'Dan Ganduje Ya Fara Nema Takarar Majalisar Tarayya a NDC Mai Adawa

'Dan Ganduje Ya Fara Nema Takarar Majalisar Tarayya a NDC Mai Adawa

  • Ɗan tsohon shugaban APC na kasa, AbdulAziz Umar Ganduje ya sayi fom domin takarar kujerar majalisar wakilan tarayya a Kano
  • Rahotanni sun nuna AbdulAziz ya bai tare da mahaifinsa, yana goyon bayan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Masu nazarin siyasa sun ce matakin zai ƙara zafafa fafatawar siyasa a Kano musamman a mazabar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Dan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sayi fom domin takarar kujerar majalisar wakilai.

AbdulAziz Abdullahi Umar Ganduje ya tsaya takara a zaben karkashin jam'iyyar adawa ta NDC mai adawa a Najeriya.

Dan Ganduje ya fara neman takara a NDC
Dan Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

AbdulAziz yana neman wakiltar mazabar Dawakin Tofa da Tofa tare da Rimin Gado a majalisar wakilai ƙarƙashin sabuwar jam’iyyar NDC, cewar Tribune.

Yadda dan Ganduje ya kai karar gidansu EFCC

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Dangantakarsa da siyasa ta kara fitowa fili bayan ya shiga wata takaddama mai cike da ce-ce-ku-ce da mahaifiyarsa, Farfesa Hafsat Umar Ganduje.

Abdula'ziz ya kai kara da kansa ga hukumar EFCC kan zargin karya wata yarjejeniya da kuma cin hanci da rashawa wanda ya tayar da kura a wancan lokaci.

Ya na neman kujerar majalisar da dan uwansa, Umar Abdullahi Ganduje, ya tsaya takara a karkashin APC a zaben shekarar 2023 a jihar Kano.

Sai dai ya sha kaye a hannun dan takarar NNPP duk da tasirin siyasar mahaifinsu a matsayinsa na gwamna a lokacin wanda ya ba Gwamna Abba Kabir nasara a matsayin gwamna.

Dan Ganduje ya bi layin Kwankwaso domin neman takara
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

'Dan Ganduje ya fara takara a NDC

Rahotanni sun bayyana cewa AbdulAziz ya raba hanya da tafiyar siyasar gidansu tare da komawa sansanin siyasar tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

An ga AbdulAziz a wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta yana bayyana manufarsa ta siyasa ga Kwankwaso yayin wata ganawa ta musamman, cewar Daily Post.

Masu lura da harkokin siyasa suna kallon matakin a matsayin babban sauyi a siyasar Kano saboda doguwar adawar APC da tafiyar Kwankwasiyya a jihar.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: Yadda Abba Kabir Yusuf ya sasanta manyan 'yan APC a Kano

Ana sa ran AbdulAziz zai fafata da ɗan takarar APC a zaben da ake ganin zai kasance cikin manyan fafatawar kujerar majalisar wakilai a Kano.

Jam’iyyar NDC da Kwankwaso ya koma bayan ficewarsa daga ADC tana ci gaba da samun karɓuwa tare da jawo sababbin magoya baya a Kano.

Masu nazari sun ce takarar AbdulAziz a ƙarƙashin NDC za ta iya sauya kawance tare da ƙara zafafa fafatawar siyasa a mazabar Dawakin Tofa.

Hadimin Ganduje ya sauya sheka zuwa ADC

A baya, kun ji cewa hadimin tsohon Shugaban APC Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da cewa ya fice daga jam'iyya mai mulki a Kano.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana dalilan da suka jawo ya sauya sheka, duk da har yanzu ubangdidansa a siyasa, Ganduje na APC mai mulkin Najeriya.

'Dan siyasar, wanda aka fi sani da Dawisu a kafafen sada zumunta ya mika bukata ga dukkanin masu goyon bayansu ta yi watsi da jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.