APC Ta Saba da Tinubu kan Zaben Osun, Ta Bayyana Matsayarta kan Nasarar Gwamna Adeleke
- Kwamitin yakin neman zaben gwamnan APC a Osun ta yi watsi da sakamakon zaben ranar 15 ga Agusta, yana mai cewa Ademola Adeleke bai samu mafi yawan ingantattun kuri’u ba
- Daraktan-Janar na yakin neman zaben, Oluwole Oke, ya ce jam’iyyar ta fara duba kayayyakin zaben kafin ta yanke shawarar matakin da za ta dauka
- APC ta ce za ta iya zuwa kotu idan bincikenta ya gano dalilan da za su ba ta damar kalubalantar sakamakon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Kwamitin yakin neman zaben gwamnan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.
Kwamitin yakin zaben ya bayyana cewa Gwamna Ademola Adeleke bai samu mafi yawan ingantattun kuri’un da aka kada ba.

Source: Twitter
Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben APC, Oluwole Oke, ya bayyana hakan yayin wata hira da Arise News ranar Litinin, 17 ga watan Agustan 2026.
A yayin hirar, ya yi bayanin dalilin da ya sa jam’iyyar ba ta taya Adeleke murnar sake lashe zabe ba.
APC ta ki amincewa da sanarwar INEC
Oke ya ce jam’iyyar ba ta amince da sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi ba, kuma ta fara duba kayayyakin zaben kafin ta yanke shawarar matakin da za ta dauka.
“Ba mu amince da sanarwar INEC ba. Wannan shi ne matsayinmu a yanzu. Mun yi amanna cewa bai samu mafi yawan ingantattun kuri’u ba,” in ji shi.
Ya ce kwamitin yakin neman zaben APC ba zai bari a matsa masa lamba ya amince da sakamakon zaben ba har sai ya kammala bincike mai zurfi kan yadda aka gudanar da zaben.
“Abin da nake fada maka shi ne, abin da muke yi yanzu, har ma domin samun bayanan da za su kasance a nan gaba, shi ne gudanar da cikakken nazari kan tsarin gaba daya sannan mu bayyana matsayarmu."
“Ba za mu bari a matsa mana lamba ta yadda za mu yi gaggawar taya Sanata Ademola Adeleke murna ba." In ji shi.
APC ta fara bincike kan zaben
Duk da cewa Shugaba Bola Tinubu ya taya Adeleke murnar nasarar da ya samu bayan sanar da sakamakon, Oke ya ce matsayin kwamitin yakin neman zaben APC ya kasance daban, domin ya mayar da hankali ne kan binciken abubuwan da suka faru a lokacin zaben.
Ya ce jam’iyyar ta fara binciken zaben tare da umartar wakilanta a fadin jihar su mika muhimman takardun zabe domin a duba su.
“Mun fara aikin tantance zaben. Mun bukaci dukkan wakilan jam’iyyarmu su mika kwafe-kwafen Form EC8A, B da C ga sakatariyar jam’iyyarmu domin a duba su. Muna bukatar mu binciki wadannan kayayyaki,” In ji shi.
APC na nazarin doka
Shugaban yakin neman zaben APC ya ce binciken zai shafi yadda aka gudanar da zaben da kuma batutuwan da suka taso kafin zaben, ciki har da bin tanade-tanaden Dokar Zabe da sauran dokokin da suka dace.

Kara karanta wannan
Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027
Ya kuma nuna cewa jam’iyyar na iya daukar matakin shari’a idan sakamakon bincikenta ya gano dalilan da suka dace da hakan.
A cewar APC, tsarin zabe bai tsaya kawai kan sanar da sakamakon ba, domin batun na iya ci gaba zuwa kotun sauraron kararrakin zabe, Kotun Daukaka Kara da kuma Kotun Koli idan ya zama dole.

Source: Twitter
Kananan hukumomin da Adeleke ya lashe
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party ya lashe kananan hukumomi 19 cikin 30 a zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar.
Sakamakon da aka tattara daga cibiyoyin tattara sakamako na kananan hukumomin ya nuna cewa Adeleke ya samu jimillar kuri’u 511,067.
Asali: Legit.ng

