Dan Takara Ya Ziyarci Kauyukan da 'Yan Bindiga Suka Yi Barna a Katsina

Dan Takara Ya Ziyarci Kauyukan da 'Yan Bindiga Suka Yi Barna a Katsina

  • 'Yan bindiga sun addabi wasu kauyuka na karamar hukumar Bakori da hare-hare wanda hakan ya tilastawa mutane barin matsugunansu
  • Hare-haren dai sun jawo mutane da dama barin gidajensu inda suka koma wasu wuraren domin yin gudun hijira
  • Dan takarar da ke neman kujerar Bakori da Danja a Majalisar Wakilai, Abbduljabbar Guga, ya ziyarci wadannan yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Bakori da Danja a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Amb. Abduljabbar Surajo Guga, ya kai ziyarar jaje a wasu yankuna.

Abduljabbar Surajo Guga ya kai ziyarar gani da ido inda ya shiga wasu yankunan da ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga domin jajanta wa al’ummar da lamarin ya shafa tare da ganin halin da suke ciki.

Guga ya kai ziyara kauyukan Bakori
Abduljabbar Guga na tafiya da jami'an tsaro yayin ziyarar da ya kai Hoto: Funtua Online Tv
Source: Facebook

Tashar Funtua Online Tv ta kawo rahoton ziyarar da dan takarar ya kai a kauyukan da ke karamar hukumar Bakori.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

Guga ya shiga kauyuka

Dan takarar da tawagarsa sun kai ziyara Guga, Kakumi da Kandarawa, da wasu yankunan Jargaba, Inda aka kammala da Garin Kabomo.

Tawagar dan takarar ta gana da shugabannin al’umma tare da kai saƙon tallafi da jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwansu sakamakon hare-haren 'yan bindiga.

Meyasa ya kai ziyarar?

Abduljabbar Guga ya bayyana cewa duk da haɗarin da ke tattare da shiga wasu daga cikin yankunan, ba zai samu natsuwa ba matuƙar bai je ya jajanta wa al’ummar da ke fuskantar wannan hali ba.

Ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da tallafa wa wasu daga cikin iyalan da wannan iftila’i ya shafa.

Ziyarar ta ɗauki tsawon lokaci, tun daga 10:00 na safe zuwa kusan ƙarfe 9:30 na dare, yayin da tawagar ke ci gaba da zirga-zirga tsakanin garuruwa da ƙauyuka, wasu daga cikinsu ta cikin dazuzzuka.

Haka kuma, duk da ruwan sama da aka shafe sa’o’i ana yi, hakan bai hana tawagar ci gaba da ziyarar ba har zuwa kammala shirin.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 da suka sa Adeleke ya tumurmusa APC a zaben Osun

Guga ya koka kan rashin tsaro

A yayin ziyarar, Guga ya ga yadda matsalar tsaro ta tilasta wa wasu mazauna yankunan barin gidajensu tare da jan hankali ga masu haƙƙin kawo ƙarshen matsalar da suyi aikin na kare rayukan al'umma.

Tawagar ta ci karo da wasu daga cikin mutanen da ke gudun hijira cikin ruwa, ciki har da mata da yara ƙanana, yayin da ake fuskantar ruwan sama da ya shafe tsawon awanni.

Guga ya kai ziyara a kauyuka
Abduljabbar Guga na jawabi yayin ziyarar da ya kai Hoto: Funtua Online Tv
Source: Facebook

Wannan yanayi ya taba zuciyar Guga, inda ya nuna damuwa kan irin halin da waɗannan al’ummomi ke ciki.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya kuɓutar da duk waɗanda ke hannun ’yan bindiga, Ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya, sannan Ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi yankin.

'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewa ta dakile wani harin 'yan bindiga.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ta kashe 'yan bindiga biyu tare da kwato makamai daga hannunsu bayan dakile harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng