ICPC Ta Gurfanar da El Rufai da Wasu 6 kan Badakalar Kwangilar Naira Biliyan 8.6

ICPC Ta Gurfanar da El Rufai da Wasu 6 kan Badakalar Kwangilar Naira Biliyan 8.6

  • ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da tsohon hadiminsa da kuma wasu kamfanoni kan tuhume-tuhume 11
  • Hukumar ta zargi El-Rufai da amincewa da kwangilar CCTV da kudinta ya haura N8.65bn da ake zargin ta saba wa dokar saye da sayarwa
  • Da aka karanta masu tuhume-tuhumen, El-Rufai da Jimi Lawal sun musanta aikata su, yayin da kotu ta sanya ranar sauraron bukatar belinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, da wasu shida kan tuhume-tuhume 11 da suka shafi zargin cin hanci, safarar kudi da sauran laifuka.

An shigar da karar ne a gaban Mai shari’a Hauwa’u Buhari ta Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna karkashin lambar shari’a FHC/KD/93C/2026.

ICPC ta gurfanar da El-Rufai da wasu kan zargin cin hanci a kwangilar N8.65bn
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a dakin da yake bitar karatu. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Wadanda ICPC ke tuhuma tare da Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da shugaban Fulani na Miyetti Allah bayan cafke shi kan $2.5m

A cikin karar da aka yi wa kwaskwarima, ICPC ta ambaci El-Rufai a matsayin wanda ake tuhuma na farko, kamar yadda rahoton Tribune ya nuna.

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da tsohon babban mai ba gwamnan shawara na musamman, Jimi Adebisi Lawal, da kamfanoni da suka hada da:

  • Singularity Network Security Limited
  • Solar Life Nigeria Limited
  • Knowledge Investment Nigeria Limited
  • Intercellular Nigeria Limited
  • Noble Coast Resources Limited

Haka kuma, an ambaci Bashir El-Rufai, babban dan uwan tsohon gwamnan, a daya daga cikin tuhume-tuhumen, amma hukumar ta ce tana nemansa ruwa a jallo.

Zargin badakalar kwangilar CCTV

ICPC ta zargi El-Rufai da amincewa da bayar da kwangilar samarwa, tsarawa da girka na’urar CCTV a birnin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

Hukumar ta ce an bayar da kwangilar ne kan kudin da ya kai N8.68bn, ga kamfanin Singularity Network Security Limited.

A cewar ICPC, kamfanin ba shi da isasshen kwarewa da cancantar gudanar da aikin, kuma matakin ya saba wa dokokin saye da sayarwa na gwamnati.

Hukumar ta kuma yi zargin cewa an rika tura kudaden da aka samu daga wannan aiki zuwa ga wasu kamfanoni da mutane daban-daban.

Kara karanta wannan

'Isra'ila ta hallaka dubban yara kanana da gangan a Falasdinu'

Hukumar ICPC tana tuhumar El-Rufai da bada kwangilar N8.68bn ba bisa ka'ida ba
Hedikwatar hukumar ICPC da ke a babban birnin tarayya Abuja. Hoto: @icpcnigeria
Source: Facebook

El-Rufai ya musanta zarge-zargen

ICPC ta ce zarge-zargen sun saba wa tanadin dokar haramta safara da wanke kudaden haram, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Lokacin da aka karanta tuhume-tuhumen a gaban kotu, El-Rufai da Jimi Lawal sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su.

Bayan karanta tuhume-tuhumen, kotu ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 1 ga Yuli, 2026 domin yanke hukunci kan bukatar belin da wadanda ake tuhumar suka shigar.

ICPC ta bayyana cewa za ta ci gaba da gabatar da hujjoji a kan zarge-zargen da ta shigar a gaban kotu.

An dage shari'ar El-Rufai zuwa Satumba

A wani labari, mun ruwaito cewa, Malam Nasir El-Rufai ya shafe sama da kwanaki 120 a tsare a hannun hukumomi tun 16 ga Fabrairun 2026.

Yayin da tsohon gwamnan ke tsare, kotu ta ɗage shari’ar cewa El-Rufa'i ya saurari wayar Nuhu Ribadu zuwa ranar 22 ga Satumban 2026.

Za a cigaba da rike shi saboda ya kasa cika sharudan beli da suka haɗa da samun ma'aikaci mai gida Maitama ko Asokoro a Abuja da zai tsaya masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com