'Dalilin da Ya Sa na Ziyarci Kabarin Kawuna kafin zuwa Rumfar Zaɓe': Gwamna Adeleke

'Dalilin da Ya Sa na Ziyarci Kabarin Kawuna kafin zuwa Rumfar Zaɓe': Gwamna Adeleke

  • Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa ya ziyarci kabarin marigayi dan uwansa, Isiaka Adeleke, kafin ya je rumfar zaɓe
  • Adeleke ya ce Isiaka, tsohon gwamnan Osun, ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa da tafiyar siyasarsa, kuma har yanzu yana kewarsa sosai
  • Gwamnan ya bayyana cewa yana ziyartar kabarin dan uwansa domin neman addu'a kafin zaɓe, yana mai cewa nasararsa ta biyu na da muhimmanci gare shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana dalilin da ya sa ya ziyarci kabarin marigayi kawunsa, Sanata Isiaka Adeleke.

Adeleke ya kai ziyara kabarin ne kafin ya je rumfar zaɓe a zaben gwamnan da aka gudanar ranar 15 ga Agusta.

Gwamna Adeleke ya ziyarci kabarin kawunsa kafin dangwala kuri'a
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun da ya lashe zabe. Hoto: Ademola Adeleke.
Source: Facebook

A wata hira da Channels TV, Adeleke ya ce ziyarar wani bangare ne na hanyar girmama marigayi kawunsa, wanda ya bayyana a matsayin mutum mai muhimmiyar rawa a rayuwarsa da tafiyar siyasarsa.

Kara karanta wannan

APC ta saba da Tinubu kan zaben Osun, ta bayyana matsayarta kan nasarar Adeleke

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake magana kan nasarar da ya samu a zaɓen, inda ya samu damar lashe wa’adi na biyu bayan kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC.

Da yake magana kan rawar da ‘yan uwansa suka taka wajen nasararsa, Adeleke ya ce marigayi dan uwansa, Isiaka, ya yi tasiri sosai a kansa, yana mai cewa suna da halaye iri daya kuma dukansu suna son rayuwa.

Ya ce:

"Ina tunanin da ni da marigayi kawuna, Isiyaka kun san shi ko, muna kama a fannoni da dama, muna yin komai iri daya.

Da aka tambaye shi ko yana kewar marigayi dan uwansa, Adeleke ya ce:

"Sosai ma kuwa, ina kewarsa sosai, idan na tuna shi har kuka nake yi, ina zuwa kabarinsa na fada masa yadda nake kewarsa.
"Ko jiya ma kafin zabe, na je ni kabarinsa kafin na kada kuri'a ta, na ce masa na sake dawowa, ina son ka yi mani addu'ar samun nasara."

A cewar Adeleke, ziyartar kabarin marigayi kawunsa kafin ya kada kuri’a na da muhimmanci saboda irin kusancin da ke tsakaninsu da kuma tasirin da Isiaka Adeleke ya yi a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 da suka sa Adeleke ya tumurmusa APC a zaben Osun

Ya ziyarci kabarin kafin ya wuce rumfar zaɓensa, inda ya kada kuri’a a lokacin zaɓen.

Sanata Isiaka Adeleke shi ne gwamnan farar hula na farko a Osun, sannan daga baya ya wakilci mazabar Osun West a Majalisar Dokokin Tarayya.

Ziyarar da Adeleke ya kai kabarin marigayi kawunsa kafin kada kuri’a ta ja hankalin jama’a, musamman bayan da ya samu nasarar lashe zaɓen.

Gwamnan ya gode wa al’ummar Osun bisa goyon bayan da suka ba shi domin samun wa’adi na biyu, yana mai alkawarin ci gaba da aiki don ci gaban jihar.

Zaben Osun: APC ka iya zuwa kotu

An ji cewa kwamitin yakin neman zaben gwamnan APC a Osun ta yi watsi da sakamakon zaben ranar 15 ga Agustan 2026.

Daraktan-Janar na yakin neman zaben, Oluwole Oke, ya ce jam’iyyar ta fara duba kayayyakin zaben kafin ta yanke shawarar matakin da za ta dauka.

APC ta ce za ta iya zuwa kotu idan bincikenta ya gano dalilan da za su ba ta damar kalubalantar sakamakon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.