Mutumin Wike na Dab da Zama 'Dan Takarar Gwamnan APC a Ribas bayan Fubara Ya Janye
- Manyan masu neman takarar gwamna a inuwar jam'iyyar jam'iyyar APC a jihar Rivers sun janye daga takara kafin zaben fitar da gwani
- Ana ganin Hon. Kingsley Chinda, na kusa da Ministan Abuja kuma mai takun saka da gwamna mai ci, Nyesom Wike, zai samu tikitin jam’iyyar
- Wannan kofa ta bude wa Mista Chinda awanni kadan bayan Gwamna Siminalayi Fubara ya ce ya janye daga neman takarar domin wanzuwar zaman lafiya a Ribas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers – Rahotanni daga jihar Rbas sun nuna mutumin Nyesom Wike, Hon. Kingsley Chinda, jagoran marasa rinjaye a majalisar wakilai ta tarayya, na dab da zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2027.
Wannan kofa ta bude masa ne bayan sauran masu neman takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC mai mulki suka sanar da janyewarsu.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Chinda, wanda ake gani a matsayin na hannun damar Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya dade yana cikin jerin mutanen da ake hasashen za su samu tikitin jam’iyyar.
Mutumin Wike zai samu takara a APC
Trust Radio ta kawo labarin cewa Chinda zai samu zama dan takarar APC a jihar Ribas ne bayan sauran ‘yan takarar sun sanar da janye wa daga fafatawar a jajibirin zaben fitar da gwani.
Na farko cikin wadanda suka janye shi ne gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, wanda aka ce tun farko an cire magoya bayansa daga tsarin tantance ‘yan takara.
A wata sanarwa mai taken “Matakina na janyewa daga zaben fitar da gwani na gwamnan Ribass,” Fubara ya bayyana cewa matakin yana da wahala amma ya zama dole.

Source: Facebook
Ya ce:
“Jagoranci yana nufin sadaukarwa. Akwai lokacin da muradin mutum zai koma baya domin amfanin jama’a. Ribas ta fi karfin kowane mutum guda, kuma a wannan lokaci mai muhimmanci, zaman lafiya da haɗin kan jihar dole su fi kowace bukata ta kai.”
Ya kara da cewa:
“Ga magoya bayana da suka tsaya tare da ni tun farko, ina mika godiya ta musamman. Na san akwai takaici da radadi saboda abubuwan da aka sadaukar. Amma ku sani amincewar da kuka yi min ba ta tafi a banza ba.”Tsohon dan takara ya hakura
APC: Tsohon dan takara ya hakura
Shi ma tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, George Kelly, ya janye daga takarar tare da nuna biyayya ga ƙawancen siyasar da Wike ke jagoranta.
Kelly ya yaba wa Wike saboda rawar da ya taka a rayuwarsa ta siyasa, yana mai cewa ƙawancen jam’iyyun da suke tare na da burin sake zaɓen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Wannan janye wa da jiga-jigan yan siyasa da za su iya neman kujerar suka yi, ya bude kofa ga mutumin Wike da ake sa ran shi ne zai zama dan takarar gwamna a Rivers.
An kifar da mutanen Fubara a APC
A baya, kun samu labarin cewa Magoya bayan gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara sun fuskanci matsala yayin da jam'iyyar APC ke tantance masu neman takara a zaben 2027 mai karato wa.
Rahoto ya nuna cewa kwamitin ya kifar da manyan na hannnun daman gwamna Fubara da ya samu matsala da ministan Abuja, Nyesom Wike a yayin zaman tantance su da aka yi gabanin zaben.
A daya bangaren kuma, yawancin mutanen da ke biyayya ga Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya yi takun saka da Fubara sun tsallake tantancewar yayin da siyasar jihar ke 'dumama.
Asali: Legit.ng


