‘Ba a Taba Azzalumi irin Sa ba’, Sanatan Kaduna Ya Lissafo Mutanen da El Rufai Ya Kama
- Shehu Sani ya yi kaca-kaca da tsohuwar gwamnatin da ta wuce, ya ce an zalunci mutane kuma an yi sata a Kaduna
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya zargi Nasir El-Rufai da zalunci da tauye hakkin jama’a a sa'ilin da yake ofis
- Kwamred ya tabo zancen shari’ar Malam El-Rufai da ICPC da kuma zargin cewa 'dan siyasar yana kishin Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Kwamred Shehu Sani ya yi magana game da halin da Nasir El-Rufai ya samu kan shi bayan barin mulki a jihar Kaduna.
Shehu Sani wanda bai tare da Malam Nasir El-Rufai tun ba yanzu ba, ya ce wasu abubuwan da tsohon gwamnan ya shuka ne yake girba.

Source: Facebook
Shehu Sani ya jero zunuban Nasir El-Rufai
A wani bidiyo da aka gani a shafin ACG Multimedia Services a Facebook, Shehu Sani ya kira Nasir El-Rufai da bakaken kalmomi.
Sanata Shehu Sani ya ce su haifaffun Kaduna, sun san ba a taba yin mugun azzalumi maras bin doka da hakkin ‘dan adam irin El-Rufai ba.
‘Dan siyasar ya ce yana da tarin misalai da za su iya zama hujjojinsa, amma ya jero kadan cikin zaluncin da ya ce tsohon gwamnan ya yi.
Mutanen da ake zargin gwamnatin El-Rufai ta kama
Ya fara da malaman Musulunci da suka yi addu’a, suna tsine wa masu hannu koran malaman makaranta ba tare da an biya su hakkinsu ba.
Shehu Sani ya ce an kama wadannan malaman addini a Zariya, aka kai su kotu, a karshe sai da aka daure su a wani kurkuku kafin shi ya fito da su.
Akwai shugabannin kiristoci, fastoci da sarakuna a Kajuru da ya ce an daure a gidan yari na watanni takwas saboda sun koka da harin ‘yan bindiga.
Kwamred ya ce gwamnatin El-Rufai ta taba cafke wani ‘dan jarida ya shekara guda a kurkuku saboda ya ce ana biyan ‘yan ta’adda kudi.
Tsohon ‘dan siyasar ya kawo misalin John Danfulai, malamin jami’a da aka daure a sanadiyyar rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook.
Sheikh Bello Yabo yana cikin wadanda Shehu Sani ya ce El-Rufai ya sa an daure a lokacinsa.
Cikin jerin da aka kawo akwai ma’aikatan jaridan gidan rediyon Najeriya na Kaduna, wani ajaridar Authentic City da ‘dan jaridar Leadership.
Tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya ya ce a ‘yan shi’a kuwa akwai wadanda sun shafe sama da shekaru hudu a gidan gyaran hali.
Rigingimun El-Rufai da Shehu Sani a kotu
Saboda sukar gwamnatinsa kuwa, Shehu Sani ya ce El-Rufai ya kai shi kotu biyar har da yi masa sharrin kashe mutumin da bai taba gani ba.
Ya kara da cewa akwai alkaliyar da aka kora daga aiki saboda ta ba su gaskiya a wata shari’a da aka yi tsakanin yaransa da gwamnatin Kaduna.
A fagen mulki, kwamred ya ce El-Rufai ya yi mulki ba tare da tausayi ko jin maganar kowa ba kuma bai daukar suka ko adawa a jihar Kaduna.
Kwamred ya ce:
"Yau dinnan, abin da ya shuka, shi ne yake girbewa."

Source: Facebook
Saboda 2027 aka tsare Malam El-Rufai?

Kara karanta wannan
Baban Chinedu ya yabi nagartar Pantami amma ya fadi wurin da za a nakasa shi a siyasa
Kwamred Shehu Sani ya yi watsi da maganar da ake yi cewa an rufe tsohon gwamnan ne saboda idan ya fito Bola Tinubu zai fadi zabe.
Ya tuna wa duniya cewa El-Rufai yana gwamna ne Atiku Abubakar ya doke APC a Kaduna a 2023.
Wani zargi da ya jefi tsohuwar gwamnatin da ita, ita ce satar dukiyar talakawa, rusa gidajen mutane, talauta jama’a da tsine wa 'yan siyasa.
Sannan ya ce babu wani aikin da Malam El-Rufai ya yi wa yankin Arewa, ya ce asali ma da shi aka yi nasarar ganin Tinubu ya dare kan mulki.
Ya kara da cewa saboda tsohon gwamna ya rasa abin da ya nema a gwamnatin Tinubu ne sai ya koma suka hade da su Atiku Abubakar.
Shehu Sani:
“An kafa gwamnati da shi, an ce ba za a yi da shi ba. Sai ya dauki fushi yana jawo ‘yan Arewa saboda su taya shi fada.
“Yau da a ce Nasiru ya zama minista ko an jawo shi fadar shugaban kasa, babu wanda zai rika duddurawa zagi da ya wuce ‘yan Arewa…”
Abin da El-Rufai yake gani a yau da sauki in ji Shehu Sani, domin a kan kai masa kwai, nama da burodi duk da hukumar ICPC ta tsare shi.
A karshe ya ce babu siyasa a kama jigon na ADC, yake cewa akwai hujjojin satar kudin Kaduna kuma babu abin da za a iya a kan shari’ar.
Nasir El-Rufai ya gamu da sukar Shehu Sani
Kwanaki rahoto ya zo cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.
Hakan ya biyo bayan kalaman sukar da El-Rufai ya yi wa jam'iyyarsa ta APC a cikin 'yan kwanakin nan, a lokacin tsohon gwamnan bai sauya-sheka ba.
Shehu Sani ya bayyana cewa El-Rufai yana sukar jam'iyyar APC ne kawai saboda takaici da kuma jin zafin rashin samun muƙami a gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng


