"Dama Sharrin Shaidan ne": Abba Ya Kawo Ƙarshen Rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

"Dama Sharrin Shaidan ne": Abba Ya Kawo Ƙarshen Rikicin Rurum da Kawu Sumaila a Kano

  • Gwamna jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sasanta rikicin da ya shiga tsakanin Hon. Alhassan Rurum da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Kawu Sumaila
  • Gwamnan ya jagoranci zaman sulhu bayan an ji Hon. Rurum na cewa ya shata layi tsakaninsa da Sanata Kawu Sumaila yayin da rikicin ya ta'azzara
  • Bangarorin biyu sun amince su yafe wa juna tare da ci gaba da aiki yayin da jam'iyyar APC ke shirin tunkarar yan adawa a babban zaben 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shiga tsakani domin kawo karshen takaddamar da ta shiga tsakanin Honarabul Kabiru Alhassan Rurum da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila.

Rikici ya nemi ya yi kamari a tsakanin manyan wakilan Kano ta Kudu a majalisun tarayyar kasar nan, har an ji Rurum na cewa ya shata layi tsakaninsa da Kawu Sumaila.

Kara karanta wannan

2027: Martanin Kwankwaso ga zargin yana yi wa Tinubu aiki a NDC

An sulhunta Kawu Sumaila da Rurum
Shugaban APC na Kano, Kawu Sumaila, Gwamna Abba Kabir Yusuf, Run,Murtala Sule Garo da jigon APC a taron sulhu Hoto: Muhammad Mustapha
Source: Facebook

Sai dai hadimin gwamna, Salisu Muhammad Kosawa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Gwamna ya kira bangarorin biyu, inda aka zauna da jiga-jigan APC domin warware matsalar.

Bangarorin biyu sun sanar da cewa sun yafe wa juna tare da warware duk wani sabani da ya shiga tsakaninsu, inda suka bayyana aniyar ci gaba da aiki tare domin ciyar da siyasar yankin gaba.

Abba ya shiga tsakanin Rurum da Kawu

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Honarabul Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya, ya ce yanzu sun sake hade kai a matsayin iyali guda kuma za su kara zumunci fiye da baya.

Honarabul Rurum ya gode wa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bisa kokarin da ya yi na samar da zaman lafiya mai dorewa tsakaninsu.

A nasa bangaren, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, ya bayyana cewa rikicin da ya shiga tsakaninsu aikin shaidan ne kawai. Ya ce yanzu sun yafe wa juna tare da mantawa da duk wani bambanci da ya gabata, sannan a hada karfi da karfe domin ci gaban APC a Kano.

Kara karanta wannan

Abba ya sulhunta Barau da Gwarzo, an samu wanda ya hakura da takarar sanata a 2027

A kalaman Kawu Sumaila:

“Mu iyali daya ne, abin da ya hada mu ya fi siyasa karfi domin muna da alaka ta jini da wasu dangantaka da ba za a iya misaltawa ba. Abin da ya faru rashin fahimta ne kawai, kuma mun warware matsalar. Hakika aikin shaidan ne."

APC ta nemi a hada kai a Kano

Shi ma shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bukaci magoya bayan bangarorin biyu su manta da abin da ya gabata tare da hada kai domin neman nasarar jam’iyyar APC daga sama har kasa.

Gwamnan Kano ne ya kira taron sulhun tsakanin manyan Kano ta Kudu a jihar
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ce:

“Ina gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda hangen nesansa da saurin shiga tsakani. Wannan ya nuna shi shugaba ne na gaskiya.”

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan Kano ne ya kira taron sulhun domin kawo karshen sabanin da ya shiga tsakanin jiga-jigan siyasar Kano ta Kudu.

Taron ya samu halartar mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, shugaban APC na Kano Umar Haruna Doguwa, Alhaji Muhammad Jamu, Sanata Kawu Sumaila da kuma Honarabul Kabiru Alhassan Rurum.

Kara karanta wannan

Mai sha'awar neman kujerar Barau ya fadi dalilin ganawarsa da Shettima, Ganduje

Gwamnan Kano ya sulhunta Barau da Gwarzo

A baya, kun samu labarin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kira zaman sulhu domin sasanta masu neman kujerar sanatan Kano ta Arewa domin zuwa Majalisar dattawa a zaben 2027.

Sulhun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta ya shafi mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da kuma tsohon karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo.

Taron sulhun wanda aka gudanar da shi a Abuja ya samu halartar manyan kusoshin jam'iyyar APC a Kano ciki har da mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo da Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng