Takarar 2027: Yadda Abba Kabir Yusuf Ya Sasanta Manyan ‘Yan APC a Kano

Takarar 2027: Yadda Abba Kabir Yusuf Ya Sasanta Manyan ‘Yan APC a Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya taka muhimmiyar rawa wajen sasanta jiga-jigan jam’iyyar APC da suka samu sabanin siyasa a sassa daban-daban na jihar Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A yayin da gangar siyasar 2027 ta fara zafi, an rika samun sabani a tsakanin manyan yan siyasar APC a sassan jihar Kano.

Bayan sauya shekar gwamna Abba Kabir Yusuf, ya karbi ragamar zama da manyan 'yan siyasar tare da cimma masalaha domin a bar wa mutum daya takara.

Gwaman Kano yana kawo sulhu a siyasar Kano
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya ke jawabi a wani taro Hoto: Sanusi Batture D-Tofa
Source: Facebook

Legit ta tattaro cewa matakin sasancin ya shafi rikicin siyasa tsakanin Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da ɗan majalisar wakilai, Kabiru Alhassan Rurum.

Yadda Abba Kabiru ya yi sulhu a Kano

Haka kuma akwai batun rikicin da ya dabaibaye siyasar Kano ta Arewa tsakanin Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo da Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya fara nema takarar majalisar tarayya a NDC mai adawa

Gwamnan ya kuma tsakanin Hon Alhassan Ado Doguwa da Hon Salisu Yusha'u Soja a Tudun wada/Doguwa idan aka shiga kudancin jihar Kaduna..

An samu wannan sulhu ne bayan an yi zama mabambamta a jihar babban birnin tarayya Abuja, wanda ya samu halartar manyan 'yan siyasa.

Daga cikin sulhu tsakanin manyan 'yan siyasa shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi akwai:

1. Hon. Rurum v Kawu Sumaila

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kira wani zama na musamman domin sasanta sabanin da ya shiga tsakanin Hon. Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Kawu Sumaila, waɗanda dukkansu manyan ‘yan siyasa ne daga yankin Kudancin Kano.

An yi sulhu tsakanin Rurum da Kawu Sumaila
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Kabiru Rurum, Kawu Sumaila da manyan APC a taron sulhu Hoto: Muhammad Mustapha
Source: Facebook

Bayan kammala taron, Hon. Rurum wanda ke wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya a majalisar wakilai, ya tabbatar da cewa an cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu.

A cewarsa, sun amince su yafe wa juna tare da dawo da haɗin kai domin ci gaban magoya bayansu da kuma jam’iyyar APC, kuma dama tun can shaidan ne ya shiga tsakaninsu.

2. ATM Gwarzo v Barau

A wani mataki na daban kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci sasanta rikicin siyasa da ya dabaibaye APC a yankin Kano ta Arewa. Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebbook cewa an gudanar da jerin tarurruka da masu ruwa da tsaki domin warware matsalar.

Kara karanta wannan

2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC

Gwamna ya sasanta rikicin Barau da ATM Gwarzo
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Barau Jibrin da Abdullahi Tijjani Gwarzo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanarwar ta ce an samu goyon baya da sa hannun shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima, wajen tabbatar da sulhun.

Taron ya kai ga cimma yarjejeniya tsakanin ATM Gwarzo da Sanata Barau Jibrin, inda ATM Gwarzo ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata domin mara wa Barau baya gabanin zaɓen 2027.

A cikin wasiƙar janye takararsa da ya aika wa shugabannin jam’iyyar APC, ATM Gwarzo ya sake jaddada biyayyarsa da kuma cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar.

3. Alhassan Ado vs Hon Soja

Da ya ke yi wa Legit karin bayani, Mai magana da yawun jam'iyyar APC reshen jihar Kano, Auwal Abdullahi Soja Gwale ya bayyana cewa an cimma masalaha a tsakanin manyan yan siyasar Doguwa da Tudun wada.

Ya ce tuni Gwamna ya shiga tsakani aka samu fahimtar juna tsakanin Hon Alhassan Ado Doguwa da kuma abokin hamayyarsa a baya, Hon Salisu Yusha'u Soja, duk da cewa dukkaninsu yan APC ne.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya samu shiga da APC ta zabi dan takararta na gwamnan Kano a 2027

Salisu Yusha'u Soja wanda ya shigo daga NNPP ya dade yana harin kujerar majalisa amma bai dace ba, amma da alama mutanen Tudun Wada sai sun kara jiran wani wa'adin na Hon. Doguwa wanda ya dade a ofis.

An yi sulhu a Tudun Wada da Duguwa
Hon Alhassan Ado Doguwa da Salisu Yusha'u Soja Hoto: Hon Salisu Yusha'u Soja
Source: Facebook

A kalamansa:

"Duka jihar Kano mun samu sulhu illa yankuna uku, su kadai mu ka shiga zabe. Amma Tudunwada/Doguwa babu wata matsala, kuma Alhassan Ado Doguwa ne ya samu rinjaye domin shi abokin burmin nasa ya janye masa. Sulhu aka samu."

Da ya ke amsa tambaya a kan ko tirsasa wa sauran masu neman takara a jihar, Auwal Abdullahi Soja ta bayyana cewa:

"Shi zababben Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda shi ne jagoran APC a jihar Kano, gwamna ne wanda ba mai tirsasa al'umma ba, gwamna ne wanda ya ke ba wa kowa yanci da dama."
"Babu wata karamar hukuma da muka sa aka yi sulhu a cikin dole. Da za mu yi dole, ba za a yi zabe a Kura da Garun Malam ba, da ba za mu yi zabe a Dawakin Kudu da Warawa ba, da ba za mu yi zabe a Bagwai da Shanono ba. Da a ce dole ake yi da su ma sai a yi masu dolen, domin Gwamna yana da damar da zai yi dole a kowace karamar hukuma."

Kara karanta wannan

Ribas: Mutumin Wike na dab da zama 'dan takarar gwamnan APC bayan Fubara ya janye

"Amma sai muka samu sulhu a wani waje, mun yi zabe a wani waje. Wannan shi ya tabbar miki da cewa duk wanda ya janye ya yi ra'ayinsa ne, bukatarsa ce, yancinsa ne. Shi ne ya ga dama."

Kano: Gwamna ya mara wa takarar Abba Bichi baya

A baya, mun kawo labarin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Hon. Abubakar Kabir Abubakar wato Abba Bichi a zaben 2027 mai zuwa.

Mai girma Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa ya ga cancantar mutanen Bichi su sake mara wa Hon. Abba Bichi baya yayin zaben, musamman ganin ribar da suka samu a yanzu.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a taron tabbatar da Abba Bichi a matsayin ɗan takarar APC shi kaɗai domin kujerar majalisar wakilai, inda aka zabe shi a matsayin dan takarar jam'iyya daya tilo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng