
Nasir Ahmad El-Rufai







Manyan 'yan adawa ciki har da Atiku Abuabakar, Nasir El-Rufa'i da Peter Obi sun kalubalanci sanya dokatar ta-baci a jihar Rivers da sauke gwamna Simi Fubara.

Yayin da yan adawa ke kokarin kawo cikas ga mulkin Bola Tinubu a 2027, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan APC sun kafa kawance.

Manyan 'yan siyasa ba su fara amsa kiran tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i na a hade wuri guda domin fatattakar gwamnatin Bola Tinubu ba.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i a bayyana takaici a kan yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya wulakanta dokar kasa ta hanyar dakatar da gwamna.

'Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun bayyana rashin jin dadinsu bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i ya kira su da jahilai, marasa ilimi.

Wani masani mai sharhi kan harkokin siyaaa, Kelly Agada ya ce hogewar El-Rufai wajen iya tara jama'a da kuma ƙulla kawance da manyan ƴan adawa za su taimake shi.

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen jihar Kaduna, ta musanta zargin da Nasir El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin Uba Sani na sata.

El-Rufai ya ce Uba Sani ya kori shugaban KADIRS ne saboda ya bukaci shugaban majalisa, Yusuf Liman, da ya biya haraji kan Naira biliyan 10 da ya ajiye.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi sabon zargi kan gwamnatin da ta gaje shi. Ya ce Uba Sani ruf da ciki yake yi da kudin Kaduna.
Nasir Ahmad El-Rufai
Samu kari