PDP Ta Kassara APC a Zaben Cike Gurbi, Na hannun Daman Wike Ya Yi Nasara
- Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi da aka yi na sanata a ranar Asabar 20 ga watan Yunin shekarar 2026
- INEC ta ce ɗan takarar PDP, Olaka Nwogu, shi ne wanda ya lashe zaɓen cike gurbin sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas
- Ta ce ta samar da na’urorin BVAS na madadin domin magance matsalolin fasaha tare da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin sauƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a Rivers.
Hukumar ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar PDP, Olaka Nwogu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbin sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas.

Source: Facebook
Jam’iyyun siyasa huɗu ne kawai tare da ‘yan takararsu INEC ta amince su shiga zaɓen, sun haɗa da APC, PDP, AA da LP, cewar Punch.
An maye gurbin marigayi Sanata Barry Mpigi
An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin marigayi Sanata Barry Mpigi, wanda ya rasu a watan Fabrairun wannan shekara da muke ciki ta 2026.
An yi zaɓen ne a ƙananan hukumomi bakwai da suka haɗa da Khana, Gokana, Tai, Eleme, Andoni, Oyigbo da Opobo.
Da take sanar da sakamakon zaɓen a cibiyar tattara sakamako da ke Bori, Farfesa Rosemary Ogu ta bayyana cewa Nwogu Olaka Johnson ya samu ƙuri’u 46,961.
Ta ce ɗan takarar PDP ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Osarokaka Ebenezer Erewari na APC, wanda ya samu ƙuri’u 1,647 kacal.
Jami’ar ta ƙara da cewa Nwogu ya cika dukkan sharuddan doka, saboda haka an ayyana shi a matsayin zababben sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas.

Source: Original
Yawan kuri'in sauran jam'iyyu a zaben
A cewarta, Douglass Fabeke na jam’iyyar AA ya samu ƙuri’u 1,175, yayin da Sam Kinani na LP ya samu ƙuri’u 367.
A halin da ake ciki, hukumar INEC ta ce tana ɗaukar matakan magance matsalolin da suka shafi na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS domin tabbatar da ingantaccen zaɓe.
Shugabar sashen wayar da kan masu zaɓe ta INEC a Rivers, Geraldine Ekelemo, ta bayyana hakan yayin rangadin wasu yankunan da aka gudanar da zaɓen.
Ta ce hukumar ta tanadi na’urorin BVAS na madadin domin amfani da su idan wata na’ura ta samu matsalar aiki, cewar TheCable.
Ekelemo ta ce INEC ta yi shiri tun da wuri wajen magance matsalolin fasaha da aka samu a wasu rumfunan zaɓe kaɗan.
APC ta lashe zaben cike gurbi a Kano
Mun ba ku labarin cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi da aka yi na majalisar wakilai a jihar Kano.
INEC ta jagoranci gudanar da zaben cike gurbin ne bayan rasuwar dan majalisar tarayya, Hon. Muhammad Hassan daga Kano.
Sakamakon ya nuna APC ta ci gaba da riƙe kujerar mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa, bayan sauran ’yan takara sun samu ƙuri’u kaɗan a zaɓen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

