Shehu Sani
A labarin nan, za a ji Sanata Shehu Sani a bayyana cewa duk da akwai damuwar shigowar sojojin Amurka ƙasar, a maganar gaskiya ana buƙatar taimako kan yan ta'adda.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita. Ya ce kasashen waje ba za su iya magance matsalar ba.
Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi martani kan tallafin kayan aikn sojoji da Amurka ta ba Najeriya. Ya ce ya kamata sauran kasashe su taimaka.
Kasar Amurka ta kawo hare-hare ta sama kan 'yan ta'adda a Najeriya. An kai hare-haren ne a Sokoto. Atiku Abubakar na daga cikin manyan da suka yi martani kan harin.
Shehu Sani ya ce karbar taimako wajen kawo farmaki da izinin Najeriya da Amurka ta yi ba tauye hakkin kasa ba ne. Ya ce za a iya neman agajin Rasha da China.
Sanata Shehu Sani ya yi magana kan takunkumin shugaban Amurka, Donald Trump game da hana 'yan Najeriya da wasu 'yan kasashen Afrika shiga Amurka.
Shehu Sani ya gargadi ƴan Najeriya da sauran ƴan Afirka da aka soke musu biza a Amurka da su koma gida kafin a kama su, yayin da gwamnatin Trump ta soke biza 80,000.
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi martani mai kaushi kan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, saboda barazanarsa ga Najeriya.
Tsohon Sanatan kaduna ta Tsakiya a Najeriya, Shehu Sani ya ce neman ƙirƙirar sababbin jihohi shekara daya kafin zaben 2027 ba shi da amfani kuma bata lokaci ne.
Shehu Sani
Samu kari