Gwamna Adeleke Ya Yi Magana kan Nasararsa, Ya Aika Sako ga Tinubu
- Gwamnan jiharOsun, Ademola Adeleke, ya aika ds sako ga Shugaba Bola Tinubu bayan sake zabensa a karo na biyu
- Hukumar INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun na 15 ga Agustan 2026
- Gwamna Ademola Adeleke ya ce sake zabensa a karo na biyu nasara ce ga dimokuraɗiyya da al’ummar jihar Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bayan sake zabensa a matsayin gwamnan jihar a zaben da aka gudanar ranar 15 ga Agusta.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar ranar Lahadi, 16 ga watan Agustan 2026.

Source: Twitter
Da yake magana da manema labarai bayan sanar da sakamakon, gwamnan ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kira shi domin taya shi murnar nasarar da ya samu, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Me Adeleke ya gayawa Shugaba Tinubu?
Adeleke, wanda ya bayyana sake zabensa a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da al’ummar Osun, ya yabawa shugaban kasar bisa tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da tasiri a Najeriya, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Na so na yi amfani da wannan dama wajen gode wa Mai Girma Shugaban Kasa. Shugaban Kasa ya kira ni kuma ya taya ni murna." "Na gode, Mai Girma Shugaban Kasa, da ka tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da wanzuwa, saboda ka yi fafutuka dominta,” in ji shi.
Tinubu ya taya Adeleke murna
Tun da farko, wani jigo a jam’iyyar Accord, Pelumi Olajengbesi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kira Adeleke domin taya shi murna tun kafin a sanar da sakamakon zaben.
Olajengbesi, yayin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan INEC ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan, ya ce shugaban kasar ya taya gwamnan murna a daren ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026.
“Bari na fada muku wannan cikin sauri: tun kafin a sanar da sakamakon a daren jiya, Mai Girma Shugaban Kasa ya kira gwamnan ya taya shi murna, kuma wannan shugabanci ne na kwarai,” in ji shi.
Gwamna Ademola Adeleke ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da sama da kuri’u 60,000..

Source: Twitter
An zargi INEC kan zaben gwamnan Osun
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin yakin neman zaben Gwamna Ademola Adeleke ya zargi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da shirya ayyana zaɓen gwamnan jihar Osun a matssyin wanda bai kammalu ba.
Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na kwamitin, Bamidele Salam,, ya yi kira ga masu sanya ido kan zaɓen da su kasance cikin shiri a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kwamitin ya ce ya samu bayanan wani shiri da yake zargi INEC da yi na ayyana zaɓen a matsayin wanda ba a kammala ba.
Asali: Legit.ng

