Kai Tsaye: Yadda Zaben Gwamnan Jihar Ekiti ke Gudana, APC na Neman Kafa Tarihi
Zaben Ekiti na tafiya cikin lumana - Yan sanda
Kwamishinan 'Yan Sanda da ke sanya idanu kan harkokin tsaro a zaben gwamnan Jihar Ekiti, Abayomi Shogunle, ya tabbatar da cewa ba a sami wani rahoton tashin hankali ba kawo yanzu.
Ya ce babu wani rahoto da ke nuna tursasawa ko tashin hankali tun bayan da aka fara gudanar da zaben a fadin jihar yau Asabar.
The Nation ta ve yayin da yake tattaunawa da manema labarai a garin Erijiyan-Ekiti, Shogunle ya bayyana zaben a matsayin mai cike da lumana.
Ya bayyana cewa masu zabe sun nuna da'a da kwanciyar hankali, yayin da hukumomin tsaro kuma suka baza jami'ansu sosai a daukacin runfunan zabe.
Sanata Bamidele ya isa rumfar zabensa
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Opeyemi Bamidele, ya isa runfar zabensa domin kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Ekiti da ke gudana.
A wani faifan bidiyo da The Nation ta wallafa, an ga magoya bayansa sun tarbe shi cikin murna da sowa yayin da ya wuce domin tantance shi kana ya jefa kuri'arsa kamar kowa.
An yi wa direban dan takarar ADC duka
Dan takarar jam'iyyar ADC a Ekiti, Dare Bejide a bayyana cewa an yi wa direban shi duka yayin da ake zaben gwamna.
Ya ce:
"Sun yi wa direba na duka, sun masa jina-jina. sun ci zarafin jami'an tsaro na."
Mataimakiyar gwamnan Ekiti ta kada kuri'a
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Ekiti kuma 'yar takarar mataimakin gwamna ta APC. Cif (Mrs) Monisade Afuye, ta yaba wa masu zabe saboda nuna kishin kasa yadda suka fito domin kad kuri'a.
Haka zalika, Mrs Afuye ta jinjina wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kuma hukumomin tsaro bisa rashin nuna banbanci a zaben da ke gudana yau Asabar.
Mrs Afuye ta bayyana haka ne yayin da take kada kuri'arta a runfar zabe ta 003, da ke mazabar Atiba/Aafin 1, a garin Ikere Ekiti.

Source: Facebook
Mazauna jihar Ekiti sun yaba da zabe cikin lumana
Yayin da jefa kuri’a ke ci gaba a zaben gwamnan Jihar Ekiti, wani mazaunin Ikere ya nuna godiya kan zaman lafiyar da aka samu a fadin jihar bayan kaɗa kuri’arsa.
“Mun gode wa Allah da zaben ya gudana cikin zaman lafiya” — wani mazaunin Ekiti ya bayyana bayan ya kaɗa kuri’arsa.
The Nation ta ce ana ci gaba da gudanar da zaben cikin lumana a wurare da dama kamar yadda mutane suka tabbatar.
Oyebanji ya aika sako
Dangane da matsalolin na'urar BVAS, Gwamna Biodun Oyebanji ya yi kira da a yi haƙuri da hukumar zaɓe, The Cable ta kawo rahoton.
“Komai yana tafiya daidai, kuma zaɓen yana gudana cikin lumana. Mutane suna cikin farin ciki, kuma fitowar masu zaɓe abin a yaba ne."
“Mun samu gamsuwa. Sai dai, ina buƙatar yin kira ga mutanenmu da su ci gaba da yin haƙuri da INEC."
“Za a gyara dukkan waɗannan matsaloli, kamar yadda INEC da kanta ta ba ni tabbaci.”
- Gwamna Biodun Oyebanji
Gwamna Oyebanji ya isa rumfar zabe
Gwamna Biodun Oyebanji ya isa rumfar zaben domin kada kuri'arsa a zaben gwamnan jihar Ekiti, rahoton TheCable ya nuna hakan.
Zai kada kuri'a ne a PU03, Ward 6, karamar hukumar Ekiti ta Yamma.
Fayose ya kada kuri'a, ya hango nasarar Oyebanji
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce nasarar Gwamna Biodun Oyebanji kusan tabbatacciya ce.
Fayose ya zanta da manema labarai bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a garin Afao-Ekiti, da ke Ƙaramar Hukumar Irepodun/Ifelodun a jihar Ekiti, cewar rahoton TheCable.
“Oyebanji ya riga ya lashe zaɓen nan. Idan ka dubi yadda abubuwa suke tafiya a jihar nan da kuma yanayin yadda mutane ke nuna goyon bayansu, ina hasashen gagarumar nasara a gare shi.”
- Ayodele Fayose
Kayan zabe sun ki isowa
Tuni dai an fara shirin sanin wanda zai zama gwamnan jihar Ekiti.
Masu kada kuri’a a karamar hukumar Afao-Ekiti a jihar Ekiti sun koka cewa an dade ba a kawo masu kayayyin zabe ba.
Kamar yadda The Nation ta rahoto, tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Peter Fayose ya fito ne daga garin Afao-Ekiti.
BVAS ya ki aiki da kyau
A wani rahoton na The Nation har ila yau, an ji cewa wasu sun yi korafin cewa na’urar BVAS ba ta aiki da kyau a wajen zaben.
Sanata Babafemi Ojudu wanda ya taba zama Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, yana cikin masu wannan koke.
An fara kada kuri'a a mazabun jihar Ekiti
Karamar Hukuma (LGA): Ado
Wuri: Filin rukunin Chief Elerebi, daura da asibitin haihuwa d ke kan titin Okeyinmi.
Lambar mazaba: 06
Rumfar zabe: 013
Rahotanni sun nuna cewa an fara kada kuri'a, inda ake tantance masu zabe kafin a ba su damar jefa kuri'unsu a rumfar zabe ta 013 da ke mazaba ta 06 a karamar hukumar Ado.

Source: Facebook
Hukumar INEC ta fara raba kayayyakin zabe
Jami'an zabe (SPO) da sauran ma'aikata wucin gadi, a yanzu haka sun fara jigilar kayayyakin zabe, wadanda suka hada da akwatunan zabe, rumfuna da kuma rijistar masu zabe zuwa wuraren da aka tura su.
Aikin na tafiya cikin tsari da kwanciyar hankali. Sai dai kuma, masu sanya idanu kan zaben sun lura cewa jami'an tsaro da ke wurin raba kayan ba su da yawa, domin kuwa 'yan sanda kadan ne aka tura.
Mutane miliyan 1 ne zasu yanke hukunci a zaben Ekiti
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriya (INEC) ta sanar da kammala aikin raba katin zabe (PVC) cikin nasara domin gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti.
Kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito, INEC ta bayyana cewa sama da masu zabe miliyan 1.02 ne suka karbi katunansu gabanin zaben gwamnan jihar Ekiti na shekarar 2026.
EFCC sun dura rumfar zaben gwamna
Labari da dumin da aka samu yanzu shi ne jami’an EFCC sun je rumfar zaben gwamna Biodun Oyebanji a Ekiti.
An ga ma’aikatan hukumar a unguwar Ikogosi a Ekiti ta yamma sakamakon zargin da aka ji cewa ana sayen kuri’un jama’a.