Oyebanji: Muhimman Abubuwa 5 da ba Ku Sani ba game da Zababben Gwamnan Ekiti

Oyebanji: Muhimman Abubuwa 5 da ba Ku Sani ba game da Zababben Gwamnan Ekiti

  • An gudanar da zaɓen gwamnan Ekiti cikin lumana a ranar 20 ga Yuni, 2026, inda ɗan takarar APC, Biodun Oyebanji, ya samu nasarar lashe zaɓen
  • Oyebanji, haifaffen Ikogosi-Ekiti a 1967, ya fara aikinsa a matsayin malami kafin ya shiga harkokin siyasa kuma ya riƙe muƙamai daban-daban
  • Zababben gwamnan ya samu digirai a Kimiyyar Siyasa daga Jami'ar Ekiti da Jami'ar Ibadan, kuma yana auren Farfesa Olayemi Oyebanji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ado-Ekiti, Ekiti - An gudanar da zaben Ekiti a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2026 domin sake zaɓen sabon gwamnan jihar bayan wa'adin Biodun Oyebanji na shekara hudu.

Jam'iyyun ADC, PDP, LP da sauransu ne suka fafata a zaben wanda ake ganin an gudanar da shi cikin lumana.

Gwamna Oyebanji na Ekiri ya koma wa'adi na 2
Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti. Hoto: Biodun Oyebanji.
Source: Twitter

Muhimman abubuwa game da Gwamna Oyebanji

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ekiti: Dalilan da suka sanya PDP da ADC kasa nasara kan APC

Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Abayomi Oyebanji, ɗan takarar jam’iyyar APC, ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti da aka gudanar a ranar 20 ga watan Yuni, 2026, cewar rahoton Channels TV.

Hukumar INEC ta ce Oyebanji ya samu ƙuri’u 319,224, dan takarar PDP, Oluwole Oluyede, ya samu ƙuri’u 40,543, sannan ɗan takarar ADC, Dare Bejide, ya samu ƙuri’u 12,872 a zaɓen da aka yi.

Legit Hausa ta yi duba kan wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da zababben gwamnan Ekiti.

1. Shekarun Gwamna Biodun Oyebanji

An haifi Oyebanji a watan Disamba na shekarar 1967 a garin Ikogosi-Ekiti da ke Ekiti da ke jihar Ekiti.

A lokacin da.aka sake zaɓensa a karo na biyu, Gwamna Biodun Oyebanji ya kasance yana da shekaru 58 a duniya.

2. Oyebanji ya taɓa zama malami

Gwamna Oyebanji ya fara aikinsa a matsayin malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami'ar Ado-Ekiti a shekarar 1993.

Ya yi aiki a jami’ar na tsawon shekaru huɗu kafin ya koma aiki a tsohon Omega Bank PLC, wanda yanzu ake kira bankin Heritage, inda ya yi aiki har zuwa Mayun 1999.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Ekiti: APC ta aika sako ga Oyebanji bayan samun tazarce

3. Muƙaman siyasa da Biodun Oyebanji ya riƙe

A watan Yunin 1999, ya shiga harkar siyasa a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin majalisa ga tsohon gwamnan Ekiti, Cif Niyi Adebayo.

Daga watan Agustan 2000 zuwa Satumban 2001, ya yi aiki a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman, sannan daga baya ya zama shugaban ma’aikatan gidan gwamnati.

A matakin tarayya, ya kasance shugaban hukumar gudanarwa ta Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Tarayya daga Yunin 2009 zuwa Disamban 2010.

A shekarar 2010, an naɗa shi kwamishinan haɗin kai da hulɗar gwamnatoci a Ekiti a wa’adin farko na Gwamna Kayode Fayemi, cewar rahoton Pulse.

A shekarar 2011, ya zama kwamishinan dabarun sauyi da aiwatar da manufofi, haka kuma ya yi aiki a matsayin kwamishinan kasafi, tsare-tsaren tattalin arziki da isar da ayyuka tsakanin Janairun 2013 da Oktoban 2014.

Lokacin wa’adin biyu na Kayode Fayemi da ya fara a 2018, Oyebanji ya zama Sakataren Gwamnatin Ekiti.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Yadda Gwamna Biodun Oyebanji ya samu tazarce a inuwar jam'iyyar APC

Ya riƙe wannan muƙami har zuwa lokacin da ya tsaya takarar gwamna a karkashin APC a shekarar 2022, inda daga bisani ya yi nasara.

Gwamna Oyebanji ya lashe zaben gwamnan Ekiti
Gwamna Biodun Oyebanji yayin da ya ke kada kuri'a a Ekiti. Hoto: Biodun Oyebanji.
Source: Twitter

4. Zurfin ilimin Gwamna Oyebanji

Oyebanji ya samu digirin farko (B.Sc.) a fannin Kimiyyar Siyasa daga Jami'ar Ondo State, wadda yanzu ake kira Jami'ar Ekiti State, a shekarar 1989.

Daga bisani ya samu digirin digirgir na biyu (M.Sc.) a fannin Kimiyyar Siyasa (Harkokin Ƙasashen Duniya da Nazarin Dabarun Tsaro) daga Jami'ar Ibadan a shekarar 1992.

5. Iyalan Gwamna Biodun Oyebanji

Zababben gwamnan yana auren Dr. Olayemi Oyebanji, wadda gimbiya ce daga Ado-Ekiti kuma farfesa mai daraja a Jami'ar Ibadan.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa aurensu ya yi albarka inda suka samu yar maza da mata wanda da yawansu suka yi aure, cewar Punch.

APC ta taya Oyebanji murnar lashe zabe

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Biodun Oyebanji na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar a ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta taya gwamnan murna kan nasarar da ya samu a zaben wanda ya ba abokan hamayyarsa tazara mai nisa.

APC ta jinjinawa hukumar zabe ta INEC ta sauran masu ruwa da zaki saboda namijin kokarin da suka yi wajen gudanar da zaben.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.