan 'yan takara uku da ake hasashen fafatawa za ta yi zafi a tsakaninsu a zaben gwamnan jihar Osun.
'Yan takaran sun hada da Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord, Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC, da kuma Najeem Salaam na jam'iyyar ADC.
Ana da masaniya mutane za su iya ziyartar dandalin Hukumar Zabe ta INEC don samun ingantattun bayani kan tsarin gudanar da zabe.
Asali: Legit.ng


