INEC Ta Mika Takarda ga 'Yan Takarar da Suka Lashe Zaben Cike Gurbi a Kano da Wasu Jihohi 5

INEC Ta Mika Takarda ga 'Yan Takarar da Suka Lashe Zaben Cike Gurbi a Kano da Wasu Jihohi 5

  • Hukumar zabe INEC ta mika takardun shaidar nasara ga wadanda suka lashe zabukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar
  • Zabukan sun gudana a mazabun sanatoci, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jiha a Kano, Kebbi da wasu jihohi hudu
  • Hukumar ta ce za ta kuma mika takardar shaidar nasara ga zababben gwamnan Ekiti da wanda ya lashe zaben mazabar Zuru a Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta mika takardun shaidar nasara ga wadanda suka lashe zabukan cike gurbi da aka gudanar ranar 20 ga watan Yuni, 2026, a jihohi shida na kasar nan.

Zabukan sun shafi kujerun Sanata a Enugu, Nasarawa ta Arewa, Ondo ta Kudu da Rivers ta Kudu maso Gabas, kujerar Majalisar Wakilai ta Dawakin Kudu/Warawa a Kano, da kujerar mazabar Zuru ta Majalisar Dokokin jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

2026: Tinubu ya yi martani da dan takarar APC ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

Hukumar INEC.
Yadda INEC ta.kka takardun shaidar lashe zabe da wadanda suka samu nasara a zaben cike gurbi Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC ta tabbatar da mika takardun shaidar nasara da wadanda suka lashe zabukan wadannan mazabu a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X yau Talata.

INEC ta taya zaɓaɓɓun yan takara murna

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, wanda Kwamishinar Hukumar ta Kasa mai kula da jihar Rivers, May Agbamuche-Mbu, ta wakilta, ya halarci taron mika takardun shaidar nasarar.

Da take jawabi, Agbamuche-Mbu ta taya wadanda suka yi nasara murna tare da jaddada muhimmancin wakiltar al’ummarsu yadda ya kamata.

Ta ce babban nauyin da ke kansu yanzu shi ne tabbatar da cewa sun yi wa mutanen da suka zabe su aiki cikin gaskiya da rikon amana.

“Abu mafi muhimmanci shi ne ku wakilci al’ummarku yadda ya kamata tare da sauke nauyin da aka dora muku,” in ji ta.

Za a mika takarda ga gwamnan Ekiti

Agbamuche-Mbu ta kuma bayyana cewa hukumar INEC za ta mika takardar shaidar nasara ga zabaɓɓen gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji a ofishint da ke birnin Ado-Ekiti.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Yadda Gwamna Biodun Oyebanji ya samu tazarce a inuwar jam'iyyar APC

Hakazalika, ta ce za a mika takardar shaidar nasara ga wanda ya lashe zaben mazabar Zuru ta Majalisar Dokokin jihar Kebbi a Birnin Kebbi.

May Agbamuche-Mbu.
Kwamishinar INEC, May Agbamuche-Mbu tare da wasu jami'ai a taron .jka takardun nasara ga yan takara Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Kwamishinonin INEC da ke wakiltar jihohin da aka gudanar da zabukan cike gurbi sun mika takardun shaidar nasarar ga yan takarar da suka lashe zabe.

Mika takardun ya tabbatar da su a hukumance a matsayin wadanda suka lashe zabukan cike gurbin da aka gudanar a yankunansu daban-daban.

INEC ta fitar da alkaluman rijistar zabe

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta bayyana Kano a matsayin jihar da ta fi samun yawan sababbin masu rijistar kada kuri'a a fadin Najeriya.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa mutum 321,921 ne suka kammala rajista ta yanar gizo, yayin da wasu 259,377 suka kammala rajista a cibiyoyin rajista.

Bayanan INEC sun nuna cewa jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan sababbin masu rajista da mutum 49,603 yayin da jihar Sokoto ta zo ta biyu da mutum 32,293, sai kuma Lagos ta kasance ta uku da mutum 27,294.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262