Adeleke Ya Zargi EFCC da Shirin Yi wa Gwamnatinsa Illa gabanin Zaɓen Osun
- Gwamna Ademola Adeleke ya yi zargin cewa EFCC na shirin daskarar da asusun gwamnatin Osun kafin zaben da za a gudanar a jihar
- Ya bayyana haka ne yayin da ya rage makonni a gudanar da zaben gwamnan jihar da ya dade ya na jawo cece-kuce a tsaknin manyan jam'iyyu
- Gwamnan, wanda daya ne daga cikin yan takara a jihar na tsoron EFCC na shirin daukar matakin ne domin jawo masa gagarumar matsala a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Osun – Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya yi zargin cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) na shirin daskarar da asusun gwamnatin jihar da na manyan jami'an gwamnatinsa.
Ya yi zargin cewa ana shirya hakan ne gabanin zaben gwamna da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta 2026 domin kokarin dakile ayyukansu.

Source: Instagram
Tribune Online ta kawo labarin cewa hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kai na jihar, Oluomo Kolapo Alimi, ya fitar a Osogbo ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2026.
Zargin gwamnan Ogun kan EFCC
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Adeleke ya ce ya samu sahihan bayanai cewa EFCC ta kammala shirin daukar wannan mataki na daskarar da asusun gwamnati.
A cewarsa, idan aka aiwatar da wannan mataki, zai zama babban take doka, domin zai kawo cikas ga gudanar da harkokin gwamnati a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben gwamna.
Ya kara da cewa babu wata hujjar doka da za ta ba da damar daskarar da asusun gwamnatin Jihar Osun, yana mai jaddada cewa EFCC ba ta da ikon yin hakan kan gwamnatin jiha.
Me EFCC ta ce game da zargin Adeleke?
Saboda haka, Gwamnan ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da kuma jama'a su lura da abin da ya kira wannan ci gaba mai tayar da hankali.
Sai dai har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa da ke mayar da martani kan zargin da gwamnan ya yi ba.

Source: Twitter
Wannan zargi ya zo ne kwana guda bayan Adeleke ya roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani kan abin da ya bayyana a matsayin kashe-kashe, tsoratarwa da kuma tsare mutane ba bisa ka'ida ba a Osun kafin zaben gwamna.
Da yake jawabi a wani gangamin yakin neman zabe a Osogbo a farkon mako, gwamnan ya ce al'ummar jihar za su yi tir da duk wani yunkuri na magudin zabe, tare da rokon Shugaba Tinubu ya hana maimaita rikicin zaben da aka taba gani a tsohuwar Yankin Yamma.
APC ta fara hararar kujerar gwamnan Osun
A baya, mun kawo labarin cewa jam'iyyar APC mai mulki ya fara kokarin razana takarar gwamna jihar Osun yayin da ake tunkarar zaben jihar a cikin yan makonni da ke tafe.
A yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na gwamnan jihar, Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce nasara ta tabbata domin sun shirya wajen tattaro masoyansu.
Manyan da ke cikin kwamitin sun hada da Ibrahim Kabir Masari, sai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau da wasu manyan yan siyasa da ake ganin za su taimaka wajen nasarar APC
Asali: Legit.ng

