Baban Chinedu Ya Yabi Nagartar Pantami amma ya Fadi Wurin Za a Nakasa Shi a Siyasa

Baban Chinedu Ya Yabi Nagartar Pantami amma ya Fadi Wurin Za a Nakasa Shi a Siyasa

  • Yusuf Haruna ya tofa albarkacin bakinsa game da shigar malaman addini cikin harkokin siyasa a Najeriya
  • Baban Chinedu kamar yadda aka fi sanin sa ya yi wa Sheikh Sani Jingir uzurin maganganun da yake yawan yi
  • Tsohon ‘dan wasan kwaikwayon ya ce ana yawan kuka da Isa Ali Pantami wajen rashin iya mu’amala da mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Katsina - Yusuf Haruna wanda kowa ya fi sani da Baban Chinedu ya tabo zancen Isa Ali Ibrahim Pantami da yake neman takara.

Malamin addinin ya fahimci abin da ya sa Sheikh Sani Jingir yake zakewa wajen tallata Bola Tinubu.

Prof. Isa Ali Pantami/Baban Chinedu
Malamin addini kuma 'dan siyasa, Isa Pantami yana magana a taro Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Tsokaci game da shigar malamai cikin siyasa

Tashar DCL Hausa ta yi hira da Yusuf Haruna a shirin siyasar zamani a matsayinsa na mai da’awar yada addinin Musulunci a Najeriya.

A fashin bakin da ya yi game da shigar malamai siyasa, ya yi tsokacin da ya ce ya yi ne tsakani da Allah SWT saboda an tambaye shi.

Kara karanta wannan

2027: Alkawarin da Pantami ya yi wa kiristoci a Gombe da ya kai ziyara coci

Yusuf Haruna ya fara da Sani Yahaya Jingir, wanda ya ce kaf Najeriya babu malamin Musulunci da ya sha wahala da kiristoci irin shi.

Uzurin da Baban Chinedu ya yi wa Sani Jingir

Ya ce sai da kiristoci suka yi yunkurin hana Sheikh Sani Yahaya Jingir yin sallah, bayan hallaka mutanen shi da-dama da aka yi.

Saboda wannan adawa a Jos ne ya ce Jingir ya dauki tallar tikitin Muslim-Muslim, amma duk da haka ya hararo kuskuren malamin.

Duk da ya yi masa uzuri, amma Baban Chinedu ya ce shehin bai la’akari da cewa yawon maganarsa ta wuce garin Jos, ana jin sa ko ina.

Baban Chinedu: 'Pantami ya cancanta amma bai da mu'amala'

A Gombe kuwa, Baban Chinedu ya nuna Isa Ali Pantami yana da damar neman takara, amma ya zarge shi da rashin iya hulda mutane.

Idan ana zancen ilmin zamani da yin kokarin lokacin da ya rike hukumar NITDA da minista a gwamnati, ya ce Isa Pantami ya yi fice.

Wani wuri da ya ga na raunin sa shi ne rashin taimakon ‘yan siyasa da yake ofis, ya ce za a rankwala shi da kasa tun wajen neman tikiti.

Kara karanta wannan

Duk da adawarsu da Tinubu, an yi abin da sai da Atiku da Obi suka yaba masa

Ai bai da mu’amala. Gaba daya malam bai da mu’amala.

- Baban Chinedu

Da aka zo da kan batun nagarta, tsohon ‘dan wasan kwaikwayon ya yarda Pantami yana da nagartar rike har Najeriya, ya kuma rantse da Allah.

Baban Chinedu ya ce:

WalLahi yana da nagarta. Amma fa mu’amala a cikin 100%, bai fi 10% ya dauka ba. Ba ma da ‘yan siyasar ba, mu’amala ma da mutane shi bai iya ba.
Isa Pantami da Baban Chinedu
'Dan takarar gwamna a Gombe, Isa Pantami da malami mai wa'azi, Baban Chinedu Hoto: Prof. Isa Ali Pantami/Baban Chinedu
Source: Facebook

Shawarar da aka ba Sheikh Pantami

Da ‘dan jaridar ya tambaya ko sauran malamai ba su ba shi shawara ya gyara, sai ya ce ba dole ba ne ya dauki shawarar ko an ba shi.

Baban Chinedu ya ce tunda ya shiga siyasa, ko da haka halin malamin addinin yake, ya kamata ya canza da nufin samun karbuwa.

“Malam bai da mu’amala, tsakani da Allah ba zan boye maka ba.”

Duk da shi ba ‘dan siyasa ba ne, Baban Chinedu ya ce ko da zaben tsaida gwani aka shiga, ba dole ba ne Isa Pantami ya samu nasara ba.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya nema a wurin Sheikh Karibullah a lokacin yana shugaban kasa

A cewarsa, idan shehin malamin ya yi sake, har a unguwarsu ta Pantami sai an doke shi duk da kasancewarsa mutumin kirki mai amana.

Baban Chinedu ya ce ya fadi wannan ne saboda ya yi hulda da shi kuma haka sauran wadanda suka yi alaka da Sheikh Pantami suke fada.

Pantami ya ziyarci coci a Gombe

Wannan rahoto ya dauko maku hudubar da Isa Ali Pantami ya yi a cocin ECWA a Gombe har da jawo ayoyin Bible da yake yi wa kiristoci jaje.

An ji yadda ta kaya tsakanin Isa Ali Pantami da kiristoci da shehin ya ziyarci coci a garin Gombe a sakamakon wata gobara da ta yi masu barna.

'Dan takaran gwamnan ya ce ba kamfe ya kawo shi ba illa ya yi masu jajen abin da ya faru da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng