Babbar Mota Ta Burma kan 'Yan APC Suna Tafiya Kamfen, an Samu Asarar Rai
- Rahoto ya nuna cewa an tabbatar da mutuwar wani dan APC bayan wata babbar mota ta burma cikin jerin masu kamfen na jam'iyyar a Osun
- Bayanan da aka fitar sun nuna cewa mutane bakwai ne sun jikkata a hadarin, yayin da ɗaya daga cikinsu kuma ke cikin mawuyacin hali a asibiti
- Jam'iyyar APC ta buƙaci a yi cikakken bincike game da hadarin, tana zargin cewa direban motar na iya burmawa kan mutanen ta da gangan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Mutum ɗaya mai suna AbdulRasaq Ahmed ya rasa ransa, yayin da wasu mutum bakwai suka jikkata bayan wata babbar mota ta kutsa cikin jerin masu kamfen na jam’iyyar APC.
An shirya gangamin ne domin mara wa ɗan takarar APC na gwamnan jihar Osun baya a zaɓen ranar 15 ga Agustan 2026, Bola Oyebamiji, a garin Ede ranar Laraba.

Source: Original
Rahoton da Punch ta wallafa ya nuna cewa hatsarin ya faru ne yayin da mahalarta gangamin ke isa yankin Oke Gada da ke Ede a jihar Osun.
'Yan APC sun yi hadarin mota a hanya
Shugaban Kwamitin yaɗa labarai na kwamitin kamfen ɗin Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, Remi Omowaiye, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce waɗanda suka jikkata suna karɓar magani a wasu asibitoci.
“Mutum ɗaya ya mutu a hatsarin. Mutum bakwai sun jikkata, kuma ɗaya daga cikinsu yana cikin mawuyacin hali,”
In ji Omowaiye.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru, yana zargin direban motar da yin biris da umarnin da jami’an FRSC suka bayar domin tsara zirga-zirga yayin gangamin.
“Lamarin abin takaici ne kuma da an kauce masa. Jami’in FRSC da ke kula da aikin ya riga ya umurci motocin da su riƙa amfani da layi guda na titi, yayin da mambobin APC za su bi ɗaya layin.
“Amma direban motar ya bi layin da muke tafiya a kai, sannan ya kutsa cikin taron. Yaron ya mutu nan take, yayin da wasu da dama suka jikkata kuma suna samun kulawa a asibiti,”
In ji shi.

Source: Facebook
'Dan takarar APC ta nemi a yi bincike
Da yake jawabi bayan ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin, mataimakin ɗan takarar gwamnan APC, Benjamin Adereti, ya kuma yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin.
Daily Post ta wallafa cewa ya ce:
“Har yanzu muna ƙoƙarin gano ainihin abin da ya janyo hakan. Yadda lamarin ya faru ya nuna kamar direban ya yi gangancin kutsawa cikin mambobin jam’iyyarmu da gangan yayin da suke kamfen a Ede.
“Ina kira ga hukumomin tsaro na jihar Osun da na Najeriya da su gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin wannan lamari,”
An fara tallata APC a shirin 2027
A wani rahoton, mun kawo muku cewa an fitar da wasu manyan motocin alfarma domin tallata 'yan takarar APC a zaben 2027 mai zuwa.
Wanda ya fitar da bidiyon motocin, Cubana Chief Priest ya sanya hotunan shugaba Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shettima a jikinsu.
'Yan Najeriya da dama sun yi martani game da abin da Cubana ya yi, inda wasu suka ce bai kamata ya yi haka a lokacin da ake fama da matsaloli a kasar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

