Hadaddiyar Daular Larabawa Ta Yanke Alaka da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
- Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da duk wata huldar kasuwanci da Iran, sakamakon hare-haren da take zargin kasar
- Matakin ya zo ne bayan karewar yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran, wadda aka tsara domin bude kawo karshen yakin
- Rahotanni sun ce Iran na nazarin wasu hanyoyin fadada yakin, ciki har da kai hari kan sansanonin Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Alaka ta sake rugujewa tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Jmahuriyar Musulunci ta Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
UAE ta sanar da dakatar da dukkanin huldar kasuwanci da hada-hadar kudi da Iran har sai an sake duba matakin.

Source: Getty Images
Daraktar Sashen Sadarwa na Dabarun Ma’aikatar Harkokin Wajen UAE, Afra Al Hameli, ta ce an dauki matakin ne saboda karuwar tashin hankali, cewar The New Arab.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya
Ta ce:
“Saboda karuwar tashin hankali, an dakatar da dukkanin kasuwanci, mu’amalar cinikayya da hada-hadar kudi da Iran har sai wani lokaci.”
A ranar Talata, UAE ta zargi Iran da harba makamai masu linzami guda biyu kan zirga-zirgar jiragen ruwa, amma ta ce sun fada cikin teku.
Sai dai Tehran ta yi watsi da zargin, inda ta bayyana shi a matsayin “marar tushe”.
Muhimmancin UAE ga tattalin arzikin Iran
UAE na daga cikin manyan abokan huldar tattalin arzikin Iran a yankin, yayin da Dubai ke taka muhimmiyar rawa wajen kasuwanci da hada-hadar kudi.
Iran ta dade tana amfani da UAE wajen shigo da kayayyaki da fitar da su, musamman saboda takunkuman Amurka da suka raunana tattalin arzikinta.
Takunkuman sun taimaka wajen kara hauhawar farashi da raunana darajar kudin Iran, yayin da Dubai ta kasance muhimmiyar hanyar kasuwancinta.
Sai dai karin farashin makamashi sakamakon yakin ya taimaka wajen kara kudaden shiga da Iran ke samu daga man fetur.
Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito cewa Iran ta samu dala biliyan 7.5 daga fitar da man fetur a cikin watanni hudu na farkon shekarar Iran.
Hare-haren Iran kan UAE
UAE ta fuskanci hare-haren Iran fiye da sauran kasashen Larabawa masu kawance da Amurka a farkon martanin Iran kan hare-haren Amurka da Isra’ila.
Jami’an UAE sun ce sama da makamai masu linzami 3,000 da jirage marasa matuka aka harba zuwa kasar yayin rikicin.
Bayanan ACLED sun nuna cewa UAE ita ce kasar Gulf da hare-haren Iran kan muhimman wuraren farar hula suka fi shafa.
Tsakanin 28 ga Fabrairu da 30 ga Yuli, hare-hare 172 kan ababen more rayuwa da ba na soja ba aka rubuta a kasashen GCC shida.
UAE ta dauki kashi 28 cikin 100 na hare-haren, inda aka kai hari kan wuraren makamashi, tashoshin jiragen ruwa, filayen jirgin sama da sauran cibiyoyin kasuwanci.
Iran ta yi gargadi ga kasashen Gulf
A wani labarin, an ji cewa shugaban rundunar sojin Iran, Ali Abdollahi, ya gargadi kasashen Gulf cewa duk wata taimako ga sojojin Amurka zai iya zama shiga cikin yakin.
Ya ce Iran na sanya ido kan yawan jiragen saman soja, musamman jiragen dakon mai, da aka jibge a sansanonin soji a kasashen Gulf.
Ali ya gargadi kasashen da ke karbar wadannan jirage cewa Iran na sane da duk wani abu da ke faruwa a sansanonin.
Asali: Legit.ng

