Gwamna Abba Ya Sulhunta Barau da Gwarzo, an Samu Wanda Ya Hakura da Takara a 2027

Gwamna Abba Ya Sulhunta Barau da Gwarzo, an Samu Wanda Ya Hakura da Takara a 2027

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kira zaman sulhu domin sasanta masu neman kujerar sanatan Kano ta Arewa domin zuwa Majalisar dattawa
  • Sulhun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta ya shafi mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Tijjani Gwarzo
  • Taron sulhun ya samu halartar manyan kusoshin jam'iyyar APC a jihar Kano ciki har da mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo da Abdullahi Umar Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi nasarar dinke baraka tsakanin wasu manyan jagororin jam’iyyar APC guda biyu a yankin Kano ta Arewa.

Gwamna Abba Kabir ya sulhunta mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da tsohon karamin Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo.

Gwamna Abba ya sasanta Barau da Gwarzo
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Barau Jibrin da Abdullahi Tijjani Gwarzo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Mai sha'awar neman kujerar Barau ya fadi dalilin ganawarsa da Shettima, Ganduje

Gwamna Abba ya sulhunta Barau da Gwarzo

Matakin sulhun da Gwamna Abba ya dauka, ya buɗe hanyar samun haɗin kai gabanin kakar zaɓe mai zuwa.

Sanarwar ta ce a wani babban taro da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano a daren ranar Talata, Gwamna Abba ya shirya tsohon Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo, da mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Barau Jibrin.

Abdullahi Tijjani Gwarzo ya hakura da takara

Ya bayyana cewa taron ya ƙare ne da sanarwar da Abdullahi Tijjani Gwarzo ya bayar na janyewa daga takarar sanata domin marawa Sanata Barau Jibrin baya.

Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, shugaban kwamitin kasafi na Majalisar wakilai, Abubakar Kabir Bichi, da shugaban APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, da sauran su.

An sasanta Barau da Abdullahi Tijjani Gwarzo
Sanata Barau Jibrin tare da Abdullahi Tijjani Gwarzo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ana kallon wannan cigaban a matsayin babban mataki na ƙarfafa haɗin kan APC a mazaɓar sanatan, inda adawar cikin gida ta yi barazanar raba kan magoya bayan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin Yobe: mutum 6 da aka hana takarar gwamna a APC sun gana da Kashim Shettima

Ta hanyar janyewar tasa, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya yi alkawarin biyayya ga muradun jam’iyyar baki ɗaya, sannan ya nuna shirye-shiryensa na yin aiki tare da Sanata Barau a zaɓe mai zuwa.

Taron sulhun na zuwa ne dai bayan tsohon Ministan ya gana da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Abuja.

An ba Shekarau takarar sanata a APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu masu neman takara shida na jam’iyyar APC sun janye daga neman tikitin kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Dukkanin masu neman takarar da suka halarci taron sulhun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta, sun sanar da cewa sun hakura, tare da bayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

A cewarsu, mara wa Shekarau baya wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a siyasar jihar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng