2027: Dalilin Gwamnan Kano na Mara wa Takarar 'Dan Majalisar Bichi baya
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Hon. Abubakar Kabir Abubakar wato Abba Bichi a 2027
- Mai girma Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa ya ga cancantar mutanen Bichi su sake mara wa Hon. Abba Bihci baya yayin zaben
- Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a taron tabbatar da Abba Bichi a matsayin ɗan takarar APC shi kaɗai domin kujerar majalisar wakilai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga yunkurin sake zaɓen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar.
'Dan majalisar wanda aka fi sani da Abba Bichi, gabanin babban zaɓen shekarar 2027 ya zama 'dan takarar APC tilo a kujerar da ya ke kai gabanin 2027.

Kara karanta wannan
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya samu tikitin takarar APC a Kano

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook.
APC ta amince Abba Bichi ya kuma takara
Gwamnan ya jaddada goyon bayansa a taron tabbatar da ‘yan takara na jam’iyyar APC da aka gudanar a Bichi, aka ayyana Abba Bichi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar shi kaɗai domin kujerar majalisar wakilai.
A cewar gwamnan, Abba Bichi ya nuna nagarta wajen wakiltar al’ummarsa tare da gudanar da ayyukan ci gaba da suka amfani jama’ar mazabar Bichi.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ina yaba wa Hon. Abubakar Kabir Abubakar saboda kyakkyawan wakilci da ya ke yi. Tun daga shekarar 2023 nake addu’ar samun damar yin aiki tare da shi, kuma yau muna aiki tare domin cigaban Bichi da jihar Kano baki ɗaya.”
Gwamna Abba ya ƙara da cewa gudunmawar da ɗan majalisar yake bayarwa wajen tallafawa matasa da kuma ayyukan raya al’umma na ci gaba da sauya rayuwar jama’a ta hanya mai kyau.

Kara karanta wannan
Rigima ta barke a wurin taro, matasa sun yi kan dan majalisar tarayya, Hon. Sadiq Tafida
Gwamna ya yaba wa al’ummar Bichi
Har ila yau, gwamnan ya buƙaci al’ummar Bichi da su ci gaba da bai wa Abba Bichi goyon baya domin tabbatar da nasararsa a zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa taron tabbatar da ɗan takarar da aka gudanar a Bichi ya kasance abin koyi duba da yadda aka tsara shi cikin haɗin kai da kuma yawan jama’ar da suka halarta.
A kalaman Gwamnan:
“Abin da mu ka gani a Bichi ya zarce misali wajen tsari da kuma tara jama’a domin goyon bayan jam’iyya."
Taron ya samu halartar manyan APC da shugabannin siyasa daga sassa daban-daban, daga ciki har da wakilan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ‘yan majalisun tarayya da jami’an jam’iyya
Barau ya zama dan takarar APC
A baya, mun kawo labarin cewa Sanata Barau Jibrin ya samu nasarar lashe tikitin APC na takarar sanatan Kano ta Arewa a babban zaben 2027 da ke tafe bayan an samu nasarar yin sulhu.

Kara karanta wannan
Shugaban majalisa da wasu wakilai 2 sun sha 'kasa a zaben tsiada gwanin APC a Nasarawa
An tabbatar da takarar Sanata Barau Jibrin ne a taron da ya gudana a sakatariyar jam'iyyar APC da ke karamar hukumar Bichi, inda manyan jam'iyya suka taya shi fatan alheri.
Daga cikin jiga-jigan jam'iyyar da suka samu damar halartar taron akwai mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo da da sauran magoya baya da ke fatan jama'ar yankin za su sake zabar Barau.
Asali: Legit.ng