An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi
Sheikh Bello yabo dan asalin jihar Sokoto ya shiga hannun jami'an tsaro tun bayan bazuwar bidiyon da ya caccaki gwamnan Kaduna a kan hana sallar Idi.
A wani sautin murya mai tsayin kusan minti biyar, malamin addinin Islama mai suna Sheikh Bello Yabo, ya caccaki Gwamna Malam Nasir El-Rufai saboda hana sallar Idi da yayi a jihar Kaduna.
A sautin muryar, ya yi kira ga Musulmi da su bijirewa hukumomi a kowanne gari da aka hana su fita sallar Idin karamar sallar don dakile yaduwar cutar korona, kamar yadda jaridar SaharaReporters ta ruwaito.
Malamin ya yi ikirarin cewa, gwamnan jihar Kaduna da duk takwarorinsa da suka hana sallar Idi ba korona suke yaka ba, Musulunci suke yaka.
Ya zargi gwamnan da bada kwanaki biyu tak don zuwa kasuwanci da siyayya amma ya hana zuwa Masallaci.
Malamin ya kara da cewa cutar korona duka karya ce don babu ita.
Ya zargi gwamnan da nuna tsabar yahudanci amma yana dogaro da cutar korona.
KU KARANTA: Kano: Yadda aka cika makil a masallatan Juma'a (Hotuna)
A wani labari na daban, Uche Achi-Okpaga, sakataren yada labarai na Ohanaeze Ndigbo, ya zargi shugabannin arewa da dora wa yankin kudu nauyin almajiran jihar.
A wata tattaunawar da yayi da jaridar The Punch, Achi-Okpaga ya zargi shugabannin yankin da kirkiro matsala a tsakaninsu ta hanyar mayar da almajiran jihohinsu.
Sau da yawa, kananan yara masu shekaru tsakanin hudu zuwa 15 ake tura su wurin malamai masana ilimin Qur'ani don neman ilimi.
Da yawa daga cikinsu na karewa da bara don samun abinci da sadaka don kuwa malaman basu iya ciyar dasu.
Tun bayan barkewar annobar Coronavirus, wasu gwamnonin a yankin arewa sun dinga mayar da almajirai jihohinsu.
Mai magana da yawun Ohanaeze yace, wannan ya saba dokar hana shige da fice tsakanin jihohi. Ya kara da cewa barin almajiran a inda suke ya fi a maimakon mayar dasu jihohinsu na asali.
"Kungiyar kabilar Igbo ta matukar damuwa da yadda almajirai ke ci gaba da shiga yankin kudancin Najeriya," yace.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng