2027: Yadda Tinubu, Atiku da Sauran Ƴan Takara ke Shirin Amfani da Tsofaffin Gwamnoni

2027: Yadda Tinubu, Atiku da Sauran Ƴan Takara ke Shirin Amfani da Tsofaffin Gwamnoni

  • Jam'iyyun siyasa sun tsananta shirin yaƙin neman zaɓen 2027, yayin da ake ita ma hukumar INEC ke daura damarar tunkarar gagarumin zaben
  • Rahotanni sun gano wadanda ake zaton yan takarar APC, ADC da sauransu ke ciki mika wa jagorancin kamfen domin tattaro kuri'ar 'yan Najeriya
  • Wannan zai zama daya daga cikin zabuka masu zafi da za a fafata a kasar nan ganin yadda dukkanin yan takara suka dauki zafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Yayin da saura ƙasa da makonni biyu a fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a hukumance, manyan jam'iyyun siyasar Najeriya sun tsananta tattaunawa kan waɗanda za su jagoranci ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓensu.

Bincike ya nuna cewa jam'iyyun na bai wa muƙamin Darakta Janar muhimmanci matuƙa, domin shi ne ke kula da tsara kamfen, haɗa kan shugabanni, tafiyar da hulɗa da masu ruwa da tsaki, tara kuɗaɗe da kuma isar da manufofin ɗan takara ga masu kaɗa ƙuri'a.

Kara karanta wannan

"Farfaganda ce": Atiku ya zargi gwamnati da jefa Najeriya a wahala

Yan takara sun fara shirin kamfen
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, Atiku Abubakar mai neman kujerar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Binciken da jaridar Punch ta yi ya bayyana cewa hukumar zabe ta INEC ta tsara ranar 19 ga Agusta, 2026 a matsayin ranar fara kamfen na shugaban ƙasa, abin da ya sa jam'iyyu suka ƙara kaimi wajen kammala shirye-shiryensu.

2027: Su waye za su tsaya wa Atiku?

Rahotanni sun nuna cewa jam'iyyar ADC ta fi karkata ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, domin ya jagoranci kamfen ɗin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Majiyoyi sun bayyana cewa idan aka tabbatar da naɗin, Tambuwal zai sake riƙe irin rawar da ya taka a zaɓen 2023 lokacin da ya jagoranci kamfen ɗin Atiku a jam'iyyar PDP.

Ana ganin Tambuwal zai yi wa ADC jagoran kamfen a 2027
Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal Hoto: Aminu Waziri Tambuwal media office
Source: Twitter

Wata majiya ta ce:

"Tambuwal ne ke kan gaba a halin yanzu."

Majiyar ta ƙara da cewa Tambuwal zai yi aiki kafada da kafada da abokin takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, wajen tsara da aiwatar da dabarun kamfen a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta dakatar da wani babban biki a Yobe, an cafke ɗan TikTok a Kano

An fara hararo masu yi wa Tinubu kamfen

A ɓangaren APC kuwa, majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa da jam'iyyar sun ce tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, da gwamnan Imo, Hope Uzodimma, su ne ke kan gaba wajen jagorantar kamfen ɗin Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Wata majiya ta bayyana cewa:

"A yanzu ba a yanke hukunci ba. Amma Hope Uzodimma ne ake ganin zai iya jagorantar ƙungiyar kamfen ta APC, duk da cewa hakan na iya sauyawa kafin a yanke hukunci na ƙarshe."

Ana kuma cewa APC na la'akari da gogewar siyasa, karɓuwa a yankuna da kuma daidaiton addini kafin ta sanar da wanda za ta zaɓa.

A jam'iyyar LP kuwa, sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Ken Asogwa, ya tabbatar da cewa an riga an zaɓi Darakta Janar na kamfen, amma za a bayyana sunansa ne tare da cikakken tsarin kamfen kafin ranar 19 ga Agusta.

Shi ma SDP ya ce ya kusa kammala shirye-shiryensa, inda ya bayyana cewa ba da daɗewa ba zai sanar da cikakken tsarin ƙungiyar kamfen ɗinsa gabanin fara yaƙin neman zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun saki sunayen mutane 2 da ke ba 'yan bindiga bayanai a Bauchi

INEC ta fitar da sunan dan takarar PDP

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta Fftar da sunan dan takarar PDP da zai kara da Bola Tinubu a 2027 sabanin Goodlukc Jonathan da aka yi zato a baya.

Bangaren jam'iyyar PDP mai goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi murnar fitar da sunan Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, aka ajiye na tsagin Saminu Turaki.

Jam'iyyar ta ce matakin da INEC ta ɗauka ya kawo ƙarshen jita-jitar cewa PDP ba za ta iya fitar da ɗan takara ba a zaɓen 2027 PDP ta kuma yi kira ga mambobin da suka fusata su dawo jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng